Dalilan da suka janyo mutuwar mutum 14 a Bauchi – Kwamishinar Lafiya

A kwanan baya ne aka samu rahoton bullar cututtuka a Jihar Bauchi har al’amarin ya janyo rasuwar wadansu mutane. Wannan ne ya sa Kwamishinar Lafiya ta Jihar Bauchi Dokta Zuwaira Hassan ta zanta da manema labarai inda ta yi karin bayani game da sanadiyyar rasuwar mutanen da yadda ya kamata mutane su kare kansu daga […]

Dalilan da suka janyo mutuwar mutum 14 a Bauchi – Kwamishinar Lafiya

A kwanan baya ne aka samu rahoton bullar cututtuka a Jihar Bauchi har al’amarin ya janyo rasuwar wadansu mutane. Wannan ne ya sa Kwamishinar Lafiya ta Jihar Bauchi Dokta Zuwaira Hassan ta zanta da manema labarai inda ta yi karin bayani game da sanadiyyar rasuwar mutanen da yadda ya kamata mutane su kare kansu daga kamuwa da cututtuka:

 

An samu labarin cewa ana fama da cutar kwalara a Jihar Bauchi haka ne?

Gaskiya ita wannan cuta ta kwalara akwai ta. Tun kimanin mako hudu ko biyar da suka gabata muka samu labarin bullarta.

 

Kamar mutum nawa ne suka kamu da cutar kuma nawa ne suka rasu?

Tun lokacin da cutar ta fara mun samu mutum 324 da suka kamu da cutar, cikinsu mun rasa mutum tara. Cikin wadanda suka rasu akwai wadanda suka kamu da cutar kuma suna fama da wasu cututtuka kamar ciwon sukari da ciwon hawan jini da makamantansu. Kuma kwanan nan mun samu bullar cutar a Kwalejin Ilimi da ke Kangere inda har dalibi mai shekara 22 ya rasu. Haka akwai cutar zazzabin bera da ake ce mata (zazzabin Lassa) ita ma mun samu mutum 44 da suka zo asibiti daga cikinsu mutum biyar sun rasu saura kuma suna karbar magani.

 

kananan hukumomi nawa ne wannan cuta ta bulla?

An samu daya daga karamar Hukumar Toro, a garin Ribina, an samu uku a karamar Hukumar Ganjuwa, a karamar Hukumar Tafawa balewa an samu daya a Bula, a karamar Hukumar Darazo ma an samu daya kuma an samu a karamar Hukumar Bauchi.

 

Wasu matakai kuka dauka domin shawo kan matsalar?

Ka ga kamar makarantar Kangere da yake suna da karancin makewayi, wadansu har cikin daji suke zuwa suna bayan gida, sun ce makewayin sun cika, an fara kwashewa, kuma ana fadakar da su kan yadda za su kiyaye kansu. Amma a cikin gari akwai mutane wadanda ake kira masu taimako a cikin al’umma (Community boluteers), suna yawo gida-gida duk wanda suka samu da cutar amai da gudawa za su kawo shi asibiti sannan duk gidan da aka samu da cutar za a sa magani a ruwan shansu da kuma bayan gidansu, kuma ana duba yadda makewayinsu yake, in suna bayan gida a makewayi da ba mai amfani da ruwa ba to shi ma ana kwashewa, sannan gidajen rediyo da talabijin muna fadakarwa muna fada wa mutane yadda za su kiyaye kansu.

 

Wane sako kike da shi ga jama’a?

Muna kira ga jama’a don Allah mutum da ya fara amai da gudawa ya kai kansa Asibitin Koyarwa na Jam’iar Abubakar Tafawa balewa da ke nan Bauchi, kyauta za a duba shi, yin haka zai sa ya samu lafiya sannan kuma zai taimaka saboda sauran mutane da ’yan uwansa kada su kamu. 

Da yake an fara ruwa ya kamata yara matasa a hadu akwashe datti, a bude magudanun ruwa domin kwayar cutar kwalara tana fita ne a bayan garin da mutane ke yi, idan ba haka ba ruwa zai kai cutar cikin ruwan shanmu ko abincin da za mu ci. A yi kokari a kwashe bayan gida idan ya cika, don kudin da za ka kashe wajen kwashe shaddar ya fi sauki a kan kudin da za ka kashe wajen jinya ko wahalar da za a sha ko kuma mutuwar da za a yi. Sannan a kula da wanke hannu idan mutum ya yi bayan gida ya wanke hannunsa ko da sabulu ko da toka, haka mata idan za su dafa abinci a wanke hannu da sabulu ko toka, sannan kafin a ci abinci a wanke hannu. Kuma ya kamata mutane su rika tafasa ruwan da za su yi amfani da shi ko su sanya maganin kare ruwa mai suna (water guard) akwai sinadarin da ke kashe kwayoyin cuta a ciki. Kuma zan yi amfani da wannan dama in gode wa Gwamnatin Tarayya da Gwamnan Jihar Bauchi saboda matakan gaggawa da suka dauka domin shawo kan yaduwar cutar.