Dalilan da mata ke son miskilin namiji
Mata da yawa sun fi son maza masu dabi’ar ta miskilanci fiye da masu haba-haba.
Ana yawan ganin miskilai a matsayin mutane masu girman kai ko raini da wulakanci saboda shiru-shirunsu, sai dai kuma ba haka abin yake ba, dabi’arsu ce haka.
Sai dai kuma duk da haka, mata da yawa sun fi son maza masu wannan dabi’ar ta miskilanci fiye da mutum mai haba-haba.
- Marwa ya yi gargadi kan halasta tabar wiwi a Najeriya
- WHO ta ba da izinin amfani da rigakafin COVID-19 da Indiya ta samar
Mujallar Tozali ta kawo dalilan da ke sa mace ta so miskilin namiji kamar haka:
- Suna da kokarin saurarar mutane saboda ba su damu da sha’anin mutane ba.
- Samun isasshen lokacin magana da mutane saboda ba su da yawan magana da mutane daban-daban
- Sun iya kwantar da hankalin yarinya saboda shirun yana basu damar su lakanci halayyar mutane.
- Suna da saurin fahimtar zancen mutane saboda ba kowace magana suke maida hankali a kai ba.
- Ba su da saurin mita ko korafi saboda shiru-shirunsu.
- Ba su da nuna takama da alfahari da suke da shi saboda su ba su ga dalilin yin hakan ba.
- Sukan koya wa mace yadda za ta kula da kanta saboda lokacin da suke da shi na nazartar halayyarta.