Dalilan da ya sa Gwamnonin APC suka ziyarce ni — Jagoran ADC
Inuwa ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya tura gwamnonin Kaduna da Katsina da Zamfara
Jigo a Jam’iyyar ADC a Jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa ya ce ziyarar da gwamnonin Kaduna da Katsina da Zamfara suka kai gidansa ba ta da alaƙa da siyasa.
A wata tattaunawa da JBC Hausa, Inuwa ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya tura Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, da Gwamna Dikko Umaru Radda na Jihar Katsina da Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara domin neman auren ɗaya daga cikin ’ya’yansa ga wani ɗan uwansa.
- Iyayen Mary Habila sun ce a ba su gawarta don binne ta
- INEC na nazarin gwajin zaɓen shugaban ƙasa kafin 2027
Ya ce, iyalansa sun amince da buƙatar, kuma a ranar ne aka ɗaura auren ma’auratan.
Sai dai ziyarar ta jawo ce-ce-ku-ce a siyasa, musamman ganin cewa Inuwa na daga cikin fitattun jagororin ADC a Katsina, jam’iyyar da ke fama da rikicin cikin gida kan batun zaɓen ’yan takara ta hanyar maslaha.
Kodayake wasu masu nazarin siyasa na ganin ziyarar na iya ɗauke da wata ma’ana ta siyasa, Inuwa ya nanata cewa batun neman aure ne kawai ya haɗa su, ba siyasa ba.