Dalilin da Amurka ta dakatar da shigar da bandar kifi daga Najeriya

Kasuwannin kasar Amurka sun dakatar da shigar da bandar kifi daga Najeriya tun watan Fabarairun bana kamar yadda kungiyar masu kiwon kifin tarwada da sauran kifi ta Najeriya (CAFFAN) ta sanar. Shugaban kungiyar CAFFAN na kasa, Mista Oloye O. Rotimi, ne ya bayyana wa wakilinmu haka bayan zabar sababbin shugabannin kungiyar reshen Birnin Tarayya Abuja […]

Dalilin da Amurka ta dakatar da shigar da bandar kifi daga Najeriya

Kasuwannin kasar Amurka sun dakatar da shigar da bandar kifi daga Najeriya tun watan Fabarairun bana kamar yadda kungiyar masu kiwon kifin tarwada da sauran kifi ta Najeriya (CAFFAN) ta sanar.

Shugaban kungiyar CAFFAN na kasa, Mista Oloye O. Rotimi, ne ya bayyana wa wakilinmu haka bayan zabar sababbin shugabannin kungiyar reshen Birnin Tarayya Abuja a karshen makon jiya.

Dalilan dakatarwan biyu ne da suka hada da: “Na farko ma’aikatan gwamnati na cikin wadanda suka haddasa faruwar hakan, saboda akwai bukatar cike takardun ka’idoji da ya kamata su yi da sashen noma na kasar Amurka amma ba su yi ba, wanda har sau uku ana bukatar su yi, suka ki bin ka’idar da kasar Amurka take so, don haka suka yanke shawarar dakatar da shigar da bandar kifi daga Najeriya zuwa kasar. Wannan matsalar tana nan tun daga watan Fabarairu 2018 har zuwa yau”.

“Wani dalilin kuma shi ne, ana kwace kifin bandar da lalata shi daga hannun masu sana’ar kifin a hanyarsu ta zuwa Amurka. Akwai mai kiwon kifin da ya fitar da shi zuwa Amurka wanda kudinsa ya kai Dalar Amurka dubu 55, amma duk ya yi asararsu, sanadiyyar sakaci daga bangaren ma’aikatan gwamnatin Najeriya,” inji Mista Oloye.

Ya ce, wadansu jama’a daga Nahiyar Afirka na amfani da damar Najeriya, wajen shigowa Najeriya su tafi da kifin Najeriya su gyara su, yayin da za su rika cewa, wannan kifi banda na kasar Ghana da Kenya ne, sai su aika kifin zuwa Amurka. Lokacin da na ziyarci wasu shagunan kasashen Afirka a Amurka, na fahimci cewa, kifin Najeriya ya fi na kowace kasa kyau,” inji shi.

Mista Oloye, ya yi karin haske game da matsalolin da kamfanonin noma ke fuskanta a Najeriya da suka hada da: karancin jari, tallata haja, tsadar abubuwan da ake bukata da karancin manoma masu ilimi a harkar.

A yayin da wakilinmu yake ganawa da sabon shugaban kungiyar CAFFAN reshen Abuja, Alhaji Mundu H. Mohammed, ya yi alkawarin tsara hanyoyin da za su taimaka wa masu kiwon kifi a Abuja don amfaninsu.