Dalilan ci gaban matsalar mai a yankin Arewa

An dora laifin karancin man fetur da dizel a jihoihn Arewacin Najeriya da kuma Abuja a kan tsadar man dizel da rashin dakon man fetur yadda ya kamata zuwa Arewacin Najeirya. Binciken wakilanmu ya gano cewa an samu raguwar dogayen layi a gidajen mai musamman a Jihar Legas, inda cikin ’yan mintoci masu ababen hawa […]

Dalilan ci gaban matsalar mai a yankin Arewa

Wani layin jarkoki a gidan mai

An dora laifin karancin man fetur da dizel a jihoihn Arewacin Najeriya da kuma Abuja a kan tsadar man dizel da rashin dakon man fetur yadda ya kamata zuwa Arewacin Najeirya.

Binciken wakilanmu ya gano cewa an samu raguwar dogayen layi a gidajen mai musamman a Jihar Legas, inda cikin ’yan mintoci masu ababen hawa ke shan mai, a yayin da a Arewacin kasar kuma tsugune ba ta kare ba.

Wakilanmu sun gano cewa da kyar, da jibin goshi ake masu ababen hawa ke samun man a kan farashin N165 da gwamnati ta kayyade  a gidajen mai a Arewacin Najeriya.

Wasu masu ababebn hawa a yankin kan kwana suna bin layi a gidajen mai a Arewacin Najeriya, wadadan ba su da sararin yin hakan kuma kan kare da sayen litar fetur a kan N250 zuwa N400 a hannun ’yan bumburutu.

Hakan ya haddasa tashin gwauron zabon farashin abububwa, a daidai lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki.

Musabbanin matsalar

A cikin wata Fabrairu ne aka shiga da wani gurbataccen mai Najeriya, lamarin da ya sa kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya sa aka janye man daga kasuwanni, ya kuma hadda karancinsa.

A ranar Laraba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba wa ’Yan Najeriya hakuri ka matsalolin da karancin ya haifar, yana mai zargin marasa kishi da aikata zagon kasa.

Duk da cewa bai kama suna ba, masana da masu lura da abubuwan da ke faruwa a bagnaren mai sun yi hasashen matsalar ba za ta yi saurin karewa ba a Arewacin Najeriya saboda karin kudin dakon manyan motoci da ke sayen litar man dizel N700 zuwa N800.

Layin ababen hawa a wani gidan mai a Kano. (Hoto: Salim U. Ibrahim)

Ana ‘cin kwakwa’

A yayin da aka samu raguwar layukan a gidajen mai a Legas da sauran jihohin Kudu, tsugune ba ta kare ba a jihohin Arewa da Abuja, masu nis da manyan rumbunan man.

Wakilinmu ya gano cewa layin ababen hawa a gidan mai na AA Rano da ke a Nyanya-Abuja, ya kai tsawon kilomita guda, inda masu ababen hawa ke ta guna-guni.

Wani direben motar haya da muka tattauna da shi, Adamu Usman, ya ce, “Na fi awa uku a nan, sai yanzu na kusa bakin kofar shiga;  Yanzu kuma sai na yi awa daya zuwa awa biyu kafin in samu.”

“N250 na sayi lita a Mararaba, Jihar Nasarawa, a wani gidan mai da babu dogon layi saboda tsadar. Na lura da dogayen layuka a wasu gidajen mai da ke sayar da fetur a kan farashin gwamnati,” inji wani mai abun hawa mai suna John Oche.

A Jihar Kano inda matsalar ta faro tun a watan Fabrairu, har a ranar Litinin, yawancin gidajen mai babu mai, in banda ’yan kadan da ke sayarwa, ga dogon layi a yayin da ’yan bumburutu ke cin karensu babu babbaka.

Wasu gidajen mai da ke sayar da litar mai a kan N165, famfuna kadan ke bayar da mai.

Wani wanda ya zo shan mai ya ce tun karfe 7 na safe ya je shan mai, amma bai samu ba sai bayan karfe 11am.

Ya ce “Babban abun tashin hankali shi ne sai ka shiga gidan mai ka samu kan famfo daya ke bayar da mai.”

Wakilinmu ya lura a wasu gidajen mai da ke wajen gari na sayar da lita a kan N225 .

Dillalai za su shigo da fetur Abuja

A yayin da matsalar karancin man fetur ke ci gaba da addabar Abuja, masu manyan rumbunan mai na Ijegun-Egba da ke Legas sun ce daga ranar Litinin za su shigo da mota 40 makare da man Abuja, daga cikin lita miliyan 106 da suke da shi a ajiye.

Bayan wani taron gaggawa da kungiyarsu ta yi a ranar Lahadi ne Shugaban kuniygar, Mista Mr Adebowale Olujimi da sakatarensa,  Eshiet E. Eshie, suka fitar da sanarwar.

“Bisa tsarinmu na yi komai a bayyana, muna sanar da cewa muna da lita miliyan 106 na man fetur a ajiye kuma za su yi lodin su a motoci.

“Duk rumbunan man da ke yankin Ijegun-Egba a shirye suke su loda su kuma tura motoci 40 na man fetur zuwa Abuja, domin taimakawa a ci karfin matsalar karancin man da ta addabi birnin.”

Kamfanonin mai da ke cikin kungiyar sun hada da kamfanonin A.A. Rano Ltd, Menj Oil Ltd, Chipet Oil Ltd, Rainoil Ltd, Stallionaire Ltd, Aipec Oil Ltd; da kuma First Royal Oil Ltd.

Za a hukunta masu kunnen kashi

Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Tymipre Sylva ya ce gwamnati za ta hukunta duk manyan dillalan man fetur da ke sayar da shi fiye da farashin da gwamnati ta kayyade.

“Ina tabbatar muku cewa duk manyan dillalan da ke sayarwa fiye da farashin da gwamanti ta kayyade za su fuskanci hukunci.

“Za mu dauki tsattsauran mataki a kan duk wanda ya yi kokarin amfani da wannan matsalar wajen azurta kansa,” inji shi.

Daga Sagir Kano Saleh, Vincent Nwanma, Simon E. Sunday (Abuja), Dickson Adama (Jos), Clement A. Oloyede (Kano) & Haruna G. Yaya (Gombe)