Dalilan da suka sanya Buhari bai sanar da majalisa tafiyarsa Birtaniya ba
Aminiya ta gano cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai sanar da majalisar tarayya a rubuce cewa zai yi balaguro zuwa kasar Biryaniya ba. A zaman da majalisar ta yi jiya, Shugaban Majalisar Bukola Saraki ya karanta wasiku hudu wadanda shugaban kasar ya aike wa majalisar amma babu wasikarsa ta tafiya Birtaniya a ciki. A […]
Aminiya ta gano cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai sanar da majalisar tarayya a rubuce cewa zai yi balaguro zuwa kasar Biryaniya ba.
A zaman da majalisar ta yi jiya, Shugaban Majalisar Bukola Saraki ya karanta wasiku hudu wadanda shugaban kasar ya aike wa majalisar amma babu wasikarsa ta tafiya Birtaniya a ciki.
A baya Buhari ya rika sanar da majalisar dukkanin baraguron da ya rika yi a rubuce kamar yadda sashen na 145 karamin sashen na 1 na kundin dokokin Najeriya ya tanada.
Shugaban ya bar Najeriya a ranar Litinin zuwa kasar Birtaniya kuma zai ci gaba da kasancewa a can har zuwa ranar 20 ga watan Afrilu.