Dalilin da aka yi wa matan Hausawa zarra a soyayya
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A kwanakin baya ne muka kawo muku mukala a kan kura-kuren da maza suke yi wajen zabar matar aure. Wannan mukalar ta ja hankalin jama’a; maza da mata, inda suka rika turo sakonninsua a kanta. Duba yadda ta dauki hankalin jama’a ne ya sanya muka ga […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A kwanakin baya ne muka kawo muku mukala a kan kura-kuren da maza suke yi wajen zabar matar aure. Wannan mukalar ta ja hankalin jama’a; maza da mata, inda suka rika turo sakonninsua a kanta. Duba yadda ta dauki hankalin jama’a ne ya sanya muka ga dacewar sanya sakonnin da aka turo a kan ta.
Ga alamu har yanzu matanmu na Hausawa ba su farka daga dogon barcin da suke yi ba, duk da irin koma-bayan da suke samu dangane da batun soyayya, musamman ma ta wajen aiwatar da ita, ta hanyoyi da daban-daban.
Dalilan da suka sa aka bar matan Hausawa a baya suna da yawa, amma zan yi kokarin kawo mafi muhimmanci don masu karatu su tatance kuma su yi alkalanci.
Yadda matanmu na Hausawa suke yi wa soyayya rikon sakainar kashi ne ya sa ake samun mace-macen aure a yankunanmu fiye da wasu yankuna na kasar nan. Don alkaluma sun nuna cewa sakin aure ya fi yawa a yankunan Husawa idan aka kwatanta da yankunan sauran kabilun kasar nan.
Kodayake an dan samu canji amma canji bai taka kara ya karya ba. Ina so mutane su fahimce ni sosai, ba so nake na tozarta ko wulakanta ko kaskantar da matanmu na Hausawa ba, ina so ne su dauki darasi su gyara halayensu don a samun al’umma tagari.
boye soyayya: Matan Husawa suna da wani karin magana da suke cewa ‘Namiji ban dan goyo ba ne’. Wato shi namiji ba a nuna masa kauna kiri-kiri. Saboda haka idan mace ta yi kuskuren nuna masa so a fili, to ta gama yawo, saboda a fahimtarsu zai rika cutar da su kuma ya ci amanarsu. Shi ya sa za ka ga da yawa daga matanmu suna boye son da suke yi wa mijinsu ko saurayin da zai aure su. Wanda hakan na sa namiji ya rika ganin matarsa ko budurwarsa ba ta son sa. Zai yi wahala ka ga Bahaushiya ta bude baki ta furta wa miji ko saurayi kalmar so, idan mutum ya yi korafi sai su ce rashin kunya ce mace ta bude baki ta ce tana son da namiji.
Rashin godiya: Matanmu suna da wata al’ada ta rashin godewa kokarin da mazajensu suke yi musu. Ba su nuna godiyar a aikace ko kuma su furta da baka. Akwai matan da suke cewa mazajensu mai suka taba yi musu tun da suka aure su. Wannana dabi’a tana daga cikin abubuwan da suke kawo sakin aure, kuma tana daga cikin dabi’un da suka sanya aka bar matanmu a baya a wajen soyayya.
Raini: Saboda tsabar raini matanmu ne suke cewa mazajensu kaddara ce ta sa suka aure su. Sai ka ji suna cewa ‘Idan ba kaddara ba ban ga dalilin da zai sa na aure ka ba’. Wannan dabi’a ta janyo an yi wa matanmu fintinkau a fagen soyayya, kuma ta janyo karin yawan sakin aure a jihohin Arewa. Babu yadda za a yi Bayarabiya ko Ibo ko wata kabila da muke tare da su a Arewa wadanda ba Hausawa ba a ga suna raina mazajensu har ta kai sun furta irin wannan magana.
Rashin kwarewa wajen yin kishi: Matanmu suna da karancin kwarewa ta wajen yin takara da kishiya. Da yawa idan an yi musu kishiya maimakon su tashi tsaye wajen ganin sun mamaye zuciyar mijinsu da soyayya, sai su tayar da hankalinsu su rika yin rikici da fada da cin zarafin mijin da kishiyar gaba daya. Har ta kai maigidan ya gaji da ita ya sake ta.
Wasu kabilu har gori suke yi mana cewa matanmu ba su iya janye hankalin maigida ta hanyar soyayya ba. Wasu har cewa suke yi idan aka hada su kishi da Bahaushiya sai sun yi galaba a kanta, saboda rashin kwarewarta a wajen kisisina da kissar janye hankalin maigida.
Rashin yi wa miji hidima: A nan ma an yi wa matanmu zarra. Za ka ga sauran matan kabilu suna yi wa mazajensu wanki da guga da wanke takalmi da lura da kwalliyar maigida da gyara masa ado, amma matanmu babu ruwansu, sai dai su ci su kwanta, babu ruwansu da mijinsu, balantana su yi masa wata hidima. Hidimar kawai da za ta yi masa shi ne, ta dafa masa abinci, ko ta kai masa ruwan wanka. Alhali ba su san cewa hidimar da ake zance ta wuce haka ba. Wadansu matan kabilun ma har yi wa majansu sutura suke yi tare da yi musu kyaututtukan bazata. Duk wannan yana kara soyayya da shakuwa tsakanin ma’aurata da masu soyayya.
Ba ina nufin namiji ya kwanta matarsa ta rika yi masa sutura ko ta rika ciyar da shi ba. Abin da nake nufi shi ne, ta rika yi masa hidimar da za ta burge shi.
Za a iya tuntubar Abubakar ta lambar waya kamar haka: 08027406827 ko ta [email protected]