Dalilai 8 da ke tunkuda mutane zuwa ɗabi’ar Luwaɗi da Maɗigo
Wasu kuma jaraba ce kawai, kamar yadda ake samun masu lalata da dabbobi.
Wani abin ban haushi da takaici da ya bullo a cikin al’umma a ’yan shekarun bayan nan shi ne; bala’in luwaɗi da maɗigo wato tarawa a tsakanin jinsi daya (namiji da namiji ko mace da mace).
A iya binciken da na gudanar kusan duk manyan addinan duniya sun haramta wannan mummunar dabi’a, hade da la’antar masu aikata ta.
- An kammala kwaso ’yan Najeriya da suka makale a Sudan —NIDCOM
- Kotu ta bayar da belin da tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan
Duk da cewa a al’adance ba za a rasa wata al’adar da ta yarda da haka ba.
Amma abin daure kai da mamaki shi ne; ko daddobi da ba su da hankali ba a gani suna aikata wannan mummunar dabi’a, sai ga mutane da Ubangiji Ya azurta da hankali, ilimi da tunani.
Namiji ya nemi dan uwansa namiji ko mace ta nemi ’yar uwarta mace da sunan biyan bukata irin ta ma’aurata ko kuma domin kawar da sha’awa da aka sani akwai tsakanin namiji da mace.
Bincike ya nuna cewa wannan dabi’a ta zama ruwan dare game duniya a tsakanin maza da mata, yara kanana, matasa kai har ma da tsofaffi.
Ko me ke tunkuda mutane suke afka wa wannan masifar?
Wadannan dalilai da zan zayyano a kasa, suna daga cikin dalilan da bincike ya nuna su ke sa mutane suna aikata wannan mummunar dabi’a:
1. Talauci: A halin da duniya take ciki na rashi da matsi, da yawan mutane abin da za su ci ma yana gagarar su.
Wasu masu dukiya da ke irin wannan dabi’a da abin duniya suke rudar mutane; musamman yara kanana da matasa har su afka wa wannan masifa.
2. Rashin hakuri: Wasu yaran da sun fara tasawa hallayarsu ta sha’awa mai tsanani take bayyana, kuma da yawansu suna karatu ne iyayensu na jira su kammala sannan a aurar da su.
Idan suka kasa hakuri sai a ga sun fara neman hanyar rage wannan sha’awa; sai Shaidan ya yi ta kawata musu hanyoyin da za su biya wa kansu bukata har su afka, tare da duban hakan zai fi musu rufin asiri tunda ba zancen daukar ciki ko yin sa.
3. Mu’amala da abokan banza: Idan mutum na mu’amala da mutanen banza, yau da gobe ko ba halinsu daya ba, wata rana za a ga sun rinjayi mutum har sun sa shi a hanyar da suke.
4. Tabarbarewar tarbiyya: A zamanin baya iyaye sun fi kula da tarbiyyar ’ya’yansu, ba kamar yanzu ba da mafi yawan iyaye hankalinsu ya fi karkata kan neman abin duniya.
Da yawa wasu yaran a gidajensu suke aikata irin wannan dabi’a, wasu ma da ’yan uwansu na jini ko shakikai, kuma a ce iyayensu ba su gano ba.
A zamaninmu ko tafiya iyayenmu suka ga mun canja sai sun bincike mu, balle har su gan mu da abin da ba su suka saya mana ba.
5. Wayar hannu: Wayar hannu da Intanet sun kawo shafukan sada zumunta (Social Media), inda wasu ta nan suke samun wadanda za su rude su har su koyi wannan dabi’a.
Wasu ma daga kallon bidiyo na irin wannan masifar ta Intanet kawai sai Shaidan ya kawata musu su ji suna sha’awar farawa.
6. Camfi: An camfa cewa duk masu irin wannan dabi’a suna yin kudi, hakan ke sa mutane da yawa afkawa cikin wannan dabi’ar.
Wani lokacin ma malaman tsibbu da bokaye ke ce wa mutane bukatarsu ba za ta biya ba sai sun aikata haka, kuma saboda Shaidan ya riga ya yi musu huduba, sai su aikata saboda neman abin duniya.
7. Jahilci: Mafi yawan mutane jahilci ya yi musu katutu, shi ya sa za a ga suna aikata dabi’ar da ko daddobi ba sa aikatawa.
Kamar yadda na fada a sama dukkan addinai sun yi hani da wannan dabi’a, duk mai hankali, ilimi da kuma aiki da shi ba zai yi sha’awar aikatawa ba.
8. Jaraba: Wasu kuma jaraba ce kawai, kamar yadda ake samun masu lalata da dabbobi.
Irin wadannan mutane abin kamar ciwo ne a jikinsu na aikata abin da hankali da tunani ma ba zai dauka ba. Kuma a duk lokacin da ya motsa musu sai sun aikata.
Mece ce mafita?
Mafita daya ce; iyaye su tashi tsaye su sa ido ga tarbiyyar ’ya’yansu, su san irin abokan da suke mu’amala, su rika bibiyar abin da suke yi a soshiyal midiya da wayoyinsu.
Sannan mutane su sani, arziki da rashi duk na Allah ne, Yana ba wanda Ya so Ya hana wanda Ya so; ba don ba Ya son su ba, sai don Ya jarraba imaninsu.
Idan mutum ya yi hakuri a gaba sai ya samu abin da bai zata ba. A takaice wani ba ya azurta wani, kuma saba wa Allah ba zai sa Ya ba ka abin da kake so ba, sai dai ka hallaka kanka.
A karshe, malaman addini su kara kaimi wurin ankarar da al’umma azabar da Ubangiji Ya tanadar wa masu aikata irin wannan dabi’a.
Hukuma kuma ta kafa doka mai tsanani da za ta hukunta wadanda aka samu da aikatawa.
Ubangiji Ka ji kanmu Ka kare mu da zuri’yarmu daga aikata wannan mummunar dabi’a!
Samira Bello Shinko imel: [email protected]