Dalilan bunkasar Dandalin Murtala da ke Kaduna
Dandalin tunawa da marigayi tsohon Shugaban kasa Janar Murtala Ranat Muhammad da ke Kaduna ya sha sauye-sauye tun zamanin turawan mulkin mallaka ya zuwa yau. Tarihin dandalin ya faro ne lokacin da turawa suka kafa wurin don ya zama filin jirgin sama na farko a garin Kaduna. Sannan bayan turawan sun gama mamaye Arewa sun […]
Dandalin tunawa da marigayi tsohon Shugaban kasa Janar Murtala Ranat Muhammad da ke Kaduna ya sha sauye-sauye tun zamanin turawan mulkin mallaka ya zuwa yau.
Tarihin dandalin ya faro ne lokacin da turawa suka kafa wurin don ya zama filin jirgin sama na farko a garin Kaduna. Sannan bayan turawan sun gama mamaye Arewa sun daina yaki sai suka mayar da wurin inda ake yin sukuwar dawaki don shakatawa wanda hakan ya sa ya samo sunan da ake ce kira ‘filin sukuwa’.
Dandalin kuma a yanzu ana yin wasanni da yawa da suka hada da Polo da kwallon kafa da na hannu da sai sauransu. Sauran sun hada da tarurruka da faretin soja da mika mulki da yin kamfe, da bukukuwa musamman ga wadanda suke da kumbar susa.
Abin mamaki shi ne yadda ake zuwa don yawon bude ido ko shakatawa musamman ma da yamma. Masu yin hakan sun hada da tsofaffin da matasa da sauransu inda suka hada da tsofaffin manyan sojoji da gwamnoni da sauransu.
A ranakun hutu kuwa tun asuba ba a kama hannun yaro, saboda masu motsa jiki suna yi wa wajen tsinke, bugu da kari har da masu saye da sayarwa.
Wannan dandalin an sa masa suna ne don tunawa da dan kishin kasa Janar Murtala Ramat Muhammad wanda Kanar Dimka da sauransu suka yi yunkurin yi masa juyin mulki sannan suka yi masa kisan gilla a shekarar 1976.
Bayan yakin duniya na biyu aka maida dandalin wurin yin sukuwar dawaki gadan-gadan. Sannan aka fara yin kwallon Polo wanda har yau ake tafafatawa. In za a iya tunawa, a nan ne ma tsohon gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Shehu Kangiwa ya rasa ransa bayan ya fado a kan doki a wasan kwallon Polo a 1982.
Bugu da kari, wani kocin wasan motsa jiki mai suna Umar Abdulhamid ya shaidawa Aminiya cewa motsa jiki na kara lafiya. Ya kuma yi kira ga jama’a akan su rika motsa jiki.
Wani daga cikin wadanda ke motsa jiki a wurin sun hada da Alhaji Abullahi Bayero wanda ya ce ya jima yana motsa jiki don ya kara kumari wanda hakan na maganin cututtuka irin su hawan jini da shan inna da makamantansus.
Haka kuma, wani makanike kuma mai horar da masu motsa jiki, Abdurrashid Idris ya ce shi da abokansa suke motsa jiki, sannan jama’a suka fara matsawa kusa dashi don yin motsa jikin tare da shi, haka tasa ya zama mai horas wa sannan ana =bashi na goro don ya sayo tabarmi da yawa da ake motsa jiki akansu duk ran asabar sa lahadi da safe.
Wadanda ke motsa jikin sun hada da matasa masu jini a jika suna gudu ba kama hannun yaro. Wasu kuma suna wasanni daban daban wasu suna ninkaya.
Manya kuwa masu yawan shekaru wanda yawancinsu suna da tumbi da teba da kiba suna tafiya sannu sannu. Wasu kuma suna yin motsa jikin ne a kan dole don sun samu shanyewar jiki.
Kuwa da inda ya sa gaba, domin ‘yan kasuwa kuwa suna ta hada-hada kamar masu sayar da lemun kwalba, dabino, lemo, kankana masu yanke kunba, da dai sauransu. Da yamma kuwa gefen daddalin yana zama kasuwa da masu saida suya. A lokacin zafi kuwa a nan ake yin barcin rana, don akwai iska mai dadi don babu hayaki da karar janereto ko na mutum ko na makwabsta.
Duk da an rubuta a allo cewa ba a koyon mota a wajen, wasu suna yi wa wannan dokar karan-tsaye don suna yin abin da suka ga dama.
Sannan an sa alamar hana masu kilisa akan doki bayan karfe biyar, amma wasu na karya dokar, don yara masu kiwon doki suna sukuwa da tayar da kura ga jama’a. Sannan ’yan sanda sun hana ‘ya’yan masu kudi yin boris da mota ko manyan mashin a filin.. Lallai dandalin zai dade yana jan hankalin jama’a masu son motsa jiki da kuma masu son hutawa musamman lokacin zafi.