‘Dalilin bullo da Gasar Rubuta Gajerun Labarai ta Aminiya’
A bana Kamfanin Media Trust Limited da ke Abuja da hadin gwiwar Gandun Kalmomi suka fito da sabuwar gasar rubutun gajerun kirkirarrun labaran Hausa, na Aminiya-Trust inda aka bukaci matasa maza da mata su fafata da juna. Shin ko mene ne babban burin wannan gasa? Aminiya ta tattauna da Shugaban Kwamitin Gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi […]
A bana Kamfanin Media Trust Limited da ke Abuja da hadin gwiwar Gandun Kalmomi suka fito da sabuwar gasar rubutun gajerun kirkirarrun labaran Hausa, na Aminiya-Trust inda aka bukaci matasa maza da mata su fafata da juna.
Shin ko mene ne babban burin wannan gasa?
Aminiya ta tattauna da Shugaban Kwamitin Gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi na Jami’ar Jihar Kaduna, wanda ya yi bayani dalla-dalla:
Kamar yadda muka kaddamar da wannan gasa a ranar 15 ga Mayun 2020, mun yi bayanin cewa gasar wata dama ce da Hukumar Gudanarwar Kamfanin Media Trust mai buga jaridar Aminiya suka ba matasan Hausawa domin su baje kolin fasaharsu ta tsarawa da ayyana gajerun labarai da ake son su burge domin samun awalajar wasu kudi da aka tanada.
- An bude Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Aminiya-Trust
- Manya dibar fari: Tarihin Rupert East, tsanin Adabin Hausa (1)
Gasa ce da ake bukatar matasa su nuna hazaka wajen ayyana labarai masu jan hankali da tattauna matsalolin da ke addabar al’ummar Hausawa.
Saboda haka daga wannan shekara za a rika gabatar da irin wannan gasa bisa wasu maudu’ai na musamman.
Kamar yadda aka tsara za a rika gudanar da wannan gasa ko wace shekara, za a kuma kashe kusan Naira miliyan 3 duk shekara domin tabbatar da gasar ta zauna da gindinta.
Ta wadanne hanyoyi gasar ta sha bamban da sauran da aka taba yi ko ake yi a yanzu?
To wannan gasa ta dan bambanta da wadanda aka yi a baya ta fuskoki da dama.
Idan muka dubi irin wannan gasa da aka gudanar a shekarun 1927 da 1929 da 1933 da kuma 1978 da ta 1980 da 1988 da hukumomin ’yan mulkin mallaka da Gwamnatin Tarayya da jihohi suka gabatar da kuma wadanda aka gabatar daga 2005 na Bashir Karaye, za a ga suna yin cikakkun littattafai ne, wato masu kalmomi 20,000 zuwa 60,000 ba gajerun labarai ba.
Amma ita wannan gasa ta gajerun labarai ce, wato masu dauke da kalmomi 1,000 zuwa 1,500.
Shi rubuta cikakken littafi ba shi da wahala sosai in aka kwatanta shi da gajeren labari da ake bukatar a hade dukkan fasaha da basira a waje daya don kawo labari mai kyau da tsari da burgewa.
Idan kuma aka dubi gasar gajerun labarai da ake gudanarwa yanzu, za a ga cewa wannan ta Aminiya ta sha bamban da su ta fuskar la’akari, wanzuwa da tabbatuwa, wato ina nufin in aka auna da gasar Pleasant Library da aka soma, amma ta kwanta dama shekara daya da fara ta.
Idan kuma muka dubi ta Hikayata da BBC ke gudanarwa da aka yi kusan shekara 5 da farawa, kuma tana ci gaba da wanzuwa, ita ta takaita ne ga mata kurum, kuma ba a la’akari da yawan shekaru, ko wace mace na iya shiga in dai ta kai shekara 18.
To ita Hukumar Gudanarwar Kamfanin Media Trust sai ta fito da tata gasar ta daban, wadda za ta ba matasa, maza da mata, dama su baje kolin basirarsu; ka ga ke nan, maza da mata kowa zai samu wannan dama.
Na ji kana cewa gasar ta matasa ce kawai, wato daga shekara 18 zuwa 35, me ya sa aka tsai da ita tsakanin wannan rukunin jama’a?
Wato bayan nazari da aka yi, an fahimci cewa al’adar raya rubutu tana tafiya ne da zamani, saboda haka gasar rubutun ita ma ya dace ta bi zamani.
Abin da nake nufi a nan shi ne, gasar da aka bari sukuku, makaka, ba a cika samun alfanunta ba.
Ka shirya gasa ta mata kurum, ka debe wani kaso na al’umma, wato maza, shi ma yana iya kawo cece-ku-ce, idan kuma ka bar shi bude, kowa na iya shiga da wuya a samu adalci tsakanin dan shekara 18 da dan shekara 60 ko 70.
Amma idan ka bar gasar tsakanin matasa, wato ’yan shekara 18 zuwa 35, maza da mata, ka ba da dama ne ga wadanda za su ja ragamar rubutu irin wannan nan gaba.
Dan shekara 20 ko 30 idan ya ci gasar zai iya samun horo da gwanancewa wadda za ta sa su zama marubutan gobe, ba kamar dan shekara 50 ko 60 ba da yana shirin barin fage.
Saboda haka Hukumar Gudanarwar Media Trust tana neman zakulo sababbin marubuta ne da za su kasance irin su Abubukar Imam ko Sulaiman Ibrahim Katsina nan gaba ko kuma irin su Balaraba Ramat da Hafsat Abdulwaheed din wannan zamani.
Wato in muka ce da sabuwar zuma yanzu ake son yin magani, abin ya fi fitowa fili.
Ta yaya kake ganin wannan gasa za ta taimaki al’umma?
Ta hanyoyi da dama. Hanya ta farko dai ana fatar za ta samar da sababbin marubuta cikin Hausa, matasa da za su dade suna bauta wa adabin Hausa.
Ta biyu kuwa saboda tsarin da aka tanada na tattauna matsalolin al’umma ko wace shekara, ana fatar marubutan su fito da matsalolin al’ummar fili, su kuma kawo mafita ko yaya, wanda ta haka ana iya samun hanyoyin da za bi a kawo karshen wasu daga cikin matsalolin al’ummar.
Wata hanyar kuma da gasar za ta taimaka wa al’ummar Hausawa ita ce in an buga labaran da fassara wadanda suka zo na daya zuwa na uku cikin Ingilishi, aka rarraba duniya ta san da su, shi ma abin godo ne ga Hausawa.
Ana fama da karancin ingantattun littattafan kirkirarrun labaran Hausa da suka dace da zamani, ko kana jin wannan gasa za ta taka rawa wajen inganta al’amarin?
Kwarai kuwa! Wannan shi ne babban makasudin assasa gasar, domin Adabin Hausa shi ma ya shiga sahun ’yan uwansa na zamani, ta yadda zai yi kafada-kafada da sauran irinsa.
Idan kuma aka samu zakakuran marubuta da suka kunno kai, aka kuma fassara rubutun nasu zuwa Ingilishi, za su kara fiddo da Adabin Hausa fili, bare kuma uwa-uba da yake akwai maudu’i na musamman, wato tattauna matsalolin dimokuradiyya da dambarwar siyasa, abu ne da zai zamanantar da rubutun, a kauce dawwama a kan soyayya da aure a ko yaushe.
Gasar ta bana ta takaita ga zube ne kurum, shin ko nan gaba za a mai da hankali zuwa ga wasan kwaikwayo ko waka?
Haka ne, ba za a iya cewa a’a ba, idan mun samu wata hukuma ta gwamnati ko mai zaman kanta da za ta agaza ta dauki nauyi, za mu so haka.
Za mu so mu ga ana gudanar da gasa ta zube daban, ta wasan kwaikwayo daban, ta rubutacciyar waka daban.
Muna nan muna lalubawa mu ga ko za a samu masu wannan niyya da kudiri.
Me za ka ce da Hukumar Gudanarwar Kamfanin Trust da ta samar da wannan dama?
Ba mu da abin da za mu ce face godiya mai tarin yawa a madadin Adabin Hausa, domin ba karamar gudunmawa wannan gasa za ta bayar ba wajen raya Adabin Hausa.
Hobbasar da Shugaban Kamfanin Media Trust, Malam Mannir Dan’ali ya yi don ganin gasar ta tabbata abin yabawa ne.
Mun gode kwarai.