Dalilan da ma’aurata ke bincikar wayar junansu
Da take zantawa da wakilinmu, wata matar aure, Ummu Salma Yahya Isah cewa ta yi, ita a wurinta, don mace ta ɗauki wayar mijinta ta duba ba wani abu ba ne.
Bincikar wayar miji da matan aure ke yi wata matsala ce da ta ɓullo tsakanin ma’aurata wacce take haddasa zargin juna wanda daga ƙarshe yake zama sanadin hatsaniya wani lokci ma har da rabuwar aure.
Ba mata kawai suke bincikar wayoyin mazan aurensu ba, hatta maza ma sau tari akan samu suna bibiyar wayoyin matansu don ganin wa mace ta kira ko wa ya kira ta. Wasu mazan ma kan bibiyi irin shafukan sada zaumuntar da matansu ke ta’amali da su a kan intanet.
A wasu lokutan akan samu mazajen da ke hana matansu shiga kafafen sada zumunta nbaki ɗaya ko ma su hana matan nasu riƙe babbar wayar don gudun abin da ka iya zuwa ya komo.
Wanna matsala ba ta tsaya a tsakanin ma’aurata kawai ba, tana shiga har tsakanin saurayi da budurwarsa. Kuma ta sha haddasa fasa auren da aka riga aka tsara komai idan zargi ya shiga kuma ya yi matuƙar tasiri.
Aminiya a wannan makon ta yi nazari mai zurfi dangane da wannan matsala kuma ta kawo sabubban wannan matsala da irin illar da take haddasa wa a tsakanin masoya.
Ya kamata mace ta duba wayar mijinta
Da take zantawa da wakilinmu, wata matar aure, Ummu Salma Yahya Isah cewa ta yi, ita a wurinta, don mace ta ɗauki wayar mijinta ta duba ba wani abu ba ne.
Ta ce abubuwan da maza ke yi na kaffa-kaffa da wayarsu, yake sa mata tunanin akwai abin da ake ɓoye masu.
Ummu Salma ta ce sau tari, idan mace ta ce mijinta, ya ara mata wayarsa, domin ta yi kira, sai ya ƙi ya ba ta kuɗi ya ce ta sayi kati. Wannan kaɗai, zai iya sa mace ta ji tana son ta san abin da yake ɓoye mata.
“Gaskiya bai dace mace ta riƙa bibiyar wayar mijinta ba. Idan mace tana son hankalinta ya kwanta, ta guji bibiyar wayar mijinta. Domin sau da dama, waya ce take kawo matsala a tsakanin ma’aurata.
Don haka, a zamantakewa tsakanin miji da mata, a yi wa juna kyakyawan zato. Kuma a kyautata wa juna, amma maganar waya, kowa ya riƙe tasa. Kada mace ta taɓa wa mijinta waya, domin kada a zo a sami matsala,” in ji ta.
Zargin ke sa mace bibiyar wayar miji
Malama Amina Muhammad cewa ta yi a ganinta, rashin yarda ce take sa mata suke sanya idokan wayoyin mazajensu.
Ta ce, “gaskiya, bai dace mace ko namiji su riƙa bibiyar wayar junansu ba. Ya kamata kowa ya riƙe wayarsa.
“Idan mace ko namiji, suka yi wani zargi a zuciyarsu, suka je suka duba wayar wani a cikinsu, za su ga abin da zai dame su. Don haka, kowa ya riƙe wayarsa, amma idan miji ya ce ka ɗauka ka duba, shi ke nan babu damuwa, sai ka ɗauka ka duba.
“Amma a ra’ayina, haka kawai bai kamata mace, ta je tana duba wayar mijinta ba, ko kuma miji ya je yana duba wayar matarsa”.
Ummul Khari Abdulmuminu Iliyasu cewa ta yi, akasari abin da ya sa mata suke sanya ido kan wayoyin mazajensu, shi ne rashin yarda da bin ƙwaƙwaf.
Ta ce kishi da yawancin mata suke ɗora wa kansu ne ya sa suke ganin ta haka ne zai sa su san halin da mazajensu suke ciki.
“A tunanin wasu matan kuma, ta haka ne za su san hanyar da za su ɗauki wani mataki na hana wani abin da ba sa son ya faru.”
Ummul Khari ta ce bai dace ba, mace ma’aurata su riƙa bibiyar wayar junansu ba “domin wannan alama ce ta zargi, shi Kuma zargi, ba ya haifar da alheri.”
Sheɗan ke zuga mata su duba wayoyin mazansu
Ta ce wani lokaci ma, abin da za ka gani bai kai ya kawo ba, amma saboda mutum ya sanya zargi a zuciyarsa, sai sheɗan ya mayar da shi babban abu, yadda zai haifar da babban rikici a tsakanin ma’aurata.
Ta ce saboda haka, bai kamata kowanne lokaci ma’aurata su riƙa bibiyar wayar junansu ba. Amma duk da haka, mutum zai iya bincike wani lokaci, idan ya ga wani abu da zuciyarsa, ba ta amince da shi ba, domin ya gane abin da ke faruwam, “amma haka kawai mata su riƙa bibiyar wayar mazajensu, bai dace ba.
“Ya kamata duk mutumin da za ka aura, ya kasance akwai aminci da yarda a tsakaninku. Ka san waye za ka aura shi ma ya san wace zai aura. Ni ina ganin idan akwai wannan, babu maganar a je ana bibiyar juna. A yi haƙuri a yarda da juna, a riƙa kyautatawa juna zato.
“Idan akwai wani abu da ake tunanin wani yana yi mara kyau a roƙa masa Ubangiji, Ya ba shi ikon gyarawa. Idan abin ya yi muni, sai a dubi mene ne mafita. Amma yawan bibiyar waya, gaskiya ni a ganina ba shi da amfani, domin sharrinsa yafi alherinsa yawa”.
Soyayya ke sa mata duba wayar mijinsu
Zulaiha Aliyu ta bayyana cewa, abu na farko da ke sa yawaicin mata sanya ido kan wayoyin mazajensu, shi ne soyayya sai kuma kishi, “ko suna ganin cewa mazajen nasu suna mu’amuala da wasu matan a waje.”
Ta ce, “amma ba shi da wani mahimmanci mace ta sanya ido kan wayar mijinta. Saboda ba ta isa ta hana shi ba, ba ta isa ta sanya shi ba. Don haka, idan ma zai nemi mace ne, ba ta isa ta hana shi ba.
“Sanya ido a kan waya zai iya kawo matsaloli da damuwa a tsakanin ma’aurata.
Don haka, mace ta kau da kanta daga abin da babu ruwanta, shi ne yafi, domin ta iya yiwuwa ma, abin da ake tunani ba haka ba ne.
“Yanzu misali kamar namiji ɗan kasuwa, zai iya kasuwanci da mace, kuma zan iya kasuwanci da namiji. Wata za ta iya kiran shi da niyar kasuwanci. Don haka, ma’aurata su ɗauke kansu daga wayoyin juna, shi ne zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman a wannan lokaci da muke ciki”.
Ya kamata ma’aurata su ɓoye wayoyinsu
Amman wani magidanci, Alhaji Abdulsalam Abubakar Magaga, ya ce, ya dace, ma’aurata su riƙa ɓoyewa juna abin da ke cikin wayarsu, “saboda ita harkar waya, tana da sirri da yawa a cikinta. Na farko akwai harkar kuɗi, akwai harkar kasuwanci, akwai harkar amana da kuka yi da wasu.”
Ya ce a kullum idan an ce a ɓoyewa juna sirrin da ke cikin waya, sai wasu su ɗauka saboda baɗala ne. Ko kuma a ce mutum yana da budurwa ne, ko yana da wata mata da suke harkar banza, shi ne ake ɓoye sirrin da ke cikin waya.
Wayar mutum sirrinsa ne
“Ni a wurina, ba zan nuna wa matata wayata ba saboda a cikin wayata ina da asusun ajiyata na banki, ba kowa ne zai nuna wa matarsa lambar sirri ta asusun ajiyarsa ta banki ba, ko ya nuna wa matarsa harkokin kasuwanci da yake yi ba, ko abin da ke cikin asusun bankinsa, haka ita ma ba za ta nuna wa mijinta ba.
“Don haka, ban ga dalilin ce-ce-ku-ce ba, don na ɓoye wa matata sirrin wayata, domin idan na nuna mata wayata, duk sirrina na banki da harkokinkasuwanci da amanar da muka yi da wani, wanda da ni muka yi amanar ba da ita ba, duk za ta gani. Don haka, kowa ya riƙe sirrin wayarsa.”
Ya kamata miji ya bibiyi wayar matarsa
Shi kuma Auwalu Garba mai siminti cewa yi bai dace mace ta riƙa bibiyar wayar mijinta ba, amma ya dace miji ya bibiyi ta matarsa.
Ya ce, ita mace, mai rauni ce ko ɗan yaya wani zai iya canza mata ra’ayi. Amma zai yi wuya wani ya canza wa miji ra’ayi a kan matarsa. Don haka, ya dace miji ya bibiyi wayar matarsa, domin ya riƙa ganin halin da take ciki.
Duba waya ya kashe aure
“Ni na ga auren wata mata da ya mutu, domin tana tura wa wani hoton al’airarta ta waya, da mijin ya gani auren ya mutu. Don haka, ya dace miji ya binciki wayar matarsa.”
Duba waya zai ƙara danƙon soyayya
To amma shi wani magidanci, Muhammed Aminu Babangida, cewa ya yi idan ma’aurata, sun yarda da junansu, don sun bibiyi wayar junansu ba laifi ba ne.
Ya ce amma idan akwai zargi, a tsakaninsu, musamman tun kafin a yi auren, da bayan auren, to a kiyayi wayar juna, shi ne mafi alheri da zaman lafiya a tsakaninsu.
Amma idan sun yarda da junansu kan su ya haɗu, za su iya bibiyar wayar junansu. Yin haka ma, yana ƙara danƙon soyayya.
Addini ya hana neman laifin mutum
Wakilinmu ya tuntuɓi Babban Limamin Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna kuma Malami a Tsangayar Koyar da Ilmin addinin Musulunci Mai zurfi ta Jami’ar Jihar Kaduna, Sheikh Imam Muhammad Sulaiman, kan abin da addinin Musulunci ya ce kan wannan al’amari.
Sheikh Imam Muhammad Sulaiman ya ce, “shi bincike, ba wai na waya kaɗai ba, kowanne irin bincike Musulunci ya hana mutum domin ya gano laifin wani.
Ya ce, “Musulunci addini ne, wanda yake son kowa ya zauna da kowa lafiya kuma ba a son ya zamanto yana neman laifin ɗan uwansa. Don haka, Manzon Allah (SAW) ya ce mumunai ’yan uwan juna ne, kada ka ɗana tarko a neman laifin ɗan uwanka.”
Sheikh Sulaiman ya yi bayanin cewa waya sirri ce ta mutum, don haka, bai kamata wani ya ɗauki wayar ɗan uwansa, mace ce ko namiji ba ya bincika. Amma shi namiji zai iya bincikawa, don shi an ɗora masa haƙƙin lafiyar matarsa.
“Ko shi ma, ba a ce komai ya riƙa bincike ba, don zai iya gano abin da baya so. Haka ita ma mace, bai kamata ta ɗauki wayar mijinta ta riƙa bincike a kai ba domin ta gano wanda yake magana da shi ba. Wannan duk yana jawo matsaloli.
Husaini Isah, Jos da Abbas Ɗalibi, Legas da Fatima Maikasuwa, Abuja da Rahima Shehu Dokaji, Kano da Hauwa Abubakar
Ci gaba a nemi Jaridar AMINIYA