Dalilan da suke sanya kaji yin kanana kwai – Dokta Bala
Wani masanin harkokin kiwon kaji da ke zaune a Birnin Tarayya, Abuja, Dokta Bala Mohammed ya bayyana dalilai 4 da suke sanya kaji yin kananan kwai da hana su yin kwan da yawa. Dokta Bala Mohammed ya bayyana wadannan dalilai ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce dalili na farko shi […]
Wani masanin harkokin kiwon kaji da ke zaune a Birnin Tarayya, Abuja, Dokta Bala Mohammed ya bayyana dalilai 4 da suke sanya kaji yin kananan kwai da hana su yin kwan da yawa.
Dokta Bala Mohammed ya bayyana wadannan dalilai ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce dalili na farko shi ne girman ’ya’yan kajin da mai kiwon kaji zai yi kiwo a gonarsa.
“Idan mai kiwon kaji ya sanya ’ya’yan kajin da suke fara yin kwai daga mako 18 zuwa 23. Ba zai a taba samun manyan kwai daga irin wadannan kaji ba,” inji shi.
Ya ce, dalili na gaba shi ne maganar ingancin da abincin da mai kiwon kaji yake bai wa kajinsa. Ya ce, idan mai kiwon kaji yana bai wa kajinsa abinci mara inganci, babu shakka kajin za su rika yin kananan kwai kuma yawan kwan da suke yi zai ragu.
Ya ce, don haka a kullum suke shawartar masu kiwon kaji kan irin abincin da ya kamata su rika bai wa kajinsu. Ya ce, akwai abinci mai inganci da ya kamata masu kiwon kaji su rika bai wa kajinsu, wadanda za su sanya kajin su rika manyan kwan da ba za su kawo musu matsala ba. Sai dai su rika yin manyan kwai.
Dokta Bala ya ce dalili na 3 shi ne irin cututtukan da suke damun kaji. Ya ce, akwai cututtuka da dama da suke damun kaji, kamar yadda masana suka yi bayani. Ya ce, akwai cututtuka da dama da idan kaji suka kamu da su, za su iya sanya su rika yin kananan kwai tare da rage yawan kwan da suke yi.
Kuma ya ce dalili na 4 shi ne maganar yanayin yankin da mai kiwon kaji yake, yana sanya kaji yin kananan kwai da kuma kasa yin kwan da yawa.
“Idan yanayin wuri mai zafi ne, kamar yankin Arewacin Najeriya, yana hana kaji cin abinci sosai, wanda yin haka zai iya sanya kajin yin kananan kwai da kasa yin kwan da yawa. Domin yanayin zafi yana hana kaji cin isasshen abinci. Wanda hakan zai iya hana kajin yin kwai da yawa,” inji shi.
Ya ce, don haka a kowanne lokaci muke bai wa masu kiwon kaji shawara kan idan yanayin zafi ya zo su rika bai wa kajinsu abinci da daddare ba sai da rana kadai ba. Domin idan dare ya yi, yanayi yakan yi sanyi, don haka kajin za su iya samun damar da za su ci isasshen abincin da zai sanya su ba da manya kwai tare da yin kwan da yawa.