Dalilan da APC ta sha kaye a Abuja
Shan kaye da Jam’iyyar APC mai mulki ta yi a zaben Shugaban Kasa da na kujerun Majalisar Dokoki na sanata da wakilai 2 a yankin Abuja da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata, ya zo wa jama’a da dama da mamaki. Magoya bayan jam’iyyar a baya lokacin da Jam’iyyar PDP ke mulkin kasar […]
Shan kaye da Jam’iyyar APC mai mulki ta yi a zaben Shugaban Kasa da na kujerun Majalisar Dokoki na sanata da wakilai 2 a yankin Abuja da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata, ya zo wa jama’a da dama da mamaki. Magoya bayan jam’iyyar a baya lokacin da Jam’iyyar PDP ke mulkin kasar nan, sun yi ta kurarin cewa jam’iyyar adawa ce ke nasara a Abuja a dukan zabubbuka, amma sai Jam’iyyar PDP ta yi amfanin da karfin mulki ta murde zaben.
Sai ga shi a yanzu a lokacin da APC take kan mulkin, ta rasa daukacin kujerun ’yan majalisa 3 da suka hada da ta dan takarar Majalisar Wakilai daga Abuja ta Arewa da ta kunshi kananan hukumomin Birni da Kewayen Abuja (AMAC) da Bwari. Sai kananan hukumomi 4 da suka hada da Gwagwalada da Kuje da Kwali da kuma Abaji na dan Majalisar Wakilai a shiyyar Kudancin Abuja. Sai kuma kujerar Sanata 1 da ke wakiltar daukacin yankin a Majalisar Dattawa.
Jam’iyyar APC ta rasa daukacin kujerun 3 da kuma ta Shugaban Kasa inda Jam’iyyar PDP ta samu galaba da kuri’a dubu 259 da 997 da dan takararta Atiku Abubakar ya samu, yayin da APC ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta samu kuri’a dubu 152 da 224 a yankin na Abuja.
Sakamakon zaben ya nuna cewa Mista Michah Jiba da ya yi takarar Majalisar Wakilai a Arewacin Abuja karkashin Jam’iyyar PDP ya samu rinjaye da kuri’a dubu 174 da 377 inda ya kada abokin hamayyarsa Mustapha Lamurde na Jam’iyyar APC da ya samu kuri’a dubu 82 da 761, kamar yadda babbar jami’ar tattara sakamakon zaben, Farfesa Rebeca Wusa Ndana ta bayyana.
Haka dan takarar Majalisar Wakilai na Jam’iyyar PDP a shiyyar Abuja ta Kudu Alhaji Hassan Sokodabo ya yi nasara a kan abokin hamayyarsa na Jam’iyyar APC, Alhaji Zakari Angulu Dobi. Ya samu kuri’a dubu 81 da 23 adadin da ya dara na abokin hamayyarsa daga APC wanda kuma shi ne ke kan kujerar a halin yanzu, wanda ya samu kuri’a dubu 65 da 123, kamar yadda babban jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Titus Idekwe ya bayyana.
Wanda ke kan kujerar Sanata daga yankin Abuja, Sanata Philip Tanimu Aduda na Jam’iyyar PDP ya samu nasara a kan abokin hamayyarsa na APC, Mista Zephaniah Jisalo da kuri’a dubu 263 da 55, adadin da ya dara na dan takarar APC wanda ya samu kuri’a dubu 148 da 401 kamar yadda babban jam’in tattara sakamakon zaben Farfesa Sani Saka ya bayyana. Ya dai samu nasarar ce a daukacin kananan hukumi 6 na Abuja.
Masu sharhi kan siyasar Abuja da dama sun ta’allaka rashin nasarar jam’iyyar ta APC a dukan kujerun da kuma na Shugaban Kasa a yankin da dalilai daban-daban.
Wani jigo a Jam’iyyar APC a yankin Abuja Alhaji Yusuf Tanko ya ce, babban abin da ya jawo wa jam’iyyar tasu matsala shi ne matakin dauki-dora da jam’iyyar ta yi amfani da shi wajen tsayar da daukacin ’yan takarar nata 3 bayan ta wahalar da ’yan takarar tare da mambobinta ta hanyar karbar kudin fam mafi tsada a tarihi da kuma gudanar da zabe “Na kato bayan kato” a daukacin yankunanta na Abuja.
Ya ce, “Ka ga da farko wanda ya zo na daya a zaben fitar da gwani na Sanata shi ne dan Majalisar Wakilai daga shiyyar Abuja ta Kudu a yanzu, wato Alhaji Zakari Angulu Dobi, sai kuma Alhaji Jibrin Usman Wowo ya zo na 2. “Amma sai aka tsayar da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar AMAC da Bwari daga shiyyar Abuja ta Arewa, Mista Zephaniah Jisalo da bai kai wata uku da dawowa jam’iyyar ba. Hakan ya fusata al’ummar Abuja ta Kudu da suka jima suna tare da Jam’iyyar APC tun tana adawa sannan sun jima suna neman kujerar ba tare da nasara ba. Abu na biyu kuma kabilar Gbagyi wadda ita ce babbar kabilar ’yan asalin Abuja sun jima suna tafiya da Jam’iyyar PDP da shi kansa Sanata Aduda da ya jima yana yi musu hidima, to raba su da shi sai an yi da gaske.”
“Sannan ga shi daukar Zephaniah don a dadada musu bai shawo kansu ba, saboda suna cewa shi bai taimaka wa al’umma irin na Aduda, ka ga ke nan sun fusata ’yan Kudancin Abuja kuma ba su iya shawo kan ’yan Arewacinta ba,” inji shi.
Haka a bangaren kujerar Majalisar Wakilai, dan siyasar ya ce jam’iyyar ta APC ta tsayar da Dokta Mustapha Lamorde wanda da ne ga mai taimaka wa Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya A’isha Buhari, wato Hajiya Hajo Sani da ba a san shi ba a siyasar Abuja, sabanin wadanda aka ce na gabansa a yayin zaben fid da gwanin, wato Barista Amanda Pam da Malam Yakubu Muhammad da kuma Mista Isa Dara, wadanda sun jima a jam’iyyar tare da yi mata hidima.
Ya ce, wadannan ’yan takarar da ke da tarin mabiya da tasiri a siyasar yankin, rashin tsayawarsu ta shafi kuri’ar da shi kansa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ka iya samu daga wajen mabiyansu. “Haka al’ummar yankin musamman Gbagyi ba su san siyasar “Ungulu da kan zabo ba” idan suka ta shi zabe daga sama har kasa sak suke yi, ba za su zabi APC a nan ba sannan su zabi PDP a can, ka san mutanenmu na karkara, hakan zai yi masu wuyar tantancewa,” inji shi.
Wani jigo a Jam’iyyar APC a garin Kubwa a yankin Birnin Tarayya, Abuja Malam Usman Umar, ya ce Jam’iyyar APC na da aiki ja a gabanta idan har tana son ta gyara tafiyar. Ya ce, babbar kabilar Abuja ta Gbagyi ta jima tana tafiya da PDP, kuma a yanzu ta kulla alakar siyasa da kabilar Ibo wadanda ya ce ba su faye zuwa garuruwansu na asali ba a lokacin zabe, sabanin ’yan Arewa. Ya ce, shawo kansu daga barin jam’iyyar da suka dauka kamar addini na bukatar gagarumin aiki.
“Dole ne manyan mutane irin su Ministan Abuja su ja su a jiki sosai tare da tafiya da su a al’amura. Haka ya ce, su kansu wadanda suka yi wa jam’iyyar hidima ba a jansu a jiki a tafi da su a al’amura ta yadda za su yi tasiri a lokacin zabe,” inji shi.
Wadansu daga cikin wadanda suka yi wa jam’iyyar aiki a lokacin zabe da Aminiya ta zan ta da su, sun ce jam’iyyar ba ta wadata su da kudi “abokin aiki” ba, kamar yadda suka ce, an bai wa takororinsu na PDP, bare su ba da kyaututtuka musamman ga mazauna karkara kamar yadda Jam’iyyar PDP ta saba yi a lokacin zabe.
Wannan nasarar da jam’yyar ta PDP ta samu na faruwa ne a lokacin da jam’iyyar ke matsayin marainiya a yankin Abuja, kasancewa a karon farko ba ta rike da matsayin shugabancin karamar hukuma ko da guda a cikin kananan hukumomi 6 na yankin.
Su ma shugabannin kananan hukumomin 6, za su fuskanci hisabinsu a ranar Asabar ta makon gobe lokacin da jihohin kasar nan ke zaben gwamnoni da na ’yan majalisarsu na jiha, inda bayanai suka ce Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello ya gargadi “Ciyamomin” su guji nuna kabilanci wajen kin mara wa ’yan takarar Jam’iyyar APC baya. Kuma su guji yin zagon kasa a lokacin zaben, a matsayin sharadi na mara masu baya a zabensu da ke tafe.