‘Dalilin da ba a samun isasshiyar wutar lantarki a Nijeriya’
Injiniyoyin Nijeriya sun kware. Sai dai rashin wadanda za su mayar da hankali.
Injinya Hamza Ibrahim, kwararren injiniya ne da ya kwashe tsawon rayuwarsa ta aiki a tsohuwar Hukumar Wutar Lantarki ta Kasa (NEPA) inda ya fara aiki a matsayin karamin injiniya a 1969 har ya kai mukamin Manajan Darakta a 1990 zuwa 1999. Har ila yau shi ne Barden Dutse a jiharsa ta Jigawa.
A tattaunawa kan rayuwarsa a filinmu na TunaBaya ya yi tsokaci kan al’amura da dama ciki har da batun wutar lantarki:
Za mu so sanin tarihin rayuwarka?
Ni Babarbare ne. A lokacin yakin Rabe, kakana Sulaiman Mai Dugu da jama’arsa daga garin Kukawa suka yanke shawarar yin kaura zuwa Kano.
A kan hanyarsu suka isa Misau. Ayarinsu uku ne; daya ayarin sai suka tafi Gombe, dayan suka nufi Lafiyan Barebari.
A Jihar Nasarawa?
Eh. Ayarin kakana sai suka yanke shawarar tafiya Kano. A hanyarsu sai suka isa Gwaram a Jihar Jigawa ta yanzu.
A nan ne suka hadu da Malam Lawan wanda shi ne Sarkin Gwaram. Kuma malamin addini ne su kuma dama malaman Alkur’ani ne.
Sai ya yi musu alkawarin zai ba su wuri mai kyau a wajen, inda akwai wani ruwa da ya taso daga Jihar Filato da Kogin Jama’are da sauransu. Wurin kasar noma ce sosai.
A wurin akwai wani kududdufi da ake kira Injari wanda yake kusa da garin. Ana amfani da shi wajen noman rani na kayan marmari da na lambu da sauransu.
Sai suka ga dama ce a wurinsu wacce ba za su iya tsallakewa ba, don haka suka amince suka zauna a Gwaram.
Daga nan aka yi wa Mai Dugu, Mai Unguwar Barebari.
Ya zauna a dukkan wadannan wurare?
Eh a wurare uku ko hudu. Bayan rasuwar kakana sai Alhaji Ibrahim Chindorima ya zama Mai Unguwar Barebari.
Har zuwa yanzu zuriyarmu ce ke sarautar wannan wuri.
A ina ka samu sarautar Barden Dutse?
Sarki ne ya yi min domin girmama ni. Sarautar Barden Dutse ne ba Gwaram ba.
Sarki ya ba ni wannan sarauta ce don yaba wa gudunmawar da na ba Jihar Jigawa a lokacin da nake Shugaban Hukumar NEPA.
A lokacin na hada kauyukan Jigawa da dama da wutar lantarki. Game da tasowa ta na yi Makarantar Elementare ta Gwaram daga 1952 zuwa 1956, sai Babbar Firamaren Kimiyya ta Birnin Kudu.
Abokan karatuna sun hada da Abubakar Rimi da Umaru Musa Zandam da Abdurrazak Kiyawa da wasu da dama.
A 1958 Kyaftin Tranchard Murphy wanda shi ne Shugaban Cibiyar Koyar da Ilimin Sana’a da Kere-Kera ta Kaduna ya zo ya gana da mu uku a Kano.
Ni da Umaru Musa Zandam da Wali Sule Ahmad daga Firamaren ta Birnin Kudu.
Kuma akwai wani Mai suna Rabiyu Aliyu da wani mutum daya.
Ba mu labarin zamanka a Gwaram a matsayinsa na Babarbare?
Ai mu mun zama ’yan Gwaram duk da cewa abin rashin dadi shi ne ban iya harshen Barbarci ba.
Bayan mun yi wannan ganawar sai muka samu gurbin karatu a makarantar ta Kaduna (Kaduna Polytechnic a yanzu).
Makarantar ta kunshi sakandare da makarantar koyon aikin injiniya da makarantar koyon harkokin kasuwanci.
Umaru Zandam, Shu’aibu Koli da Rabiyu Aliyu suka tafi sakandaren kerekere, yayin da Sulaiman Wali Ahmad da ni muka tafi makarantar injiniyanci.
A makarantar aikin injiniya muka hadu da Bodunrin, David Ologe da Babalola, Babatunde, wadanda ’yan Kabba ne da ke tsohuwar Jihar Kwara.
A lokacin Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello Sardauna bai nuna bambanci tsakanin Musulmi ko Kirista.
A lokacin akwai Yarbawa da yawa ya yi kokarin hada kan ’yan Arewa babu ruwansa da kabilanci.
Shin kai ka zabi ka zama injiniya ko sa ka aka yi?
Eh. Gaskiya da ma ina son ia zama injinya.
Ga shi kuma lokacin da na yi karatu a Makarantar Fasaha ta Kaduna na samu satifiket wanda daidai yake da Diploma a kan injiniyan lantarki don haka na zabi karanta aikin injiniya.
Me ya ba ka sha’awa ka zabi zama injiniya kana matashi?
Tun dama can ina sha’awar zama injiniya. Saboda ina jin labarai a BBC da wasu kafafen watsa labarai a kan aikin injiniya sai hakan ya sa min sha’awar in zama injinya.
A matsayina na yaro karami jirage da makamantansu suna karfafa maka gwiwa ka ji kana so ka zama injinya.
Yaya aka yi ka samu tallafin karatu zuwa Ingila?
Kamar yadda na fadi shi Sa Ahmadu Bello Sardauna babu ruwansa da batun kai Bahaushe ne ko Bafulatani ko Bayarbe.
Idan har ka cancanta za a dauke ka. Hakan ya sa aka dauki David Ologe daga Kabba da ni kuma Hamza Ibrahim.
Wannan ya faru ne a 1964. Domin na kammala karatun karamar difloma a 1963 har na fara aiki a ofishin NEPA a Jos.
A lokacin aikinmu shi ne a tura mu wurare don hada falwayar wutar lantarki.
Lokacin da ka samu tallafin karatu zuwa Ingila yaya ka ji lura da karancin shekarunka?
Gaskiya abin ya zo min a wani sabon al’amari. Domin na hadu da kalubale.
Yaya aka yi ka iya zama a can ga karatu ga canjin wuri?
Ta bangaren karatu na yi sa’a domin na hadu da mutanen kirki da ke aiki a BBC bangaren Hausa.
Ina tare da wani abokina marigayi Inawu Garba wanda dan Kaduna ne.
Shi yake zuwa ya dauke ni daga Kaduna mu tafi Landan.
Bayan ka gama karatu sai ina?
Bayan na gama sai na fara aiki da BBC a matsayin mai ba da gudunmawa da safe.
Ina fassara labarai daga Ingilishi zuwa Hausa sannan in karanta.
A can ne na hadu da Farfesa Ibrahim Ayagi da MalamMuhammad Ibrahim da marigayi Ciroman Keffi da wasu da dama.
A matsayinka na wanda ya karata injiniya, yaya aka yi ka iya karanta labarai a BBC?
Bayan na karanta labarai da safe idan ma’aikacinsu saboda wani dalili bai zo aiki ba sai a ba ni in karanta har sai da ta kai wata rana shugabansu ya ce na burge shi.
Tsawon wane lokaci ka kwashe a Landan shin ka yi kokarin canza aiki?
Daga 1964 zuwa1969. Duk da cewa na gama a 1968. Na zauna a BBC na wasu watanni a matsayin mai bayar da gudunmawa daga waje.
Da ka dawo Nijeriya wane aiki ka yi a lokacin ka zama kwararren Injiniya. Ina jin ka dawo zuwa NEPA ce kamar yadda aka san ta a lokaci…
Eh, a lokacin an hade Hukumar Madatsun Ruwa ta Neja da Kamfanin Lantatki. Ina jin a 1972.
Lokacin da na dawo sai na fara aiki a Legas. Daga baya suka mayar da ni Jos a matsayin cikakken injiniya.
Lokacin wutar lantarki da ake bayarwa ita ce 3.3 KB inda na kara ta zuwa 11. KB a can ne ma na yi aure.
Daga Jos na tafi Kano a matsayin injiniyan gunduma. Daga Kano sai na tafi Maiduguri. Na sha wahala a wancan lokaci saboda ba su da layin wuta. Injunan janerata ne ake amfani da su.
Sai daga baya muka samu aka hada layin wutar aka dasa taransfoma mai karfin 2×35 MBA tare a sanar da wasu abubuwan inda har aka iya bayar da wuta a garin.
Akwai lokacin da za ka iya cewa an samu tsayayyiyar wutar lantarki a kasar nan koda a manyan birane?
Mun hadu da wahala a lamarin. Kamar yadda ka sani ba mu samun kudi a shekarun 1990 zuwa 1997.
Ina jin a wadancan shekarun bakwai an ba mu Dala miliyan 109.5 kawai.
Kasafin kudin a kan Dalar Amurka aka yi?
Idan ka dauki 1994 misali mun kasafta Naira miliyan 142 ne, a lokacin Dala tana da darajar Naira 22 don haka gaba daya muna da kiyasin Dala miliyan 6.45.
Mu kuma mun samar da Naira biliyan 5.5. Wani abu shi ne ba mu samu Naira miliyan 142.
Dole ne mu sa hannu a kan yarjejeniya a tsakaninmu da Ma’aikatar Kudi kuma a ba mu bashi a kan kudin ruwa na kaso bakwai. Idan ka lura akwai wahala a lokaci.
Akwai wani lokaci da Bankin Duniya ya zo ya ga irin wahalar da muke ciki. Su da kansu suka ce lallai maaikatan NEPA suna yin kokarin.
Sun ga yadda muke kokarin samar da wutar da wannan dan kudi. Ga shi a lokacin ana karbar Naira daya a kan duk kilowat na awa daya.
Shin karancin kudin wuta da ake biya ne ya janyo rashin samunta?
Ba haka ba ne. A lokacin ya kamata a ce an kara kudin wutar lantarki amma ba a yi haka ba.
A duk lokacin da muka nema sai gwamnati ta ce wai mu bi a hankali.
Kamar abin da ke faruwa yanzu ne yadda ga shi an sayar da wutar kamar yadda na fahimta tiriliyoyin Naira ake fitarwa ana sanya wa a harkar.
Za ka yi mamaki mu ko a wancan lokaci ba a ba mu komai da sunan tallafi.
Wato ko a lokacin da aka fara, kamfanoninn wutar lantarki ba su taba samun isassun kudin da za su iya bayar da tsayayyiyar wutar lantarki a kasar nan ba?
Kwarai kuwa domin akwai bashin Turawa da yawa a kan gwamnati.
Amma ai mun samu kudin mai in ana batun kudi ne? Me ya faru?
A lokacin muna amfani da kudin shigar da muke samu na cikin gida don mu iya gudanar da ayyukanmu.
A lokacin har mukan biya albashin wata na da kwana 13, a matsayin yaba kokarin ma’aikata duk da matsalar rashin kudin da muke fuskanta muna iya kula da ma’aikatanmu.
Sai dai ba ku iya samar da wutar lantarki tsayayyiya ba ko?
A 1992 ba mu taba samun lokacin da wuta ta fadi ba haka a 1996. Ka duba ka ga yadda ma’aikatan NEPA suka yi kokari kwarai duk da cewa babu isasshen kudi.
Amma mutane ba su taba yaba mana ba Rashin faduwar hanyar wuta ba shi ne ke nufin samun tsayayyiyar wutar lantarki ba.
Shin kana nufin ba a taba samun faduwar wutar gaba daya kamar yadda muke gani a yanzu ba?
Eh, haka ne musamman a irin wuraren da suke da matsala.
Har yanzu muna da matsalar wuta?
Eh, haka ne. Ba mu da wutar da za ta ishi kowane gida da kasuwannni da masana’antu. Ba mu iya bayar da wutar awa 24.
A matsayinka na injiniya ka yi aiki har ka zama Manajan Daraktan Hukumar NEPA a 1990, na yi zaton wannan mukamin na siyasa ne, ba na aikin injiniya ba ne?
Ba siyasa ba ce, na fada maka na fara aiki a matsayin karamin injiniya. Ban taba tsallake wani matsayi na aikin injiniya ba.
Kana nufin sai da ka je kowane matsayi, bi-da-bi ke nan?
Gaskiya ne domin ni ne mutumin da ya taba zama Mataimakin Darakta ba a kuma sake yin haka ba. Sannan daga bisani na zama darakta.
Ni mamba ne a a Makarantar Injiniyoyi da kuma Kungiyar Injiniyoyi ta Kasa.
A takaice na cancanta in rike wannan matsayi. Ni Injiniya ne mai rajista.
Shin ta yaya aka sanar da kai wannan matsayi?
Ina Umarah a lokacin da wata gobara ta auku. Bayan na dawo na zama Janar Manaja a cikin wani mawuyacin hali.
An nada ni Janar Manaja na wucin-gadi daga bisani aka tabbatar da ni a mukamin.
Na fara aiki a hukumar ce a lokacin da take cike da matsaloli.
Muna da wasu ma’aikata masu tsatstsaurar ra’ayi da suke kiran kansu ’yan kungiyar jin dadin ma’aikata.
Sun tura shugabanin kungiyar gefe guda, wadannan masu tsatstsaurar ra’ayi suka haye kujerar shugabancin ma’aikatan a wasu bangarori.
Daga tashoshi daban-daban suka zo tashar Egbin domin ta da tarzoma. Sun ce wai za su shiga yajin aiki har sai mun kara masu albashi da alawus.
A lokacin akwai doka da ta hana karin albashi. Wannan lokaci wani irin yanayi muka shiga mai sarkakiya.
Na shiga tunanin yadda za a yi mu fita daga wannan sarkakiya tunda ba za mu yarda a rufe wajen ba a lokacin.
Akwai rikicin siyasa don haka dole ne a dauki mataki. Ni da Babban Jami’in Sashen Kudi Mouftah Baba Ahmed muka yarda mu yi wani abu.
Dole muka nemi ma’aikatan masu taurin kai a lokacin akwai matasa ’yan bana-bakwai da ke ta da hatsaniya, amma a cikin dare na yanke shawarar zuwa tashar.
Babban Sakataren Sashen Samar da Wutar Lantarki, Ben Cabin wanda injiniya ne bai da lafiya amma sai na biya ta gidansa domin ganinsa saboda ina ganin bai dace ba in ziyarci tasharsa ba tare da saninsa ba.
A kan hanya, direbana ya ce min bai dace mu wuce kai-tsaye ba saboda yin haka akwai hadari.
Ya ce ana iya kai mana hari don haka sai ya ba da shawarar mu dauki sojoji ko ’yan sanda su yi mana rakiya.
Na ce masa ba za mu je da kowa ba tare za mu je a matsayin Janar Manaja a ce zan je ganawa da ma’aikata na sai da rakiyar sojoji ko ’yan sanda.
Kawai sai na je a haka.
Ko ka iya magance matsalar?
Mun je wurin cikin dare muka yi taro. Mun kara masu albashin tare da ba su wasu kudaden da suka hada da alawus.
Suka ce wai abin da muka ba su na wucingadi ne saboda suna son albashinsu ya yi daidai da na ma’aikatan Kamfanin NNPC.
A kusa akwai Ma’aikatan Gas ta Kasa inda mai kula da wurin aikinshi kawai kunna gas amma albashinsa ya fi na ma’aikatanmu.
Sun nuna suna aiki ne cikin hadari amma kuma albashinsu bai kai na ma’aikatan NNPC ba, don haka suke ganin suna bukatar albashi mai gwabi.
Muka tattauna inda muka kara masu albashi da alawus tare da sanar da su cewa akwai takunkumi daga gwamnati.
Shi ya sa a lokacin da na zo na fahimci ina cikin matsala. Amma Allah Ya taimake ni, gwamnati ba tare da na sha wahala ba ta aminci da karin.
Wani abin kuma shi ne dukkan bankunan suna yajin aiki amma sai muka samu damar kula da wasu bangarori na samar da wutar lantarki. Muka samo helikwatfa.
Muna da su har uku da suke zirga-zirga da zarar akwai matsala a kowane layi za su tashi su je don sanin matsalar.
Muka kai daya daga cikin jiragen Marina da zarar yaran nan marasa kunya sun hango jirgin na zuwa sai su ruga domin a tunaninsu sojoji ne ko ’yan sanda ke sintiri.
Jakunkunan kudi?
Eh, sun taso ne daga Cibiyar Kula ta Kasa da ke Oshogbo.
Mun fada masu cewa akwai manyan baki da ke zuwa sun dauka kila sojoji ne ko ’yan sanda ko wasu can.
A lokacin da jirgin ya sauka sai suka ga an dauko jakunkuna da kudi.
Muka fada masu ai albashinsu ne sai suka cika da farin ciki. Wannan shi ne sakamakon biyayya.
Idan ka nuna kula ga ma’aikatanka ko shakka babu za su kasance masu biyayya ga ma’aikatar ko kamfanin.
Mun yi wasu abubuwan da yawa sannan har na kammala wa’adina babu yajin aiki.
Haka mun dauki ma’aikata aiki wajen ’yan Arewa 400 a cikin wannan matsanancin yanayi.
Abin da muka yi shi ne mun yi kididdigar ma’aikata a hukumar. Muna da ma’aikata 36,000.
A yayin da wasu jihohi ke da ma’aikata 3,000, wasu na da 2,000 wasu 1,500 amma a jihata ta Jigawa muna da ma’aikata 200 ko 300 ne kacal.
Don haka sai muka ce mutanen da suka karanci fannin injiniya su zo neman aiki.
Wasu daga cikin manajojin suka ce za su bincika sashin da za a sa wadanda aka dauka.
Yanzu yawancinsu ne ke rike da manyan mukamai a kamfanin wutar lantarki a kasa.
Mun yi haka ne cikin sauki ba tare da matsala ba domin mutane sun fahimci manufarmu.
A matsayinka na tsohon Janar Manaja na NEPA ina matsalar take ne inda kasa mai tarin jama’a akalla miliyan 250 amma take da wuta megawat 4000 zuwa 5000 kacal?
Ina ganin rashin hangen nesa ne da tunani, idan babu manufa ba za a samu wuta ba.
Shi ya sa muka samu tsarin Vision 2010.
Kana da cikinsu ne?
Eh.
Mun kasa cim ma wannan manufa ke nan?
Kwarai kuwa, amma fa Injiniyoyin Nijariya sun kware. Kuma suna daga cikin kwararru a duniya.
Akwai lokacin da Bankin Duniya ya zo wurinmu domin ba mu shawarar yadda za mu inganta karfin wutar lantarkimu.
Wasunsu mambobin kungiya ko cibiyar injiniyoyin lantarki ne a yayin da mu kuma a lokacin muna da kwararrun ma’aikata a NEPA.
Muna da masu shaidar takardar digiri na uku, don haka mu ne ya kamata mu karantar da su ba su karantar da mu ba.
Saboda haka abin da kawai suka yi shi ne tambaya aka kuma ba su amsa. Suka rubuta abin da muka fada masu suka mika rahotonsu. Muna da kwararrun injiniyoyin a duniya .
Injiniyoyin Nijeriya sun kware. Sai dai rashin wadanda za su mayar da hankali wajen ganin an yi abin da ya dace a Mambila.
Shekara nawa ke nan ake magana a kan Mambila? Me ya kamata a yi ke nan?
Eh, zan yi kira ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya tuna da Mambila.
Ba ina nufin su hana babban aikin titin ba ne amma kuma su tuna da Mambila da batun aikin hanyar bututun samar da iskar gas.
Sannan a tabbatar da batun iskar gas din ya kai Abuja da Kaduna da Kano domin a samu damar gina wasu tashohin wutar lantarki don samun ingantattaciyar wuta da za a rika bai wa abokan hulda.
Abin takaici ne kasar Afirka ta Kudu duk da cewa ita ma tana da matsala a yanzu amma ce wai har za su iya samar da wutar lantarki megawatt 50,000 amma mu muna nan a 4000 zuwa 5000 na megawatt.
Idan muna da niyya za mu iya samar da kudin da ake bukata. Sai kana da tsayayyiyar wutar lantarki ce za ka iya ci gaba a duniya.
Akwai kuma mutane da yawa da ke sintiri a tituna da ba su yin komai. Wannan matsala ce da ya kamata mu kula da ita.
Da zarar sun samu aikin yi ba za a samu masu garkuwa da mutane ba.
Dole a kafa dokar ta-baci a fannin wutar lantarki kuma a zuba makudan kudi saboda idan kana da wutar lantarki komai zai zo da sauki.
Wannan ne hanyar ci gaba a zamananace.
Mene ne ra’ayinka game da sayar da Hukumar NEPA da aka yi?
Ina ganin an yi gaggawa, yanzu muna cewa ba za mu iya samar wa mutane mita ba.
Wanda kuma babban tushen kasuwanci shi ne iya bai wa mutane mita domin sanin iya wutar da mutum ke sha saboda a samu kudaden shiga.
Me ya sa kake ganin akwai bukatar yin amfani da wutar sola ? Ko dama na cikin tsarin samar da wutar lantarki ne a kasa?
A yanzu dai batun wutar sola mai amfani da rana ce kan gaba kuma saboda ci gaba da aka samu a bangaren kimiyya za a iya samar da wuta ta hanyar rana.
A baya mutane sun dauka cewa batun wutar sola a gida kawai ake bukatarta amma ana iya amfani da ita a manyan abubuwa.
Wasu mutane ma na cewa ko a sahara kana iya samar da wutar sola. Abu ne mai yiwuwa.
Me kake yi tunda ka yi ritaya a 1999?
Babu wani abu sosai domin na kusa cika shekara 80. Abin da kawai nake yi yanzu shi ne in je filin wasan golf. Nan ne ofishina yanzu. Akwai ’yan ababe da nake yi.
Na kasance daya daga cikin mambobin Kamfanin Samar da Wutar Lantarki, shi ke nan.
Ina bukatar hutu ne kawai domin idan ka yi ritaya bayan shekara 35 a sashen samar da wutar lantarki a lokacin mai tsanani dole ka bukaci hutu.
Alhamdulillah, ina cikin koshin lafiya zan iya ci, zan iya sa kaya in tafi duk inda nake son zuwa.
A kullum ina mika godiyata ga Allah kan dukkan rahamomin da Ya yi min musamman ta lafiya.
Wasu su kan bude wasu abubuwa bayan ritaya ko noma haka?
Ina da babbar gona a Gora akwai wata kuma a nan Kaduna. Ina kuma da wata gonar a Gwaram.
Sai dai abin sai hakuri saboda dole sai ka je wurin.
Har yanzu kana zuwa Gwaram?
Eh, lokaci bayan lokaci.
Kana fita kasar waje?
A’a, amma ina zuwa Umarah lokacin Ramadan. Ina zuwa yin ibada.
Yaya batun zuwa duba lafiya da sauransu?
Ina cikin koshin lafiya, amma nakan je idan ta kama.
Ina kafi sha’awar zuwa?
Na kan je Ingila saboda a can ne na yi karatu sai kuma Saudiyya. Ina ganin zuwata Amurka bai fi sau biyu ba.
Bayan ga wasan golf, me kake yi don walwala?
Karanta jaridun Daily Trust, kallon Trust TV da CNN da sauransu. Da na yi Sallah da safe, sai karanta Alkur’ani domin godiya ga Allah.