Dalilai uku da ke janyo rikici tsakanin ’yan siyasa da sarakuna

Ya rage ga Nijeriya ta fayyace irin aikin da sarakunan za su yi a cikin al’umma, domin har yanzu babu kamarsu.

Dalilai uku da ke janyo rikici tsakanin ’yan siyasa da sarakuna

Yi wa dokar masarautu gyaran fuska a Jihar Sakkwato da takardar tuhumar neman bahasi kan ƙin shirya hawan daba da Gwamnatin Jihar Katsina ta aike wa Sarkin Katsina da kuma ɗauki-ba-ɗaɗin da ake yi tsakanin ɓangaren Muhammadu Sanusi II da Alhaji Aminu Ado Bayero a kan wane ne Sarkin Kano, suna ci gaba da sanya tsoro a zukatan al’ummar Arewa kan makomar masarautun yankin.

Kamar yadda kafar labarai ta BBCHausa ta yi sharhi a kai, ta ce ana yi wa wannan al’amari kallon zaman tankiya a tsakanin sarakuna da ’yan siyasa masu mulki.

Kuma wannan ne ke sanya al’umma tambayar me ke haddasa rikici tsakanin ɓangarorin biyu?

BBC ta tuntubi Farfesa Shu’aibu Shehu Aliyu, Daraktan Cibiyar Bincike da Adana Kayan Tarihi ta Jami’ar Ahmadu Bello (Arewa House) da ke Kaduna da kuma Dokta Raliya Zubairu Mahmud ta Sashen Nazarin Tarihi a Jami’ar Ilimi ta Jihar Kano da ke Kumbotso.

Masanan sun bayyana wasu dalilai uku da suka ce su ne ke janyo rashin fahimtar juna a tsakanin sarakuna da ’yan siyasa kamar haka:

1) Rashin fayyace aikin sarakuna a tsarin mulki

Tun farko babbar matsalar da ke haddasa rikici a tsakanin sarakuna da ’yan siyasa ita ce rashin fayyace aikin da sarakunan ya kamata su yi a Kundin Tsarin Mulkin Kasa.

“Idan ka dubi tsarin mulkin ba a fayyace irin aikin da sarakunan ya kamata su yi ba.

“Rashin sanin ayyukansu ne ya sa suke shiga abubuwan da ake ganin ba su shafe su ba.

“Ko a gyaran fuskar da aka yi wa Kundin Tsarin Mulki a 1999, ba wani fayyataccen tsarin da aka fitar musu.

“Amma duk da rashin fayyacewar da tsarin mulkin bai yi ba, za ka ga har yanzu akwai abubuwan da ba a yi sai da su.

“Misali idan kana son sayen fili ko ƙasa sai da sa-hannun dagaci ko mai unguwa.

“Haka batun kasancewar mutum ɗan gari, dole sai da sa-hannun dagaci ko mai unguwa.

“Amma kuma duk ba sa cikin tsarin mulki. To me ya sa ba za a gyara ba domin ba su waɗannan damarmaki,” in ji Dokta Raliya Zubairu Mahmud.

2) Shigar Sarakuna siyasa

Zarge-zargen shigar sarakuna siyasa kusan za a iya cewa na daga cikin manyan dalilan da ke ƙara rura wutar rikici a tsakanin sarakunan da ’yan siyasa.

“Sarki ya kamata ya zama uban kowa, don haka bai kamata ya sa hannu a cikin siyasa ba.

“Kuma tsoma baki a siyasar ke janyo musu rashin ƙima a hannun ’yan siyasa.

“Kamata ya yi sarki ya zama mai sa ido mai kuma bayar da shawara. Hakan zai sa ’yan siyasa su girmama shi.

„Amma idan ɗan siyasa ya fuskanci cewa sarki ko hakimi ko dagaci ko mai unguwa ya nuna masa hamayya, to, idan ya samu dama ba zai bar shi ba.

“Ko dai ya tsige shi ya musanya shi da wani ko ya bijiro da tsare-tsaren da za su rage masa ƙarfi,’’in ji Raliya.

3) ’Yan siyasa na ‘ƙullatar’ sarakuna

“Wataƙila mutanen da suka ci zaɓe kan ƙullaci sarakunan da suka tarar a kan mulki inda suke ɗaukar matakan wulaƙanta su sakamakon fahimtar cewa sarkin ya ƙalubalance su ko kuma ya nemar wa abokin hamayyarsu ƙuri’a.

“Wani lokacin ma za ka ga ’yan siyasar na da alaƙa da gidajen sarauta ko su ma sun gaji sarautar.

“Ka ga ke nan kujerun mulkin na ba su damar ɗaukar fansa a kan sarakunan ta yadda ko dai su cusa danginsu a sarautar ko su cire sarkin da suka tarar domin dora jininsu ko abokansu.

“Sannan akan samu yanayin da wasu ’yan siyasa kan ƙullaci masarauta, watakila saboda wani rikici da ya haɗa masarautar da mahaifansu ko wani abu mai kama da haka.

“Wasu kuma kawai jininsu ne bai haɗu da sarakunan ba, bisa tunanin cewa sarakunan ba su da wani muhimmanci a tsarin da ake ciki.

“Lokacin da aka fara karya lagon sarakunan A bangaren Farfesa Shu’aibu Shehu Aliyu, Daraktan Arewa House da ke Kaduna ya ce tun bayan cire sarakuna da dama da Gwamna Lord Lugard ya yi a Arewacin Najeriya, babban dalilin da ya fara janyo ’yan siyasa su raina sarakunan shi ne lokacin da aka fara siyasa a Nijeriya a 1952, inda aka zaɓi wakilai daga lardunan uku na Nijeriya.

“To a wancan lokaci an samu saɓani tsakanin mutanen da aka zaɓa suka zama ’yan majalisa daga Jihar Arewa da sarakan yankunansu.

“Misali an zaɓi mutum ya zama Minista kuma idan ya koma garinsu zai shiga fadar sarki da takalmi sannan ya gaisa da sarki.

“Wannan ne ya fara janyo rikici tsakanin ’yan siyasa da masarautu.

“Duk da dai daga baya an sauya cewa dole ne kowa idan ya koma gida ya yi biyayya ga al’adun gargajiya.

“A baya kafin juyin mulkin farko, akwai Majalisar Sarakuna sannan sarakuna na cikin harkokin gwamnati inda wasu sarakunan ma suka zama ministoci.

“Misali Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I ya taɓa zama Gwamnan Riƙon Kwarya. Sannan Sarkin Zazzau Jafaru ya taɓa zama Minista.

“Haka Sarkin Katsina Usman Nagwaggo ya taɓa zama Minista,” in ji Farfesa Shu’aibu Shehu Aliyu.

Farfesa Shu’aibu ya ƙara da cewa an fara karya lagon sarakunan ne a 1966.

“To amma bayan juyin mulki musamman lokacin da aka yi gyaran tsarin mulkin da ya samar da ƙananan hukumomi a 1966, sai aka fara cire wasu iko da sarakunan ke da su misali ’yan doka da kotuna duka aka cire su daga hannun sarakunan.

“Haka aka yi ta yi har karshe lokacin da aka yi wa dokar ƙananan hukumomi kwaskwarima a 1988 inda aka cire hannun sarakuna daga harkokin mulki aka bar su tsurarsu.

“Abin da ya fi takaici ma shi ne yadda aka mayar da su ƙarƙashin ’yan siyasa misali hakimi na ƙarƙashin shugaban ƙaramar hukuma. Ko tafiya zai yi sai da izini. Hatta albashinsu na hannu ƙananan hukumomi.

Illolin wulaƙanta masarautun gargajiya

Farfesa Shu’aibu ya danganta matsalolin da Arewacin Nijeriya ke fuskanta na rashin tsaro da shaye-shaye da irin yadda aka mayar da sarakunan koma baya.

A baya sarakunan nan su ne shugabannin addini. Jama’a na martaba su sosai. Su ne hanyar da ake bi wajen isar da sako ga talakawa.

“Idan ka duba tun daga sarki, hakimi, dagaci har zuwa mai unguwa. Saboda haka lalata tsarin da aka yi na ɗaya daga cikin dalilan matsalar rashin tsaro a Arewa.

“Saboda a baya duk wani baƙo idan ya zo gari gidan mai unguwa za a kai shi.

“Su kansu ’yan siyasa na amfani da sarakunan wajen kaiwa ga talakawa musamman idan ka dubi batun rijistar zaɓe, allurar riga-kafi da sauransu, duk da sarakunan ake amfani.

“Saboda lalata wannan tsari ba ƙaramar illa ke yi wa tsarin zamantakewa ba a Arewacin Nijeriya,” in ji Farfesan.

Mafita

Duka masanan biyu Farfesa Shu’aibu Shehu Aliyu da Dokta Raliya Zubairu Mahmud, sun amince cewa fayyace ayyukan sarakuna a Kundin Tsarin Mulkin Kasa ne kawai zai magance matsalar.

“Ya rage ga Nijeriya ta fayyace irin aikin da sarakunan za su yi a cikin al’umma, domin har yanzu babu kamarsu.

“Kada a manta ko da lokacin mulkin Turawan mulkin mallaka ta hanyarsu Turawan suka iya yin mulkin da suke so saboda muhimmancinsu,” in ji Farfesa Shu’aibu.

To sai dai Dokta Raliya ta ce matsalar da za a fuskanta koda an fayyace matsayin sarakunan a Kundin Tsarin Mulki ita ce “Ai ’yan siyasar ne dai za su zauna su rubuta abin da suke so. Ka ga ke nan jiya-i-yau.”