Dalilan da suka sanya da wuya ’yan kwallon Najeriya su iya lashe kyautar Gwarzon dan kwallon Duniya (Ballon D’or)
Tun lokacin da aka fara gasar Gwarzon dan kwallon Duniya a shekarar 1991, babu dan kwallon Najeriya da ya taba lashe gasar. Ko a shekarar 1996 da kuma 1999 a lokacin da shahararren dan kwallon Najeriya Kanu Nwankwo yake tashe, bayan ya lashe Gasar Gwarzon dan kwallon Afirka sau biyu, bai samu damar lashe Gwarzon […]

Tun lokacin da aka fara gasar Gwarzon dan kwallon Duniya a shekarar 1991, babu dan kwallon Najeriya da ya taba lashe gasar. Ko a shekarar 1996 da kuma 1999 a lokacin da shahararren dan kwallon Najeriya Kanu Nwankwo yake tashe, bayan ya lashe Gasar Gwarzon dan kwallon Afirka sau biyu, bai samu damar lashe Gwarzon dan kwallon Duniya ba hasalima ko a wancan lokaci ba ya cikin jerin ’yan kwallo 10 da suka fafata a gasar. Sai dai dan kwallo daya ne kacal dan Afirka da ya fito daga Laberiya mai suna George Weah ya taba lashe Gwarzon dan kwallon Duniya a shekarar 1995. Ko me ye daililin da ya sa ’yan kwallon Najeriya ba sa iya lashe gasar? Ga wasu daga cikin dalilan da wakilinmu Ahmed Garba Mohammed ya kalato mana saboda karuwar masu karatunmu kamar haka:
1. Da yawa daga cikin ’yan kwallon Najeriya ba a Turai suke kwallo ba:
daya daga cilin dalilin da ya sa ’yan kwallon Najeriya ba za su iya lashe Gasar Gwarzon dan kwallon Duniya ba shi ne yadda suke wasa a wasu kananan kungiyoyin kwallon kafa da ba kasafai suka yi fice a duniya ba. Da yawansu sun fi yin kwallo ne a kasashen Larabawa da na Asiya da Afirka da sauransu. Wadanda ke yin kwallo a kasashen Turai ma ba kasafai suke yi wa kungiyoyinsu wasa a kan kari ba. An fi karrama ’yan kwallon da ke kwallo a manyan kasashen Turai irin su Ingila da Faransa da Italiya da Jamus da Sifen da Hollan da Beljiyum da sauransu. Haka kuma duk da yake akwai wadanda suke kwallo a Nahiyar Turai amma mafi yawansu suna cin benchi ne ba kasafai ake sa su a wasa ba.
Ko shahararren dan kwallon Laberiya, George Weah ya lashe Gwarzon dan kwallon Duniya ne a shekarar 1995 a lokacin da yake buga wa kulob din AC Milan na Italiya kwallo. Har yau, ba a taba samun wani dan kwallo da ya lashe gasar daga Afirka ba, bayan shi. dan kwallon bai taba lashe gasar cin kofin Afirka ba, kuma bai taba yin wasa a gasar cin kofin duniya ba. Amma yadda dan kwallon ya haskaka a kulob din AC Milan ta ba shi damar doke ’yan kwallo irin su Paolo Maldini shi na na AC Milan a Gasar Gwarzon dan kwallon Duniya a shekarar 1995. Saboda haka da su ma ’yan kwallon Najeriya za su rika haskakawa a manyan kulob-kulob a Nahiyar Turai da watakila sun samun sukunin lashe kayutar. Idan za a tuna, dan kwallon Najeriya Austin Jay-Jay Okocha ya yi matukar yin kokari a kulob din Bolton na Ingila a shekarar 2004 al’amarin da ya sa aka zabe shi a Gwarzon dan kwallon Afirka na BCC amma ganin yadda dan kwallon ya yi wasa ne a kulob din da ya cikin sahun farko a Ingila ta sa Okocha bai kai labari a gasar gwarzon dan kwallon duniya a shekarar ba.
2. ’Yan Najeriya ba su cika haskakawa a kulob din da suke yi wa kwallo ba
Wani dalilin da ya sa da wahala a samun dan kwallon Najeriya da zai iya lashe gasar Gwarzon dan kwallon Duniya shi ne ba su cika haskakawa a kulob din da suke yi wa kwallo ba. Hasalima ko suna wasa a manyan kulob a Nahiyar Turai za ka tarar da yawansu suna cin benchi ne, ba kasafai ake sanya su a wasa ba. dan kwallon Najeriya daya da ya shafe kusan shekara 6 yana yi wa babban kulob a Ingila kwallo shi ne John Mikel Obi. Shi ma al’amarinsa sai a hankali a mafi yawan lokuta yana cin benchi ne, ba kasafai yake yi wa kulob din kwallo ba. Mikel Obi ya taba zama na biyu a jerin ’yan kwallo matasa da suka fafata a gasar cin kofin duniya ta matasa, baya ga shaharareen dan kwallon duniya Lionel Messi dan Ajantina. Abin mamaki sai ga shi Lionel Messi ya lashe gasar har sau hudu a jere amma John Mikel Obi ko kusa bai kama kafar Messi a yunkurin lashe gasar.
Kodayake John Mikel Obi ya lashe kofuna irin su Champions League da na Europa da na firimiya da kofin kalubale (FA) da sauransu amma hakan bai ba shi damar zama Gwarzon dan kwallon Duniya ne, don a mafi yawan lokuta yana zama a benchi ne, ko kuma a fara wasa da shi amma daga baya a canza shi.
3. ’Yan kwallon Najeriya ba kasafai suke yin tsada a kakar saye da sayar da ’yan kwallo ba
Dalili na uku shi ne yadda ’yan kwallon Najeriya ba su da tsada a kakar saye da sayar da ’yan kwallo. Alal misali a tsakanin shekaru 5 zuwa 6 da suka gabata ba a taba samun dan kwallon da ya yi tsada irin Brown Ideye ba bayan da kulob din West Bromwich ya saye shi a bara a kan Fam miliyan 10 (kudin da kulob din bai taba kashewa a wajen cefane ba sai a kan Ideye). Abin bakin ciki duk da wadannan makudan kudi da aka kashe a kan dan kwallon sai ga shi ya nuna alamar barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana ganin yadda yake cin benchi. Hakan ta sa masu nazarin harkar kwallo suka ce kwalliya dai ba ta biya kudin sabulu ba. Kenan, babu dan kwallon Najeriya da aka taba saya da tsada kamar Ideye a shekaru shida da suka wuce, wannan ya nuna ’yan kwallon Najeriya ba sa haskawa da hakan ta sa da wuya su iya lashe Gwarzon dan kwallon Duniya.
4. Gasar rukunin firimiya na Najeriya ba ta da armashi
Dalili na hudu kuma shi ne yadda Gasar rukuni-rukuni na Najeriya bai da armashi. Hasalima mafi yawan ’yan kwallon Najeriya suna yin wasa a gida ne saboda babu yadda za su yi. Da zarar sun samu sukuni sai su fice daga kasar ko ma Nahiyar Afirka gaba daya. dan kwallon Masar Mohammed Aboutrika ya so lashe Gasar Gwarzon dan kwallon Afirka a shekarar 2008 a lokacin da yake buga wa kulob din Al-Ahly kwallo amma da wuya ka fi dan kwallon Najeriya ya kusa lashe gasar Gwarzon dan kwallon Afirka ko na Duniya saboda yana buga kwallo a gasar rukuni-rukuni na Najeriya. Kwanan nan aka fara gasar rukunin firimiya na Najeriya amma kafin a je ko’ina har an fara samun matsaloli saboda rashin tsari mai kyau. ’Yan kwallon Najeriya kadan ne suka samun damar zuwa Nahiyar Turai don buga kwallo daga gasar rukunin firimiya na Najeriya tun bayan ’yan wasa irin su marigayi Rashidi Yekini da Kanu Kwankwo da Austin Okocha da Stephen Keshi da Obafemi Martins da sauransu.
Idan za a tuna a ranar 12 ga watan Janiarun wannan shekara ce aka zabi Cristiano Ronaldo a matsayin Gwarzon dan kwallon Duniya. Wannan shi ne karo na uku da dan kwallon yake lashe kyautar. Kyaftin din kungiyoyin kwallon kafa da masu horarwa ne da kuma wasu daga cikin ’yan jaridu suke gudanar da zaben a duk shekara. Sai dai abin da muke hankoro shi ne a samu dan kwallon Najeriya da zai lashe gasar a nan gaba don ganin ya kafa tarihi kamar yadda George Weah na Laberiya ya taba lashewa a shekarar 2005.