Dalilan da ’yan fim din Kano suka fi na Kaduna – Sabi’u Gidaje
Sabi’u Muhammad Gidaje yana daya daga cikin jarumai da ake damawa da su a masana’antar fina-finan Hausa, jarumin wanda furodusa ne ya yi wa wakilinmu bayanin yadda ya fara harkar fim, kalubalen da ya fuskanta da nasarorin da ya cimma da kuma burinsa a sana’ar. Ga yadda hirar ta kasance: Tarihina a takaiceAssalamu alaikum, sunana […]
Sabi’u Muhammad Gidaje yana daya daga cikin jarumai da ake damawa da su a masana’antar fina-finan Hausa, jarumin wanda furodusa ne ya yi wa wakilinmu bayanin yadda ya fara harkar fim, kalubalen da ya fuskanta da nasarorin da ya cimma da kuma burinsa a sana’ar. Ga yadda hirar ta kasance:
Tarihina a takaice
Assalamu alaikum, sunana Sabi’u Muhammad Gidaje. Kuma mun gaji sunan Gidaje ne daga mahaifinmu wato Alhaji Muhammadu Inuwa Gidaje. Hakazalika, kamfanin shirya fina-finanmu shi ma yana amsa wannan sunan ne. An haife ni ne 14 ga watan Yuli, shekarar 1988 a unguwar Tudun Wada da ke garin Kaduna. Na yi makarantar firamare daga nan na wuce sakandare ta Abubakar Gumi College (Makarantar Chanchangi), inda na kammala a shekarar 2010. Na karasa Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Kaduna wato (Kaduna Polytechnic), inda na karanta difloma a fannin aikin Banki da Hada-hadar Kudi, inda na kammala a shekarar 2013.
Farkon abin da ya ja hankalina zuwa sana’ar fim shi ne, akwai wani yayana wato marigayi Alkassim wanda Allah Ya yi wa rasuwa a Kano, a shekarar 2004. Kuma ya gamu da ajalinsa ne sakamakon hadarin mota lokacin yana tsakiyar shirya wani fim mai suna ‘Shahada’. A lokacin shirin wannan fim din ne ya fara shigar da ni sana’ar. Da farko an fara sanya ni ne a fina-finai a matsayin jarumi, daga bisani na fara shiryawa da kaina.
Fina-finan da na fito cikinsu
Akwai fina-finai kamarsu: ‘Ga Fili ga Mai Doki’ da ‘Basaja’ da ‘Gadar Zare’da ‘Matar Uba’ da ‘da da Uwa’ da ‘Attajiri’ da sauransu. daya daga cikin fina-finan da na shirya kuma shi ne ‘Gama’.
Jarumin da na fi jin dadin aiki da shi
A gaskiya ina jin dadin aiki da kowa, ba wani da zan ce idan muna fim yana ba ni kwarjini a ido. Kuma duka wanda na kira aiki yana amsa kirana. Daga manyan jarumai har zuwa kanana. Kai idan ma taimako na nema a wajensu suna taimaka mini, domin haka nake alfahari da duka abokan sana’ata.
Abin da ya sa wasu suke kallon Jihar Kano ta fi Kaduna ci gaba ta fuskar shirya fina-finan Hausa
Wannan batun haka yake, amma ba wai sana’ar ta fi karfi a Kano ba ne. Idan ka duba mu a nan Kaduna, za ka ga kusan galibin ’yan fim suna raba kafa ne. Ko dai suna makaranta, ko kuma suna wata sana’a. A bangaren Kano su suna yin fim din ne ka’in da na’in fiye da yadda muke yi. Misali ni kaina, bayan wannan sana’ar ina zuwa makaranta, ina kuma gudanar da harkokin kasuwanci. Ka ga idan ba makaranta, ina harkokin fim, idan babu harkokin fim, ina kasuwa. Har ila yau, Kanawa sun fi mu jajircewa saboda ko da kuwa za su fadi ne ba sa fasa ci gaba da shirya fina-finai nan da can, amma mu a Kaduna idan ka duba da kyau za ka ga wasu suna shirya fim ne daga bana sai badi. Kuma ba wai rashin kudi ne ke jawo hakan ba, a’a, sai dai ana iya cewa rashin sukuni ne ke haddasa hakan. Saboda kamar yadda na bayyana tun farko wasu ba wai sana’ar fim ce kadai sana’ar da suke yi ba, amma akwai wasu sana’o’in da suke gudanarwa.
Kuma yana da matukar muhimmanci mu fahimci cewa, yanzu Kanawan da kansu suna barin Kano zuwa Kaduna domin daukar fina-finansu. Misali idan aka yi fim guda goma a Kano, za ka samu akalla guda 20 a Kaduna suka zo suka yi. Akwai lokacin da na taba tambayar wani jarumi dalilin da ya sa suke zuwa Kaduna daukar fim. Sai jarumin ya ce dalilan suna da yawa, amma daya daga shi ne sun fi samun sakewa a nan.
kalubale
A gaskiya ban fuskanci kalubale wajen samun karbuwa wurin mutane ba. Kodayake, na sha wahala sosai, amma ba ta neman karbuwa ba. Har ila yau, ina kallon hakan ne a matsayin darasi tun da yanzu an fara girbar ribar. Hakazalika, ta bangaren shirya fina-finai akwai wani babban kalubalen da muke fuskanta wajen sayar da fina-finanmu a kasuwa saboda wasu Marketers (’yan kasuwa) ba sa kyautawa kuma ba sa taimakon masu shirya fim da kuma sana’ar baki daya. Ya kamata mu ji tsoron Allah saboda mu gudu tare, mu tsira tare.
Nasarori
Da farko zan fara godiya ne ga masu ba mu goyon baya. Gaskiya jama’a na nuna mana kauna kuma muna jin dadin hakan. Ka ga ko a makaranta akwai wuraren da ba za a bar dalibi ya shiga ba, sai ya nuna katin shaida wato (ID card), amma ni fuskata ita ID card dina. Hakazalika, na samu dimbin kyaututtukan girmamawa. Har ila yau, a kamfaninmu na Gidaje Film Production muna bai wa matasa horo kan rera waka wato (Lyrics) da rubuta labari wato (Sreenplay) da sauransu.
Burina
Ba ni da wani buri da ya wuce wannan sana’ar ta ci gaba da samun daukaka. Kuma yana da kyau sosai mu dinga hada kawunanmu domin masu magana na cewa tsintsiya madaurinta daya.
Fim din da nake shiryawa yanzu
Tabbas akwai wani fim da nake shiryawa yanzu haka, amma sunansa sirri ne. Labarin fim din ya kunshi siyasa da illar shan miyagun kwayoyi. Kuma na yi nisa da aikinsa, zai isa kasuwa nan ba da jimawa ba.
Iyali
Ban yi aure ba tukuna, amma na daura niyya.