Dalilin da aka daina ganin Kanabaro a fim din A Duniya
An samo wannan suna ne daga wani kasurgumin mai laifi a wani yanki da ba na wayayyun mutane ba.
Shirin fim A Duniya shiri ne da ya shahara matuka, musamman a tsakanin matasa, wanda bai rasa nasaba da tsarin labarin fim din.
A fim din mai dogon zango, an bayyana abubuwa da dama da suka shafi matasa kai-tsaye na harkar daba da harkallar miyagun kwayoyi da fyade da sauransu.
- Abin da ’yan Najeriya ke cewa kan janye sunan Maryam Shetty daga jerin ministoci
- DPO ya biya wa saurayi sadakin aure
Tijjani Abdullahi Asase, wanda fitaccen jarumin finafinan Hausa ne, shi ne furodusan shirin na A Duniya sannan ya taka rawar Kanabaro a ciki.
Kusan za a iya cewa da shi fim din ya yi suna, inda kusan shi aka fi gani a matsayin fuskar fim din.
A cikin wata tattaunawa da ya yi da Aminiya, Asase ya ce ya zabi sunan Kanabaro ne saboda, “A cikin al’ummar Najeriya ko in ce Arewacin Najeriya suna fada wa mutum Kanabaro (Canavaro) ne idan mutum ya zama mai kwakwalwa wato mai fasaha ko wata hikima.
Shi kansa Canavaro dan kwallon kafar Italiya idan ka kula ana cewa Canavaro ka ci, ka hana ci. Wato ya ci kwallo kuma ya dawo ya hana a ci.”
A shirin na A Duniya kuwa, “An samo wannan suna ne daga wani kasurgumin mai laifi a wani yanki da ba na wayayyun mutane ba, kuma wanda yake da kwakwalwa tun daga tasowarsa wannan kwakwalwar da yake da ita idan ya lissafa sai ka ga yana ganin kamar abu ba zai iya yiwuwa ba, amma sai a ga ya yiwu.”
Da yake magana a kan tsarin labarin, sai ya ce, “Fim din A Duniya yana nuna zurfin son zuciya na al’umma ne, mutane ba za su bari a samu zaman lafiya ba, kuma idan kana kallon fim din an kirkire shi ne a kan son zuciya irin na dan Adam.”
Sai dai kwatsam, ana cikin fim din sai aka yi wayi gari an daina ganin Kanabaro a fim din, wanda mutane da dama da suke bibiyarsa suke tunanin nasa ne.
Mutane da dama sun dauka ko labarin ne na dan kawar da shi, kafin daga bisani aka fara ce-ce-ku-cen cewa akwai lauje a cikin nadi.
Sanusi Dan Yaro, wanda shi ne wanda yake daukar nauyin fim din ya bayyana a wata hira da ya yi da gidan rediyon Freedom da ke Kano cewa sun samu sabani mai karfi da Asase, wanda har sabanin ya kai ga bata alakarsu ta sama da shekara 20.
“Shirin A Duniya na ci gaba. Kawai da shi, da babu shi abin da na sa a raina shi ne ya yi amfani da damar cewa kai ba za a iya yi ba.
“Don haka idan babu wanda zai kalla sai ni kadai, zan yi in kalla a wayata saboda in tabbatar maka cewa ko da kai ko ba kai zan iya yi,” in ji shi.
Sanusi Dan Yaro ya ce akwai aminci a tsakaninsu, wanda hakan ya sa bayan da ya ga Kashi na 1 na karbo kasancewar ya yi ta fadi-tashi bai samu nasara ba, sai kawai ya rika zuba kudi ba tare da lissafi ko rubutu ba.
Matsalar ta fara ce a cewarsa a lokacin da ya bukaci a fara lissafi tare da rubuta kudaden da ake kashewa.
“Wata rana na zauna, kasancewar ina cikin daraktocin shirin Gidan Badamasi. Sai na ga kasafin kudinmu na kusa da nasu.
“Sai na kira shi (Asase) muka zauna na nuna masa cewa Gidan Badamasi suna awa daidaya ne kuma fitowa 13 a duk zango, ni kuma ina yin minti 30 kuma fitowa 10 a duk zango, kuma su ba su da kayan aiki, haya suke yi, ni kuma ina da kayan aiki.
“Kuma sun fi mu biyan kudin jarumai, bai kamata a ce kudinmu ya kusa da nasu ba. Sai na ce masa ba so nake a koma baya ba, amma daga lokacin ina so a duk zango a rubuto abin da ake bukatar za a kashe, in bayar.
“Ya ce tun daga lokacin da za su fara Zango na 8 ya rika bin Tijjani Asase su zauna a kan shirin, kawai sai Asasen ya nemi cewa zai fita a shirin.
“Kawai sai ya fito cewa zai fara nasa, tunaninsa tunda shi ne yake jan fim din, idan ya fita za a daina fim din ko bibiyar fim din.
“Muna cikin haka ne ya nemi cewa a zo a zauna a yi lissafi a fitar masa da hakkinsa. Haka kuwa aka zauna a ofishin Ado Gidan Dabino, ya bukaci a raba kudin da aka samu, na yarda, ya ce kayan aikin ma a raba, na yarda.
“Na yi haka ne domin ya hakura a ci gaba da fim din. Daga baya kuma ya sake zuwa ya samu Gidan Dabino da Falalu A. Dorayi cewa dole sai an sayar da tashar YouTube din da muke dora fim din a raba kudin. Nan na fahimci cewa akwai matsala babba.
Sanusi Dan Yaro ya ce bayan duk abubuwan da suka wakana, daga baya ya samu Asase domin su ci gaba da aikin, amma ya bayyana masa cewa shi ba zai ci gaba da fim din ba.
Sai dai a martanin da Sani Kabiru Lulu wanda shi ne mai tallatawa da kasuwacin fim din na A Duniya ya yi a wani faifan bidiyo da aka dora a tashar alkuku Hausa tv, ya ce maganganun Dan Yaro karairayi ne kawai.
A cewarsa, “Asase ba zai yi A Duniya ba, kuma ba abin da ya alakanta shi da A Duniya saboda abu ne da ya gina, aka masa cin amana a cikin abin da ya gina, karshe ma aka rushe shi aka ce an kore shi a shirin.
“Kai kuma da ka je ka yi bayani a rediyo, Kanabaro ne ya yi sanadiyar kafa fa ka zama abin da ka zama. Shi ya sa aka koya maka tace finafinai, ya hada ka da abokansa suka fara ba ka aiki.
“Shirin A Duniya labarin Asase, sannan YouTube din ma sunan matarsa marigayiya Zina, wato Zinaru.
“Saboda da ita ce ya sa Zinariya Hausa tv, kuma duk labarin da ake sanyawa a A Duniya daga zango na 1 zuwa 6 duk Asase ne ya tsara.
Sani Lulu ya kara da cewa duk maganganun da Dan Yaro ya yi cewa ya kashe kudade a kan shirin duk karya ne, domin a cewarsa, shinkafa da wake ake ci a ba mutane kudin mota.
“Idan da gaske fim din A Duniya naka ne kamar yadda ka fada, me ya sa ka yarda aka raba kudi da kayayyakin da aka samu sanadiyar fim din.
“Kuma tun da aka fara fim din nan, Asase ai bai taba sanin me ake samu a YouTube ba, kuma a takaice ana samu Naira miliyan biyu a duk fitowa.
“Ba ka yi maganar wannan ba, sai kudin masu turawa ta waya, kuma ba ka taba ba Asase kudin YouTube ba.
Ina aka kwana?
Aminiya ta duba shafin YouTube na Zinariya, inda ta ga tuni an ci gaba da nuna A Duniya din ba tare da Asasen ba.
Fitowa ta karshe na kimanin mako biyu da suka gabata wato fitowa na 94, mutum 286 ne suka kalli shirin.
Sabon shirin da Asase ya fara mai suna Lokaci kuma yanzu ana fitowa na 33, Zango na 3. Fitowa ta karshe wato ta 33 da Aminiya ta leka tashar Tijjani Asase, mutum dubu 43 suka kalla a lokacin ziyarar ta.