Dalilan yajin aikin malaman jami’o’in Najeriya

A wannan makon, mun samu wannan muhimmiyar mukala daga daya daga cikin iyayen Gizagawan Najeriya, wato Farfesa Yusuf M. Adamu (08034064325), marubuci, manazarci, malami a Sashen Labarin kasa (Geography), Jami’ar Bayero Kano. Ga abin da yake cewa:Koyaushe aka ce malaman jami’a na yajin aiki, mutane kan fadi albarkacin bakinsu. Wasu su goyi bayanmu wasu kuma […]

Dalilan yajin aikin malaman jami’o’in Najeriya

Shugaban Gizagawan Jihar Kano, Abban Saudat, a yayin da yake jawabi a bikin Goron Sallah, a makon jiyaA wannan makon, mun samu wannan muhimmiyar mukala daga daya daga cikin iyayen Gizagawan Najeriya, wato Farfesa Yusuf M. Adamu (08034064325), marubuci, manazarci, malami a Sashen Labarin kasa (Geography), Jami’ar Bayero Kano. Ga abin da yake cewa:
Koyaushe aka ce malaman jami’a na yajin aiki, mutane kan fadi albarkacin bakinsu. Wasu su goyi bayanmu wasu kuma su goyi bayan gwamnati. Wasu kuma su tsaya a tsaka-tsaki, suna ganin laifin kowa. A wannan karo ma haka muka tsincin kanmu.
Da yawa mutane na mamakin me ya sa muka dauki yajin aiki da muhimmancin da har wasu suna ganin cewa da mun nemi abu an hana mu sai mu tafi yajin aiki. Wannan dalili ne ya sa na ga ya dace a matsayina na malamin jami’a, in yi wa jama’ar Najeriya bayani a kan halin da muka tsinci kanmu a wannan karo, ko ma yi wa juna adalci.
Yajin aikin malaman jami’a da ya fara shahara shi ne wanda aka yi lokacin mulkin soja na Janar Babangida, karkashin shugabancin Dokta Attahiru Jega a 1992. Yajin aiki ne da aka yi fiye da wata shida ana yi, har ya jawo aka rufe dukkan jami’o’in Najeriya. A wannan lokacin, bayan tsayar da albashin malamai da aka yi, har ma ta kai an haramta kungiyar Malaman Jami’ar. Daga bisani ma aka kori duk malaman jami’o’in Najeriya. Da malamai suka jajirce, a karshe dai aka daidaita bisa yarjejeniya tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya.
A sakamakon wannan yarjejeniyar ne aka kafa Hukumar Taimakon Ilmi (ETF). Manufarta ita ce tara kudaden da za a gudanar da harkokin jami’o’i da su. Sai dai ba a samu cimma wannan manufa  ba, domin ETF ta zama ta tallafin ilmin firamare da na sakandare da na manyan makarantun gaba da sakandire da kuma jami’o’i. Tara mahaukatan kudi daga harajin masana’antu da ASUU ta ba da shawarar a rika karba domin Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da kudin da za ta biya bukatun jami’o’in. An ci gaba da tara wadannan kudade tun lokacin Babangida har zuwa yau.
A lokacin mulkin Janar Sani Abacha, an kara wani yajin domin gwamnati ta aiwatar ko cika alkawarin da ta yi wa malaman, kamar yadda yake kunshe a cikin yarjejeniyar. Wannan yajin aikin shi ma an yi fiye da watannin shida ana yi, kuma har Abacha ya mutu ba a daidaita ba. Mun yi wani yajin lokacin Obasanjo, mun yi lokacin Umaru Musa ’Yar’aduwa, wanda a 2009 aka zauna aka amince aka kuma sa hannu tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU.
Wasu za su ce wai mu ba mu da wata hanyar sa gwamnati ta yi abu ne sai yajin aiki? Amsar ita ce ‘E.’ Dalili kuwa shi ne, muna da shugabanni ne wadanda ba su san ya kamata ba. Mutane ne wadanda talaka ba ya zuciyarsu, kasar nan ba ta gabansu kuma ba su damu da kowa ba sai abin da zuciyarsu ta raya musu.
Wannan yajin na yanzu da muka tafi, ba sabo ba ne. Mun tafi yajin aiki ne bayan mun bi gwamnati iyaka yinmu. Mun lallaba ta mun kuma yi ta ba da gargadi cewa matukar Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da kin aiwatar da abubuwan da aka amince da su a yarjejeniyar da muka kulla da su a baya to za mu shiga yajin aiki. Gwamnatin Jonathan ta yi kunnen uwar shegu da mu. Mu ba shegu ba ne to.
Ya kamata jama’a su fahimci cewa ASUU da ’ya’yanta ba su kaunar yajin aiki ko kadan, domin su ma yana shafar su. Yana shafar aikinsu da dalibansu, su ma suna da ’ya’ya a jami’o’i. Saboda haka ana shiga yajin aiki ne kawai bayan an yi iyaka kokari, abu ya ci tura.
A watan Oktobar 2009, Gwamnatin Tarayya, bisa wakilcin jami’anta suka kai matsaya da ASUU, aka kuma sa hannu da amincewar ita gwamnatin za ta aiwatar da abubuwan da aka sa hannu a kansu. Manyan abubuwan da aka amince da su sun hada da:
1-Samar da kudaden da ake bukata domin farfado da jami’o’in Najeriya. 2-Taimakon Gwamnatin Tarayya ga jami’o’in jihohi. 3-kara kasafin kudi daki-daki har ta kai Najeriya na ware kashi 26 na kasafin kudinta ga bangaren ilmi daga 2009 zuwa 2020. 4 -Biyan alawus-alawus na malamai bisa ayyukan da suka riga suka yi daga 2009 zuwa 2012. 5-Maida shekarun ritaya na Farfesoshi zuwa shekara 70 maimakon shekara 65. 6-Mika wa jami’o’i kadarorin gwamnati na gine-gine da ke Legas domin samar da kudin tafiyar da jami’o’i kuma a rage wa ita gwamnatin wahala. 7-Kafa sashen bincike a kamfanoni domin inganta su maimakon dogaro da kasashen waje koyaushe da kuma samar da kayan aiki a dakunan bincike da ajujuwa a jami’o’i.
Mun tafi yajin aikin gargadi daga Disamba 8, 2011 zuwa 20 ga Maris 2012 amma abu guda kawai Gwamnatin Tarayya ta aiwatar, watau daga shekarun ritaya zuwa 70. Daga wancan lokacin ASUU ta yi ta fadi-tashi da fafutuka ta hanyar tattaunawa da kwamitin aiwatarwa na Gwamnatin Tarayya, tattaunawa da Kwamitin ilmi na Majalisar Tarayya, rubuta wasiku da bayanai a jaridu, duk don gudun shiga yajin aiki. Duk wannan bai yi amfani wurin shawo kan Gwamnati Tarayya ba.
Daga bisani Gwamnatin Tarayya ta sa kwamiti mai zaman kansa ya zagaya duk jami’o’in kasar nan, domin ganin hakikanin halin da suke ciki, suka kuma kawo mata rahoto. Ina daya daga cikin wadanda suka zagaya wasu jami’o’i a gabanshin kasar nan kuma abubuwan da muka gani sun tayar mana da hankali. Lokacin da aka gabatar wa Majalisar Gudanarwar Gwamnatin Tarayya da rahoton sai kunya ta rufe su, kowa ya fara kallon dan uwansa yana cewa shi bai san lalacewar da ta kai haka ba. Wallahi wasu jami’o’in ko darajar sakandare ba su kai ba ta fuskar kayan aiki. Mun ga makarantar da ake lakca a sitadiyon, mun ga wadda malamai hudu har da Farfesa ke zaune a ofishi guda. Mun ga rijiyoyin da dalibai suka fada saboda neman ruwa. Mun ga dakunan binciken da kayan aikinsu tun na 1960 zuwa 1970 ne, su ake amfani da su. Mun ga… mun ga… abubuwa dai marasa dadi.
Mu ba jahilai ba ne kuma kowane dan Najeriya ya san yadda ake barnar kudin kasa ta hanyoyi marasa amfani.  Mun ga yadda ake biyan ’yan majalisa albashi zabtari-da-kanka (har da masu dumama kujera). Mun ga yadda aka yi da masu satar ragowar kudin mai wanda har yanzu maganar ta sha ruwa. Mun ga yadda aka sace kudin NEPA aka yi shiru da maganar. Mun ga yadda ake rabon kudi ga mutanen da ba sa kara wa kasar nan komai illa wai ana samun mai a yankinsu. Muna ganin yadda gwamnoni ke sayen jiragen sama. Muna ganin barna iri-iri. Duk da wannan sai ministocin Jonathan su shafa wa fuska toka su fito su ce wai Najeriya ba ta da kudin da za ta gyara jami’o’i.
Mun ji su diyansu suna wasu kasashe suna karatu, to amma ai dukiyoyin da suke hannunsu ba nasu ba ne, na kasa ne, na ’yan Najeriya ne. Mu riko muka ba su kuma ba abin kunya ba ne halin da jami’o’i ke ciki a kasar nan. Ba yabon kai ba, malaman da suke koyarwa a jami’o’inmu za su iya koyarwa a kowace kasa a duniya. Amma babu kayan aiki, babu kayan bincike me za ka yi?
Ya kamata mutanen Najeriya su fahimci cewa zaman da muka yi muna aiki a jami’o’i ba wai don mun rasa aikin yi ba ne, illa kishin kasa. Dukanmu za mu iya barin aji mu shiga gwamnati ko mu shiga siyasa a dama da mu. Za mu iya barin kasar mu tafi ci-rani koma mu yi kaura ta dindindin. To amma, in mun yi haka mun yi wa kasarmu adalci? Mu da kudin kasa aka ilmantar da mu don haka muka ga ya zamar mana wajibi mu zauna mu taimaki kasarmu ta haihuwa.
Lokaci ya yi da ’yan Nijeriya za su fahimci cewa yajin aikin nan da muke yi muna yin shi domin a gyara, domin shi kadai ne yaren da gwamnatocinmu ke ji. Muna neman goyon bayan al’umma da kuma addu’arsu. Allah Ya taimake mu a gyara jami’oi’nmu, domin kasarmu ta ci gaba; amin.

Hidindimin Gizagawan Zumunci

Bagizage Yusuf Abubakar Dingyadi (08035877331) na gayyatar daukacin Gizagawan Zumunci, domin halartar bikin nadin sarautarsa ta ‘Magayakin Garkuwan Sakkwato,’ wanda za a gudanar a fadar Garkuwa, Alhaji Attahiru Bafarawa, Sakkwato a gobe Asabar, da misalin karfe biyu na rana.
Muna rokon Allah Ya albarkaci wannan mukami kuma Ya sa mai amfani ne ga al’umma gaba daya, amin. – Gizago.
***
Bagizage Saifullahi Mika’ilu Mato (08162949976) na gayyatar daukacin Gizagawan Zumunci zuwa daurin aurensa da A’isha Yusuf, wanda za a gabatar a gobe Asabar, da karfe 11:30 na safe, a Babban Masallacin kankara, Jihar Katsina.
Muna rokon Allah Ya sa albarka ga auren, Ya sanya a yi taro lafiya, amin. – Gizago.
***
Za mu ci gaba da rijistar sababbin Gizagawa a makon gobe, insha Allah.