Dalilin da aka sake zabena – Danchuwa
Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe kuma dan majalisa mai wakiltar Mazabar Mamudo a Karamar Hukumar Potiskum, Alhaji Auwalu Isa Danchuwa, ya ce saboda al’ummar mazabarsa sun samu ribar dimokuradiyya ne ya sa suka sake zabarsa. Ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce a shekarar 2006 garuruwa biyu ne […]
Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe kuma dan majalisa mai wakiltar Mazabar Mamudo a Karamar Hukumar Potiskum, Alhaji Auwalu Isa Danchuwa, ya ce saboda al’ummar mazabarsa sun samu ribar dimokuradiyya ne ya sa suka sake zabarsa.
Ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce a shekarar 2006 garuruwa biyu ne kadai suke da wutar lantarki a mazabarsa, wato Mamudo da Ayada, amma da ya zama dan majalisa ya samar wa da garuruwa 10 da suka hada da Gwaji, Badejo Yagal Dakasku, Bingel, Maje, Danchuwa, Juma’a, Alhaji Baba da Jalam.
Mataimakin Shugaban Majalisar, ya ce ya yi dalilin samar da hanya mai tsawon kilomita 16, kuma yanzu haka akwai aikin hanya mai tsawon kilomita 18 da ake yi a mazabarsa.
Ya ce daga zaman sa dan majalisa yankinsa ya samu ajujuwan karatu 140 da asibitoci 13, ya ce a baya suna da rijiyoyin burtsatse shida ne kadai amma yanzu suna da 29 a yankin.
Auwalu Danchuwa, ya gode wa mutanen mazabarsa, inda ya shaida wa al’ummar Jihar Yobe cewa su ’yan majalisa 24 suna aiki tare ba wanda ke nuna ya fi wani saboda suna wakiltar jama’arsu.
Ya nemi hadin kai da goyon bayan jama’arsa, inda ya ce kofarsa a bude take don karbar shawarwari masu amfani da za su ciyar da al’ummar mazabar da jihar gaba.