Dalilin da ba zan tsoma baki kan rikicin Masarautar Kano ba — Shekarau

A ranar da maganar ta kai ga zuwa kotu, na ce ba zan yi magana ba ko tsoma baki a cikinta ba.

Dalilin da ba zan tsoma baki kan rikicin Masarautar Kano ba — Shekarau

Sanata Malam Ibrahim Shekarau

Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana damuwa kan dambarwar da ke faruwa a Masarautar Kano.

Shekarau ya bayyana cewa rikicin masarautar lamari ne da ke ci masa tuwo a ƙwarya amma ba ya son tsoma bakinsa a ciki.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin ɗin Channels a ranar Juma’a.

Sai dai Shekarau ya ɗora laifin rikicin masarautar kacokam a kan ’yan siyasa, inda ya yi fatan cewa za a warware shi nan ba da jimawa ba.

“Ni babban mamba ne a Majalisar Masarautar kuma baya ga haka na yi mulkin jihar. Domin haka ni babban ɗan jihar ne.

“A ranar da maganar ta kai ga zuwa kotu, na ce ba zan yi magana ba ko tsoma baki a cikinta ba duk abin da zai faru.

“Abin na damu na. Ni ɗan Kano ne. Ina son zaman lafiyar Kano a kodayaushe. Muna nan muna jira sannan addu’a ta ita ce a kawo ƙarshen rikicin nan ba da jimawa ba.

“Za a samu kwanciyar hankali, muna buƙatar masarautun gargajiya. Ba zan yi magana sosai a kan hakan ba saboda ina ɗaya cikin masu riƙe da sarauta.

“Batun siyasa ne ya sanya muka tsinci kanmu cikin wannan rikicin. Idan da a ce ’yan siyasa ba su shiga ciki ba, sannan da an tuntubi masarautun gargajiyar ta hanyar da ta dace, da ba mu samu kanmu cikin wannan matsala ba.”

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna