Dalilin cire Sadiq Umar daga tawagar Super Eagles a Gasar AFCON

Tuni dai kocin tawagar ta Super Eagles José Peseiro ya maye gurbin Umar Sadiq da Paul Onuachu.

Dalilin cire Sadiq Umar daga tawagar Super Eagles a Gasar AFCON

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta ƙaryata raɗe-raɗin cewa da gangan aka cire ɗan wasan Super Eagles Sadiq Umar daga cikin tawagar da ke wakiltar kasar a Gasar AFCON.

Wannan dai na kunshe ne cikin sanarwar da NFF ta fitar a ranar Talata a shafin X.

A cewarta, “Tawagar ƙwallon ƙafa ta Super Eagels ta koka kan rahotannin da wasu kafafen watsa labarai ke watsawa na ci gaba da zuzuta batun rashin lafiyar dan wasan mai taka leda a Sifaniya Sadiq Umar ta hanyar kitsa labaran ƙarya da zato mara kyau.”

Sanarwar NFF na zuwa ne a daidai lokacin da aka ga sunan ɗan wasan a cikin waɗanda za su buga wa kulob dinsa na Real Sociedad wasa a ranar Laraba.

Hakan ne ya sa mutane a Nijeriya suka fara bayyana ra’ayi, inda suke zargin cewa da gangan aka cire sunansa a jerin masu buga wa ƙasar wasanni a Gasar AFCON.

NFF dai ta ce tun a lokacin da ta cire sunan Sadiq ta fitar da sanarwa kan yadda aka fitar da shi daga masu wakiltar Najeriya a gasar da ake fafatawa a kasar Cote d’Ivoire.

“Sai dai mun yi mamaki kan labarin da yake tashe a shafukan sada zumunta kan batun Sadiq Umar da yadda aka cire shi daga tawagar.”

A sanarwar ta ranar Talata, NFF ta ce “gaskiyar magana ita ce ma’aikatan jinyarmu sun bi tsarin jinya da ya dace, kuma sun yi aiki tukuru wajen yanke shawarar bai wa koci José Peseiro dama a cire dan wasan daga tawagar.”

Hukumar NFF ta ce dan wasan ya ji ciwo a wasan Nijeriya da Guinea da aka yi a Abu Dhabi ranar 8 ga watan Janairu gabannin gasar cin kofin Afirka.

Sanarwar NFF ta ce “an yi kokarin a cire shi a wasan, sai dai dan wasan ya ce zai iya ci-gaba da wasan.

“Washe garin da aka yi wasan, sai kumburin kafarsa ya karu,” in ji hukumar NFF.

“A lokacin da tawagar ta yi tafiya daga Legas zuwa Abidjan, sai kumburin kafarsa ya karu, lamarin da ya sa aka yanke shewarar cire shi a cikin wadanda za su buga gasar,” in NFF.

Tuni dai kocin tawagar ta Super Eagles José Peseiro ya maye gurbin Umar Sadiq da Paul Onuachu.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda