Dalilan da Donald Trump ya lashe zaɓen Amurka

Me lashe zaɓen Donald Trump yake nufi ga Amurka? Ta faru ta ƙare – an yi wa mai dami ɗaya sata. Ta dai tabbata Donald Trump zai yi kome fadar White House a ranar 20 ga watan Janairun baɗi a matsayin Shugaban Amurka na 47. Shugaban ƙasar na yanzu, Joe Biden ne ya kayar da […]

Dalilan da Donald Trump ya lashe zaɓen Amurka

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump

Me lashe zaɓen Donald Trump yake nufi ga Amurka?

Ta faru ta ƙare – an yi wa mai dami ɗaya sata. Ta dai tabbata Donald Trump zai yi kome fadar White House a ranar 20 ga watan Janairun baɗi a matsayin Shugaban Amurka na 47.

Shugaban ƙasar na yanzu, Joe Biden ne ya kayar da shi shekara huɗu da suka gabata.

Tun gabanin a sanar da sakamakon zaben a hukumance ne Trump ya yi wa magoya bayansa jawabi, inda a ciki ya bayyana cewa, ya samu gagarumar nasara a zaben.

Trump ya gode wa magoya bayansa a wani jawabi da ya gabatar, yana mai cewa, “Amurka ta ba mu wata babbar dama da ba a taba ganin irin ta ba.”

Trump ya fi mayar da akalar yaƙin zabensa ne kan farfaɗo da tattalin arziki da yaƙi da kwararowar baƙin haure zuwa Amurka.

Sakamakon zaben da aka gudanar ranar Talata ya nuna yadda Trump ya samu ƙuri’un da suka kai shi ga lashe zaben tare da samun rinjayen wakilan zabe na Shugaban Ƙasa da ake kira da Electoral College.

Nasarar tasa ta kuma fito fili ne daga ƙuri’un wasu muhimman jihohin da aka sa ido sosai a kansu.

Sakamakon zaben zai ci gaba da jan hankali, musamman ganin yadda ya kawo wani sabon shafi a tarihin siyasar Amurka, inda Trump zai zama ɗaya daga cikin tsoffin shugabannin Amurkar da suka sake komawa kan mulki bayan shekara huɗu.

Har ila yau, zaben 2024 ya janyo hankalin duniya saboda zai iya kawo sauye­sauye a manufofin Amurka a fannonin tattalin arziki da shige da fice da tsaro da kuma dangantakar Amurka da sauran ƙasashen waje.

Muhimman ababuwan da suka taimaka wa Trump lashe zaɓe

A cewar wata ’yar Nijeriya da take zama a Amurka fiye da shekara 30 mai suna Huraira Musa, batutuwa da dama ne suka taimaka wa Trump lashe zaben.

Ɗaya daga ciki shi ne yadda fitar ɗangon da Turawa suka yi domin kaɗa masa ƙuri’a, inda aka ƙiyasta cewa, aƙalla kashi 71 na fararen fata ne suka jefa ƙuri’unsu – lamarin da ya zama ba saban ba a tarihin zaben Amurka cikin shekaru.

Tace,“sannanAmurkawan Latin da ake kira Latinos (Amurkawa ne da asalinsu ko kuma barbararyawan Sipaniyawa ne) da su ma suka yi fitar ɗango wajen zabar Trump.

Haka kuma, akwai kuma ɗalibai fararen fata da a baya ba su cika yin zabe ba, a wannan karon sun fito sosai domin kaɗa ƙuri’a, kuma kusan dukkansu Trump suka zaba. Wannan shi ake ganin kamar yana da nasaba da batun wariyar launin fata. Ba za su so a ce mace baƙar fata ta zama shugabar ƙasa a ƙasarsu ba.

Duk wani batu da ake yi cewa saboda dalilai na tattalin arziki ko manufofin Amurka a ƙasashen waje – kamar dai an fake ne da guzuma, domin a harbi karsana.

Ka san a 2016, Amurkawa sun ƙi zabar mace farar fata ’yar uwarsu – yanzu za su ce babu dalilin da zai sa su zabi mace baƙar fata a matsayin shugabar ƙasa.

Hakazalika, Trump ya samu ƙuri’un maza fiye da kashi 10 cikin 100 ɗari a kan yadda maza suke zabe,’’ in ji Huraira.

Muhimman abubuwa 6 da suka faru a zaɓen

Bayan sanar da Donald Trump a matsayin zababben Shugaban Ƙasar Amurka, ga wasu muhimman abubuwa guda shida da suka faru.

Donald Trump ya samu nasarar yin kome a fadar shugaban ƙasar bayan doke Kamala Haris.

Trump ya samu nasarar wuce ƙuri’u wakilan zabe guda 270 da ake buƙata domin zama shugaban ƙasa. Tun da farko, a jawabinsa da magoya bayansa a Florida ya ce, ya samu gagarumar nasara.

Trump ya yi kamfe ne da alƙawarin inganta tattalin arzikin ƙasar – inda ya yi alƙawarin yaƙi da hauhawar farashi da tsuke iyakokin ƙasar domin hana kwararowar baƙin haure da gina katanga tsakanin Amurka da Meziko.

Har zuwa ranar Laraba da rana – an ci gaba da tattara sakamakon zaben daga wasu jihohi, ciki har da masu muhimmanci guda uku – Neɓada da Michigan da Arizona.

Wani sauyi da aka samu shi ne yadda Jami’iyyar Republican ta ƙwace rinjayen majalisar dattawa.

Yadda Trump zai fuskanci yaƙe-yaƙen da ya gada

Donald Trump na yawan nanata cewa, zai kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe, amma zai gaji manyan yaƙe-yaƙe guda biyu: Yaƙin Rasha a Ukraine da yaƙin Isra’ila a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda wakilin BBC a harkokin tsaro, Frank Gardner ya bayyana.

Haka kuma akwai Koriya ta Arewa, wadda ke yunƙurin assasa makamashin nukiliya da kuma hasashen da ake yi China za ta ƙara mamaye Taiwan, wadda ƙawar Amurka ce.

Yadda Trump zai fuskanci waɗannan yaƙe-yaƙe abu ne da ba za a iya fahimta ba a yanzu, musamman ganin a yanzu da ba ya tare da fitattun janarorin soji da suka yi aiki a tare a wancan gwamnatin.

Sai dai kuma barin abokan hamayyarka cikin duhu yana da muhimmanci a irin wannan yanayi.

Shin zai tursasa Putin ya shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Ukraine da iya dawo da Shugaban Ƙasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-Un teburin sulhu? Zai iya hana Beijjing mamaye Taiwan da iya tursasa Iran ta dakatar da ƙungiyoyin da take ɗaukar nauyi domin hana Isra’ila, wadda take samun goyon bayan Amurka kai hari a cibiyoyin makamashin nukiliyarta?

Waɗannan  amsoshi lokaci ne kawai zai iya ba da amsarsu.

Waiwaye kan wasu manufofin Donald Trump

Yanzu da Donald Trump ya zama zababben shugaban ƙasar Amurka, bari mu yi waiwaye kan wasu ƙudurorinsa.

Tattalin arziki: Trump ya yi alƙawarin yaƙi da hauhawar farashin kayayyaki a Amurka. Ya ce, zai yi hakan ne ta hanyar ƙarfafa makamashi da samar da wasu wuraren haƙo albarkatun man fetur.

’Yan ci-rani: Trump ya sha bayyanawa a lokacin yaƙin neman zabensa cewa, zai tsuke iyakokin ƙasar, tare da ƙarasa gina takangar da ke tsakanin Amurka da Meziko. Ya kuma yi alƙawarin korar ’yan ci-rani da ba a taba gani ba.

Haraji: A game da haraji, ya ƙirƙiro wasu ƙarin haraji, ciki har da wasu waɗanda ya bullo da su a 2017, waɗanda ake zargi za su fi taimakon masu arziki.

Sauyin yanayi: A baya ya bullo da ɗaruruwan hanyoyin kare muhalli, ciki har da rage fitar da iskar daga kamfanoni da ababen hawa. Yanzu ma ya ƙuduri aniyar ɗorawa kan wannan ƙuduri.

Zubar da ciki: Trump bai fito ƙarara kan matsayarsa a game da zubar da ciki ba, duk da yakan bayyana shi a matsayin ’yanci. Sai dai alƙalan Kotun Ƙoli uku da ya naɗa a zamaninsa na cikin waɗanda suka warware hukuncin Roe da Wade, wanda hukunci ne da aka yi domin ba mata ’yancin zubar da ciki.