Dalilan da maza masu nakasa basu son auren mace irinsu

Idan na zo na auri makauniya ko gurguwa ba za a samu zaman lafiya ba.

Dalilan da maza masu nakasa basu son auren mace irinsu

Wasu maza masu nakasa

Auren nakasassu bai bambanta da sauran auren ba, saboda masu nakasa suna da kwadayin samun abokan zama wanda za a gina a kan soyayya har ta kai ga sun samu iyali.

Sai dai Aminiya ta tattauna da wasu maza masu nakasa a kan dalilan da ya sa basu son auren nakasassahiya.

Rabiu Adamu wani nakassahe [mai hannu daya] ya ce “idan kika duba ni nakasasshe ne, akwai ayyuka a gida da dole yana da bukatar tallafi.

“Idan ta kasance ita gurguwa ni gurgu dole muna bukatar wanda zai tallafa mana wajen wasu aikace-aikace.

“Misali makaho ba zai iya aurar makauniya ba dole sai ya nemo dan jagora wanda zai zauna yana musu abubuwa.

“Saboda haka idan na auri mai lafiyayyun gabobi za ta taimaka min a wasu ayyuka wanda nima zan samu sauki ke nan.”

Hassan Zaria, wani gurgu dan asalin Jihar Kaduna ya ce ba zai iya auren nakasasshiya ba domin shi ma nakasasshe ne.

“Idan na auri nakasasshiya ba za ta iya kulla da ni ko ta yaya zan kula da ita, misali a gida ta yaya za mu iya sarrafa gida ko kula da gida.

“A yanzu da kafafuna basu da amfani idan na zo na auri makauniya ko gurguwa ba za a samu zaman lafiya ba.

Haka shi ma wani makaho mai suna Yakubu Samaila, ya ce “ni makaho ne bana iya ganin abubuwa ba a tsamanin zan auri makauniya kamar ni.

“Zan iya hakura da gurguwa amma ba makauniya ba domin zan so na auri wadda take ganin tun da bana gani.”

Wadannan matsalolin ba mata kadai suke shafa ba har da mazan, kasancewar su ma nakasassun mata ba sa son aure nakasasshe.

Galibi mata masu nakasa na son auren namiji mai lafiyayyun gabobi kafin saboda gudun shan wahala.

Aminiya ta ruwaito cewa nakasassun mata a Najeriya sun koka kan yadda maza ke kin neman aurensu har ma da kuma yadda wasu mazan ke nuna masu kyama saboda nakasar da Allah Ya dora masu.

Sun bayyana yadda suke shan wahalar samun mazajen aure a duk lokacin da suka isa aure da yadda ake barinsu su rika rayuwa cikin kadaici ba tare da samun abokin zama ba.

Shugabar Hadaddiyar Kungiyar Nakasassu ta Kasa ce ta bayyana haka a wani taron bikin Ranar Mata ta Duniya da aka shirya a Jihar Edo.

A jawabin da ta yi a wajen taron kamar yadda Jaridar Leadership ta wallafa, ta ce yanzu babban kalubalen da mata nakasassu ke fuskanta shi ne matsalar rashin samun mazajen aure a kasar nan baya ga matsalar kyama da wariya da ake nuna masu a makarantu da wuraren ayyuka.

Ta ce “babbar matsalar da mata nakasassu ke fuskanta shi ne matsalar wariya ta bangaren aure da ake nuna masu, ta inda maza hatta nakasassun mazan ke kin nemansu da aure.”

Ta kara da cewa “a wasu lokutan ma har gatsari ake masu da cewa shin su ma suna lissafa kansu cikin sahun mata ne.”

A karshe ta yi kira ga jama’a da su tausaya su rika auren mata masu wannan larura saboda irin halin a tausaya masu da suke shiga.