Dalilin da ba a fara biyan masu hidimar ƙasa N77,000 ba — NYSC
Bayanin da muka samu ba a ce mana yaushe za a fara biya ba, amma dai an tabbatar mana cewa an yi musu ƙari.
Hukumar NYSC ta ce dalilin da ya sa aka samu jinkirin soma biyan sabon ƙarin alawus ɗin masu yi wa ƙasa hidima, shi ne gwamnati ba ta sakar wa hukumar kuɗin sabon ƙarin ba.
Shugaban hukumar, Birgediya Janar Yus’au Dogara Ahmed ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da BBC Hausa.
- 2027: Neman tazarce ba ya gabana yanzu — Tinubu
- Sana’ar Bola-jari: Muna taka sawun barawo — Shugaban ‘yan gwangwan
Ya bayyana cewa, a hukumance sun samu takardar amincewa da ƙarin, amma ba a riga aka sakar wa hukumar kuɗin ba.
“Ai ba ma masu hidimar ƙasa kaɗai ba, har ma’aikatan hukumarmu su ma an yi musu ƙarin, su kan nasu ma ya kai kusan wata huɗu zuwa biyar, amma ba a fara biyansu ba.
“Amma muna sa rai nan ba da jimawa ba, za a fara biya, amma bai riga ya zo hannunma ba tukunna,” in ji shi.
“Bayanin da muka samu ba a ce mana yaushe za a fara biya ba, amma dai an tabbatar mana cewa an yi musu ƙari daga ranar 29 ga watan Yulin 2024,” kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne Hukumar NYSC ta fitar da sanarwa ƙari a alawus ɗin masu yi wa ƙasa hidima daga naira 33,000 zuwa 77,000.
Sanarwar ta ce ƙarin sabon alawus ɗin zai fara aiki ne daga watan Yulin wannan shekarar, abin da ke nuna cewa masu yi wa ƙasa hidimar za su samu ariyas na aƙalla wata uku.
To sai dai da dama daga cikin masu hidimar ƙasar sun saka rai da ganin ƙarin a alawus ɗin a watan da ya gabata.