Dalilin da ba mu rikici da gwamnati a yanzu – Sheikh Turi
Sheikh Muhammad Turi shi ne Na’ibin Sheikh Ibrahim Zakzaky kuma jagoran ’yan uwa Musulmi a Kano. A ranar Asabar da ta gabata ya ziyarci garin Saminaka da ke Jihar Kaduna inda ya halarci maulidin da kungiyar ’yan uwa Musulmi suka shirya. Wakilinmu ya tattauna da shi kan halin da ake ciki a kasar nan da […]
Sheikh Muhammad Turi shi ne Na’ibin Sheikh Ibrahim Zakzaky kuma jagoran ’yan uwa Musulmi a Kano. A ranar Asabar da ta gabata ya ziyarci garin Saminaka da ke Jihar Kaduna inda ya halarci maulidin da kungiyar ’yan uwa Musulmi suka shirya. Wakilinmu ya tattauna da shi kan halin da ake ciki a kasar nan da wasu abubuwa da suka shafi kungiyar:
Aminiya: Allah gafarta Malam ina mafita dangane da halin da aka shiga a Najeriya?
Sheikh Turi: To, mafita dai ga al’ummar Najeriya dangane da halin da ake ciki shi ne addinin Musulunci, kuma addinin Musulunci a matsayin mafita a Najeriya, ba bako ba ne. Musamman idan mutanen Najeriya za su tsaya su yi wa kansu fada su yi tunani. Domin kamar a shekarun baya, Allah Ya tayar da malamin addinin Musulunci Shehu Usman danfodiyo wanda ya kawo gyara a cikin al’ummarmu. Ka ga Shehu danfodiyo ba wata jam’iyya ya kafa ba, ya maida zukatan al’umma ne zuwa ga Allah. Saboda haka gyaran zukatan al’umma, talakawa da shugabanni a sanya tsoron Allah zukatansu mai hakki a ba shi hakkinsa, shi ne kawai zai kawo mana gyara a kasar nan. Amma a yanzu wasu suna neman shugabanci ne domin su ci hakkin jama’a, kuma idan aka ci gaba da yin haka za mu kara shiga duhu a kasar nan. Don haka mafita ga al’ummar kasar nan, shi ne mu koma zuwa ga Allah, mu koma zuwa ga tsarin addinin Musulunci, wanda shi ne mafita ga Musulmi da wadanda ba Musulmi ba. Domin tsarin ya koyar da yadda za a yi zamantakewa da wanda ba Musulmi ba. Kowanne Musulmi ya san tarihin addinin musulunci, a lokacin da abubuwa suka yi tsauri a Makka, Manzon Allah (SAW) ya tura Musulmi zuwa kasar Habasha wurin Sarkin kasar Najjashi wanda Kirista ne. Saboda haka yana da muhimmanci kwarai da gaske mutanen kasar nan Musulmi da Kirista su sa hankali da basira a cikin al’amuransu. Musulmi ya kamata su gane masu kokarin su yi amfani da Musulunci, domin su zalunci al’umma ba addinin ya dame su ba. Haka su ma Kirista ya kamata su gane wannan, domin akwai Kiristan da suke da mukamai da suke fakewa da addini suke wawushe dukiyar al’umma, duk da Musulmi da Kiristoci akwai irin wadannan.
Saboda haka talakan Najeriya Musulmi da Kirista ya kamata ya sanya hankali da tunani a cikin al’amuransa. Domin ba daidai ba ne talaka Musulmi ko Kirista su je suna kashe junansu suna tashin hankali ba, domin ba shi da alheri, babu wanda zai amfana, face irin wadanda suke wawushe dukiyar al’umma. Duk wanda ya san san tarihin kasar nan kafin bayyanar Shehu Usman danfodiyo, ya san yadda sarakuna suke ta zalunci, Shehu danfodiyo ya zo ya mayar da mutane kan addinin Musulunci aka samu tarbiyya da zaman lafiya.
Aminiya: Me za ka ce kan kisan gillar da ake yi wa malamai a kasar nan musamman wanda aka yi wa marigayi Sheikh Albani a makon da ya gabata a Zariya?
Sheikh Turi: Shi kisan gilla babu shakka abin takaici ne, domin kashe dan Adam abu ne mummuna malami ne ko ba malami ba. Babu shakka abin takaici ne yadda kasar nan ta fada tarkon makiya ta yadda maimakon mutumin kasar nan ya samu kariya da walwalar rayuwa, sai ya zamana ran dan Adam an wayi gari ba a bakin komai yake ba. Duk kasar da abubuwa suka tabarbare, mai laifi na farko shi ne hukuma. Saboda haka wannan abu da ke faruwa ya nuna cewa hukuma ta gaza.
Aminiya: Wasu suna cewa sukar da kuke yi wa gwamnati a baya, kamar yanzu abin ba haka yake ba mene ne gaskiyar wannan magana?
Sheikh Turi: To mutane su ne za su yi hukunci, domin yanzu na ce maka laifin hukuma ne tabarbarewar al’amura a kasar nan. Don haka ni ban san abin da wasu suke son mu yi ba. Da ma mu kira muke yi, ko a baya ba mu taba far wa kowa ba, sai dai a zo a far mana a kashe mu a kama wasunmu a daure. Saboda haka in ba ka ji an karkashemu ba, to wadanda suke kashe mu ne ba su zo ba.
Aminiya: To, mene ne gaskiyar zargin da wasu suke yi wa wannan kungiya cewa gwamnatin Jonathan tana son ta yi amfani da ku, don zarcewa a zaben shekarar 2015?
Sheikh Turi: Wannan hasashe ne mara tushe. Ka san shi dan Adam ba za ka raba shi da irin wannan hasashe mara tushe ba. Don haka maganar gaskiya babu tushe a wannan hasashe.
Aminiya: Wane sako ko kira ne kake da shi ga al’ummar kasar nan?
Sheikh Turi: To, babban sako shi ne sha’anin hadin kai ya kamata mutane su sanya hankali da basira su hada kansu. Musulmi su fahimci juna su yi hakuri da junansu su hada kansu kuma su hada kai da wadanda ba Musulmi ba. Wannan shi ne zai kawo mana zaman lafiya da ci gaba a kasar nan tamu.