Dalilanmu na komawa PDP – Shekarau da Bafarawa
Tsohon Gamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da takwaransa na Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa sun bayyana cewa rashin adalci ne daga jam’iyyarsu ta APC ya sa suka koma PDP.Shekarau wanda ya koma PDP a shekaranjiya Laraba, ya bi sahun Bafarawa ne wanda ya koma PDP a farkon wannan mako, wanda kuma aka ce sun […]

Tsohon Gamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da takwaransa na Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa sun bayyana cewa rashin adalci ne daga jam’iyyarsu ta APC ya sa suka koma PDP.
Shekarau wanda ya koma PDP a shekaranjiya Laraba, ya bi sahun Bafarawa ne wanda ya koma PDP a farkon wannan mako, wanda kuma aka ce sun gana kafin Bafarawa ya bayyana ficewarsa daga APC.
Malam Shekarau ya bayyana komawarsa PDP ne a lokacin taron masu ruwa da
tsaki na tsohuwar Jam’iyyar ANPP da aka gudanar a gidansa da ke Mundubawa
a birnin Kano.
Malam Shekarau ya ce akwai rashin adalci a tsarin shugabancin Jam’iyyar APC, kasancewar sun rubuta takarda zuwa ga sakatariyarta ta kasa kan halin da take ciki a Jihar Kano, amma ba su samu wata gamsasshiyar amsa ba bayan mako shida. “Bisa shawarwarin magoya baya game da rashin adalcin da aka yi mana a Jam’iyyar APC nake kira ga magoya bayanmu da masu yi mana fatan alheri su daina
alakanta kansu da Jam’iyyar APC ta kowace siga, ina kuma kira da su zo su mara wa Jam’iyyar PDP baya,” inji Shekarau.
Shik kuwa Alhaji Attahiru Bafarawa ya fice daga APC zuwa PDP ne a ranar Asabar da ta gabata, inda ya ce “Wannan jam’iyya ta APC an kafa ta ce don a samar da adalci da tsamo kasar nan daga rugujewa, amma bayan an fara tafiya sai aka fara canja asasin jam’iyyar, son mulki ya rufe idanun shugabannin jam’iyyar suka fara yi mana rashin adalci, rashin adalci ne ya sa na bar jam’iyyar zuwa PDP.”
Ya ce ya bar APC ba don ra’ayinsa ba ne, magoya bayansa ne suka tursasa shi saboda siyasa ta mutane ce kuma ya koma PDP ne ba don wata bukata ko neman mukami ba.
Sai dai a yayin da tsofaffin gwamnonin biyu suka koma PDP, a can Majalisar Dattawa PDP ta rasa sanatoci 11wadanda suka koma APC a shekaranjiya Laraba. Sanatocin da suka koma APC din sun hada da Alhaji Bukola Saraki daga Jihar Kwara da Alhaji Muhammad danjuma Goje daga Gombe da Mohammed Ndume daga Jihar Borno da kuma Dokta Abdullahi Adamu dga Jihar Nasarawa, kuma ana sa ran wasu sanatocin za su bi bayansu a cikin makonni masu zuwa.