Dalilan da aka ba ni Sarauniyar noma ta Jihar Katsina – Binta  Dalhatu

Tarihi ya nuna cewa tun tale-tale mata na taka muhimmiyar rawa wajen harkar noma, inda a wasu lokutan in aka duka gona sukan tsere wa wadansu maza. Wannan kokari da suke yi ne ya sa har zuwa yau wannan tasiri nasu bai gushe ba. Hajiya Binta Haruna Dalhatu matashiyar manomiya ce wadda kuma ta kafa […]

Dalilan da aka ba ni Sarauniyar noma ta Jihar Katsina – Binta  Dalhatu

Binta  Dalhatu

Tarihi ya nuna cewa tun tale-tale mata na taka muhimmiyar rawa wajen harkar noma, inda a wasu lokutan in aka duka gona sukan tsere wa wadansu maza. Wannan kokari da suke yi ne ya sa har zuwa yau wannan tasiri nasu bai gushe ba.

Hajiya Binta Haruna Dalhatu matashiyar manomiya ce wadda kuma ta kafa kuma take jagorancin wasu daga cikin kungiyoyin manoma mata, kuma ta bayyanawa Aminiya abin da take ganin shi ne dalilan da suka sanya Hukumar Kula da Harkokin Noma da Raya Karkara ta Jihar Katsina, (KTARDA) ta ba ta Sarauniyar Noma ta Jihar Katsina.

Hajiya Binta ta ce tun farko abin da ya hada ta da sauran mata musamman na karkara a lokacin da take aikin gwamnati zuwa lokacin da ta ajiye aikin shi ne noma.

“Na fara mu’amala da noma ta hanyar kafa kungiya,saboda na karanta fannin ci gaban al’umma da yankunansu. Na kara tsintar kaina a haka bayan na shiga harkar siyasa a shekarar 2008, domin har mukamin kansila mai kula da sashen ruwa da tsabta na rike a karamar hukumata ta Rimi. Ina aiki da FADAMA III,  inda muke amsar kaya muna raba wa mutane ta hanyar tallafi. Sakamakon hidimomi sun fara yi mini yawa ya sa sai na ajiye aikin gwamnati domin in samu damar ci gaba da harkokin kungiya. Ajiye aikin ke da wuya,sai kawai aka aiko mini daga Abuja cewa an ba ni jami’a mai kula da kungiyoyin kananan manoma mata ta Jihar Katsina. Samun wannan mukami ne ma ya ba ni damar zuwa kasar Tanzaniya inda na yi wani kwas a harkar noman da kungiyoyi,” inji ta.

Ta kara da cewa, “Kazalika, kawo batun noman shinkafa da wannan gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Masari suka yi, ya kara ba ni damar yin aiki da sashen  kula da wannan bangare domin nan ma an ba ni jagorancin sashen mata.”

Ta ce babu wanda ya ba ta shawarar shiga harkar noma, da kanta ta yanke wannan hukunci.

Yadda ta zama Sarauniyar Noma 

“Shi wannan mukami na Sarauniyar Noma Hukumar Kula da Harkokin Noma da Raya Karkara (KTARDA) ce ta ba ni shi a wajen bikin nuna kayan amfanin gona da aka yi a bara a garin Kafin Soli. Ba ni na nema ba, hasali ma ban san abin da suka shirya ba sai dai kawai aka kira ni aka ce hukumar ta ba ni wannan matsayi. Ba nadi ne na Sarki ko wani Hakimi ba, nadi ne daga ita Hukumar,” inji ta.

In kuma har akwai wani dalilin faruwar hakan kamar yadda ta ce, to a tunaninta bai wuce ta kawo  wani nau’in amfanin gona ba da matan da take yi wa jagoranci suka yi ba. A cewarta, duk wani abin da maza suke nomawa, su ma mata suna noma shi walau a kungiyance ko a daidaikunsu.

Manomiyar ta ce, “Ba na jin nauyin shiga cikin kowane lungu ko sako wajen wayar da kai don ganin cewa mata sun dukufa ga yin noma. Kuma duk inda wani abu ya fito na batun noma, to gaskiya sai inda karfina ya kare, amma zan yi iyakar yi na in ga mun same shi.”