Dalilin ba ’yan acaba wurin kwana a cikin makabarta – Limamin Kubwa
Babban Limamin Kubwa da ke Abuja, Malam Abdurrahim Yahaya Muhammad ya ce wurin kwana da suka bai wa wadansu masu sana’ar acaba a cikin makabartar garin ya taimaka wajen samar da tsaro da kuma magance shiga ana aikata tsafi a kan kabari. Aminiya ta zanta da malamin ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan […]
Babban Limamin Kubwa da ke Abuja, Malam Abdurrahim Yahaya Muhammad ya ce wurin kwana da suka bai wa wadansu masu sana’ar acaba a cikin makabartar garin ya taimaka wajen samar da tsaro da kuma magance shiga ana aikata tsafi a kan kabari.
Aminiya ta zanta da malamin ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan aikin gayya da ya hada da yankar ciyawa da cike kaburbura da aka gudanar a makabartar.
Ya ce ko kamar wata biyu da suka gabata an samu wani Musulmi da sunan malanta da ya je makabartar da wadansu mutum biyu da ba Musulmi ba, inda ya aike su zuwa cikin makabartar suka tone wani kabari suka binne layu. Ya ce wani manomi da ke da gona a kusa da makabartar ya an karar da shi ta waya kuma bayan zuwansa wajen ’yan acaba da dakinsu ke hade da wurin wankar gawa, suka kama mutanen tare da wanda ya sa su aikin wanda yake jiransu a waje.
“ Bayan ’yan acaba sun kama su, muka dauke su a mota tare da mika su ga ’yan sanda. Zamansu a wajen nan ya taimaka har ga wannan unguwa kuma kamar yadda ka gani su ne mafi yawan wadanda suka taimaka wajen wannan aikin gyara a yau bayan mun nemi daukinsu, kasancewar a baya an sha yekuwar gayya amma wadanda ke zuwa aikin yawansu bai gamsarwa,” inji shi.
Malam Abdurrahim Muhammad ya bukaci al’ummar Musulmi a duk inda suke su rika taimakawa wajen aikin gyaran makabarta sannan ya yi kira ga masu hali a cikinsu su rika ziyartar makabarta don gane wa idanunsu irin abubuwan da ake bukata don inganta makabarta da kayan aiki kamar itace da kuma jawo ruwa.
Mai gadin makabartar Malam Ibrahim Salihu ya ce sakamakon yadda wadansu miyagu ke aikata ba daidai ba a cikin makabarta, duk lokacin da aka samu wadansu da suka bukaci yin ziyara a makabartar, ba a barinsu haka, sai an yi musu rakiya don sa ido a kansu. Ya yi msali da wani abu da ya faru a baya inda ya ce wani ya zo wajen da rago a motarsa kan zai yanka ragon ya ba su sadakarsa, bayan ya dauki kai da yake son ya binne a kabarin dan unsa da ke wajen.
“Ya yi kokarin ya hada mana da kudi don cimma burinsa, da bai samu amincewarmu sai ya tafi da ragonsa,” inji mai gadin.