Dalilin da aka yi mini lakabin Ali Nuhun Legas-Ibrahim Abdullahi
Aminiya ta samu tattaunawa da matashin jarumi Ibrahim Abdullahi wanda ake yi wa lakabin Ali Nuhun Legas. Ya bayyana dalilin da ya sa ya fara harkar fim. Ga yadda hirar ta kasance:Za mu so ka gabatar da kanka?Sunana Ibrahim Abdullahi. An haife ni a unguwar Markaz da ke cikin karamar hukumar Agege a Jihar Legas. […]

Aminiya ta samu tattaunawa da matashin jarumi Ibrahim Abdullahi wanda ake yi wa lakabin Ali Nuhun Legas. Ya bayyana dalilin da ya sa ya fara harkar fim. Ga yadda hirar ta kasance:
Za mu so ka gabatar da kanka?
Sunana Ibrahim Abdullahi. An haife ni a unguwar Markaz da ke cikin karamar hukumar Agege a Jihar Legas. Na yi makarantar firamare da sakandire a yankin Agege. Daga nan na tsaya da harkar karatu na shiga harkar kwallon kafa gadan-gadan.
Me ya sa ake yi maka lakabi da Ali Nuhun Legas?
Saboda ina sha’awar yadda yake yin wasa da kuma kwarewar da yake da ita. Da jama’a suka lura da haka sai suke kira na da Ali Nuhun Legas. Wasu ma cewa suke yi muna da yanayi iri daya da Ali Nuhu.
Ta yaya aka ka shiga harkar fim ?
Gaskiya na shiga harkar fim ne saboda sha’awa kuma na ga ta fi min harkar kwallon kafa. Ka san komai na rayuwa yana bukatar sha’awa. Idan kana da sha’awar abu to babu shakka idan ka fara shi za ka samu nasara amma idan ba ka da sha’awa ba za ka cim ma burin da ka sa a gaba ba.
Me ya sa ka bar kwallon kafa ka shiga harkar fim?
Gaskiya ga ni na yi lamarin kwallon kafa yana neman ya fi karfina domin samun ci gaba a harkar kwallo yana da wahala, saboda harka ce ta kashe kudi. Za ka samu wakilai masu fita da mutane kasashen waje masu cutar jama’a. Za su karbi kudinka amma sai su gudu. Sun cuce ni har sau biyu, sun karbi kudina amma ba su kai ni ko’ina ba. Sai na ga ina da sha’awar harkar fim sai na shiga domin na ba da gudunmawata.
Me ya ja hankalinka ka a harkar fim?
Abin da ya ja hankalina shi ne na lura cewa a nan Jihar Legas ba mu da ’yan fim din Hausa idan ma akwai su to sun yi karanci, to sai ya kasance na yi tunanin shiga fim domin na wayar da kan jama’a na fadakar da su al’amuran duniya da rayuwa. Kuma idan ka lura za ka ga cewa wadanda suke shirya fim din Hausa a Arewa idan za su zo Legas dole sai sun taho da ’yan wasa. To ka ga kasancewar muna da ’yan wasa a nan idan za su zo shirya fim a nan Legas ka ga ba sai sun sha wahala sun taho da ’yan wasa ba mu za mu iya yi musu duk abin da suke bukata.
Shekarar ka nawa da fara harkar fim kuma fina-finai nawa ka yi?
Ka san mu yara ne yanzu muka fara. Ban dade ba amma na fito a wani fim din ‘Son Masoyi’ wanda ya kunshi labari a kan wata yarinya da iyayenta suke so su yi mata auren dole kuma labari ne wanda ya faru da gaske a zahiri. Na fito a jarumi kuma na yi bajinta sosai domin na yi iya kokarina na ga na yi duk abin da ake bukata.
Wane kalubale ka fuskanta lokacin da aka dora maka kyamara?
Gaskiya lokacin da aka dora mini kyamara na ji das amma da taimakon Allah daga baya sai na ji kamar na dade ina yi. Domin da na fito sau daya ban kara jin wata fargaba ba.
Ba ka tunanin yanzu mutane za su rika yi ma wani kallo musamma yadda wasu ke yi wa ’yan fim kallon mutanen banza?
Kallon da mutane za su yi mini ba zai taka wata rawa ta kashe mini jiki ba, domin na dauki harkar fim sana’a. Kuma Iyayena da ’yan’uwana sun ba ni goyon baya. Saboda haka ba na damuwa da duk abinda jama’a za su fada. Ai a haka ma mutane suna maganganu iri-iri amma ba ma damuwa saboda mun amince cewa fim sana’a ce mai kyau.
Wane buri kake so ka cim ma a harkar fim?
Ina so na samu daukaka mutane su san ni kamar yadda Allah Ya daukaka Ali Nuhu da Sani Danja. Kuma Ina so ni ma na zama ta hanyata mutane na koyon darasin rayuwa da kuma ilimi. Domin ita harkar fim ta kunshi ilimantarwa da nishatarwa.