Dalilin da aka samu ƙarin farashin man fetur — Ministan Labarai

Ba mu da hannu a ƙarin kuɗin man fetur da aka yi a ƙasar a ranar Laraba.

Dalilin da aka samu ƙarin farashin man fetur — Ministan Labarai

Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalili yayin da kuma take cewa ba ta da hannu a ƙarin kuɗin man fetur da aka yi a ƙasar a ranar Laraba.

Ministan Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da Aminiya dangane da ƙarin kuɗin man da aka yi baya-bayan nan.

Ya ce “dalilan da suka kawo wannan ƙarin farashin sun haɗa da rikicin Gabas ta Tsakiya, saboda ya haifar da tashin farashin mai a kasuwannin duniya.”

Ministan ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da ba NNPCL da gwamnatin haɗin kai, “Gwamnati za ta yi amfani da kuɗin tallafin da aka cire wajen inganta fannin lafiya da ilimi, tsaro.”

A jiya Laraba ce Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya yi ƙarin kuɗin fetur, inda farashin ya tashi daga naira 897 zuwa 1,030 kowace lita a Abuja, yayin da a Jihar Legas ya tashi daga naira 855 zuwa 998.

A bayanan sabon farashin da NNPCL ya fitar, za a riƙa sayar da duk litar man fetur kan Naira 1,025 a gidajen mansa da ke Kudu maso Yamma sannan a riƙa sayarwa kan Naira 1,045 a Kudu maso Gabashin Nijeriya.

Haka kuma, sabon farashin ya nuna litar man fetur ta koma Naira 1,075 a Kudu maso Kudu da Arewa maso Gabas sannan a riƙa sayarwa kan Naira 1,070 a Arewa maso Yamma da kuma Naira 1,030 a Arewa ta Tsakiya.

Tun a watan Satumba ne NNPCL ya ƙara farashin litar man daga N617 zuwa N897 gabanin ya fara sayen man daga Dangote, yana mai cewa yana fama da ƙarancin kuɗi.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya