Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo
A bana, sai da ƙyar muke iya fita da tireloli biyu a mako. Wannan saboda yadda manoma da yawa ba su samu damar noman cittar ba ne sosai.
A yayin da farashin buhu daya na danyar citta da ke a matsayin iri ya yi tashin gwauron zabon da ba a taɓa ganin irin sa ba, inda ake sayar da shi a kan Naira 210,000 kowane buhu, shi kuwa busasshen buhun citta ana sayar da shi ne daga Naira dubu 500,000 zuwa Naira 550,000 a yankin Kudancin Jihar Kaduna da aka fi noman ta a Nijeriya.
Hakan ba ya rasa nasaba da matsalar kwayoyin cutar da suka lahanta mafi yawan cittar da aka noma a 2024, wanda ya yi sanadiyyar karancin irin cittan da kuma hauhawar farashin taki da magunguna da sauran ayyukan noman cittar.
- Hausawa sun yi bikin cika shekara 153 da zama a garin Owerri
- DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’
A 2024, manoman citta a Kudancin Kaduna, inda daya daga cikin inda ake samar da mafi ingancin citta a duniya suka gamu da mummunan ibtila’in da ya lalata musu citta, inda wata kwayar cutar fungus ta halaka mafi yawan amfanin gonakinsu, wanda ya haifar da asarar biliyoyin Naira.
Manoman da suka dogara kacokan a kan noman citta a matsayin babban hanyar samun kudin shiga, sun shiga cikin halin zulumi da ya kai ga yawancinsu sun bar gonakinsu ba tare da noman citta ba, yayin da da dama daga cikinsu suka koma noman shinkafa da wake da gero da kurkur da dankalin Turawa da kuma masara don rage asarar da suka yi.
Michael John, wani manomin citta daga garin Kushe Kowi da ke Karamar Hukumar Kagarko, ya bayyana halin da ya shiga a lokacin bullar cutar.
Ya ce, “kafin wannan cutar, nakan noma buhu 350 na citta kowace shekara. Amma tun bayan bullar cutar, na daina noman citta gaba daya.
Cutar ta lalata jarina, kuma ba ni da kudin da zan sake farawa. Farashin irin citta a yanzu ya sa ba zan iya komawa noman ba.”
Ya bayyana cewa, shekaru da dama da suka gabata, al’ummarsu kan noma doya ce da gyada.
“Amma daga baya sun mayar da hankali a kan noman citta kawai. Sai dai wannan matakin da suka dauka ya haifar musu da matsalar karyewar tattalin arziki.
“Mun rasa jarinmu, yanzu kuma muna fama da talauci,” in ji shi.
Ya kara da cewa, bai taba samun wani tallafi daga gwamnati ko rancen kudi don tallafa wa harkar noman citta ba, inda ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka wa manoman karkara irinsa, ganin yadda farashin Irin da na taki da magungunan kwari da na sufuri ke kara tsananta.
Illar cutar ta fungus da tsadar
Irin sun haifar da raguwar cittan da ake samarwa daga Kudancin Kaduna.
Wasu ’yan kasuwar citta a garin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a sun bayyana halin da ake ciki a sanadiyyar rashin isasshiyar cittar a yankin.
“A baya, daga watan Nuwamba zuwa Janairu, muna iya jigilar motocin tirela sama da 200 na citta kowane mako daga Kudancin Kaduna,” in ji Babangida Abubakar, wani mai harkar citta a Kafanchan.
“A bana, sai da ƙyar muke iya fita da tireloli biyu a mako. Wannan saboda yadda manoma da yawa ba su samu damar noman cittar ba ne sosai,’’ in ji shi Rebecca Yakubu, wata ‘yar kasuwa, ta bayyana kaduwarta game da karancin cittar, ta ce, “karancin citta ya sa farashinta ya yi tsada sosai.’’
“Kodayake ga wadanda ke da cittar da za su sayar, suna samun amfani sosai, amma idan manoma suka ci gaba da barin noman citta, za mu iya fuskantar rugujewar kasuwar citta a Kudancin Kaduna baki daya.”
Kira ga Gwamnati
Yusuf Danjuma, wani masanin aikin gona a Kudancin Kaduna, ya yi kira ga gwamnati da ta shiga lamarin don magance wannan matsalar.
Ya ba da shawarar kafa gonakin gwaji don samar da iri mai inganci da za a rarraba ga manoma cikin sauki.
“Dole ne mu nemi mafita a kai,” in ji Danjuma.
“Ya kamata gwamnati ta kafa gonakin gwaji a cikin al’ummomin da ke noman cittar.
“Wannan zai sake dawo da amincin ga manoma da karfafa su komawa ga noman citta.”
Ya kuma jaddada muhimmancin horar da manoma kan gano da kuma magance cututtuka domin guje wa sake faruwar lamarin nan gaba.
Gudunmawar kungiyoyi da taimakekeniya
Haka kuma, manoma da dama sun yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da gwamnatoci da su samar da iri mai rahusa tare da tallafa musu da rance mai saukin biya don ci gaba da noman.
Wannan zai rage tsadar sake fara noman da ya zama babban cikas ga yawancin manoman.
Yayin da ake fuskantar wannan matsalar, hanya guda da za a iya bi don ceto harkar noman citta a Kudancin Kaduna ita ce hadin kai da hadakar duk masu ruwa da tsaki, wanda zai taimaka wajen dawo da martabar yankin a matsayin babbar cibiyar noma da samar da citta mai inganci.