Dalilai 4 da ka iya hana ganin jinjirin watan Ramadan ranar Talata

Ko da da manyan na’urorin hangen nesa, zai yi matuƙar wahala a hango jinjirin a wannan rana.

Dalilai 4 da ka iya hana ganin jinjirin watan Ramadan ranar Talata

Al’ummar musulmi a faɗin duniya na shirin fara azumin watan Ramadan na shekarar 1447 Hijiriyya, ibadar da ke da matuƙar muhimmanci wajen kusantar Allah da tsarkake zuciya.

Sai dai fara azumin na ta’allaƙa ne da ganin jinjirin wata, wanda shi ne alamar shigowar sabon wata a kalandar Musulunci.

Don haka ne a jiya Litinin, Sarkin Musulmin Nijeriya, Mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al’umma su fita duban jinjirin watan Ramadan daga yammacin Talata, 17 ga Fabrairu, 2026.

Idan aka ga jinjirin a wannan dare, Laraba ce za ta zama ranar farko ta azumi. Amma idan ba a gan shi ba, to Alhamis 19 ga Fabrairu ce za a fara azumi.

Dalilai da ka iya hana ganin jinjirin watan

Sai dai masana ilimin taurari sun yi hasashen cewa akwai yiwuwar ba za a ga jinjirin watan a ranar Talata ba, ko da ido ko da na’urar hangen nesa.

Ga wasu daga cikin dalilan da suka bayar

Sabon Haihuwar Wata:

An tsara cewa za a haifi jinjirin ne da misalin ƙarfe 1:01 na rana a ranar Talata. Wannan na nufin zuwa lokacin faɗuwar rana, bai kai awa shida da haihuwa ba — wanda ke sa ya yi ƙuruciya sosai a gani.

Ƙarancin Tsayuwarsa a Sama:

Jinjirin zai tsaya ne a kusan digiri biyu kacal a sararin samaniya, kuma zai ɓuya bayan faɗuwar rana da kusan minti tara. Wannan ɗan gajeren lokaci yana rage yiwuwar ganinsa.

Kusanci da Hasken Rana:

Watan zai kasance kusa da hasken rana, wanda ke sa haskensa ya yi rauni kuma ya wahalar da ganinsa.

Yanayin Gani Ko da Na’ura:

A kimiyyance, ko da da manyan na’urorin hangen nesa, zai yi matuƙar wahala a hango jinjirin a wannan rana.

Masana sun ce mafi dacewa a kimiyyance shi ne a iya ganin watan a yammacin 18 ga Fabrairu.

Simwal Usman Jibril, mamba a kwamitin duban wata na Nijeriya, ya bayyana cewa wannan hasashe ya samo asali ne daga lissafi da binciken kimiyya da suka yi a wannan fanni.

Bin Umarnin Addini Duk da Hasashe

Duk da wannan hasashe na kimiyya, sai dai Simwal ya jaddada cewa dole ne Musulmai su fita duban wata kamar yadda koyarwar Manzon Allah (SAW) ta tanada, la’akari da cewa hasashen kimiyya ba ya maye gurbin ibadar nema da gani.

Haka kuma, ya ce idan Saudiyya ta sanar da ganin wata a ranar Talata, Nijeriya na iya bin sahu, musamman kasancewar Saudiyya na gaban Nijeriya da kusan awa biyu kuma tana amfani da manyan na’urorin zamani.

Yadda Ƙasashe Ke Bambanta

Ƙasashe kamar Nijar da Ghana su ma za su duba watan a ranar Talata, amma hasashen kimiyya ya nuna su ma na iya fara azumi a Alhamis.

A ɓangaren duniya kuwa, ƙasashe irin su Oman, Turkiyya, Singapore, Indiya da Pakistan sun shirya fara azumi a ranar Alhamis 19 ga Fabrairu bisa lissafin ilimin taurari.