Dalilin da farashin man fetur zai ci gaba da hauhawa — IPMAN

Idan kudin sufurin dauko man fetur ya hau to dole ne masu gidajen man su kara kudin man fetur.

Dalilin da farashin man fetur zai ci gaba da hauhawa — IPMAN

An ƙara farashin man fetur a Najeriya

Kungiyar Dillalan Man Fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN), ta ce farashin man fetur zai ci gaba da karuwa muddin dalar Amurka ta tashi a kasuwar canji, amma kwararru a fannin tattalin arziki na cewa akwai mafita.

Shugaban IPMAN na kasa Chinedu Okworonkwo ne ya bayyana haka a wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa, inda ya ce kungiyar za ta kara kudin man fetur nan ba da jimawa ba a bisa dalilin tashin farashin dalar Amurka a kasuwar canji.

Chinedu ya ce ya lura cewa farashin man zai ci gaba da hauhawa idan dala ta ci gaba da tashi a kasuwar hada hadar kudi.

A nashi nazarin, mataimakin shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Abubakar Maigandi Dakingari, ya yi karin hasken kan bayanan shugaban kungiyar cewa su kansu ’yan kasuwar mai masu zaman kansu suna cikin wani yanayi domin suna dauko mai amma babu ciniki saboda tsadar sa.

Maigandi ya ce abin ya zama abin tausayi musamman ma a yankin Arewacin Najeriya inda yawancin gidajen man a rufe suke saboda babu kasuwa.

Maigandi ya ce abin ya shafe su saboda ba sa samun kudin biyan ma’aikatansu balle su biya bukatunsu na yau da kullum.

A nashi nazarin, kwararre a fannin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati ya ce dama dole a samu irin wannan yanayi muddun kaya sun fi masu son kayan yawa a kasuwa, amma idan kaya sun yi yawa a kasuwa kuma babu mai saye farashin yana iya sauka.

Mikati ya ce kasuwar daban ta ke a harkar man fetur domin hanyar samo man yana taka rawa a kasuwar ta.

Mikati ya ce idan kudin sufurin dauko man fetur ya hau to dole ne masu gidajen man su kara kudin man fetur domin suna amfani ne da alkaluman da suke samu a lokacin da suka samo man.

Mikati ya ce ana amfani ne da kudaden ketare wajen samo man fetur kuma farashin kara tsada ya ke yi.

Shi ma Kwararre a fanin kasuwanci da hadahadar kudi, Dokta Ali Abdullahi na Jami’ar Kashere, ya ce cire hannu a tallafin mai da gwamnati ta yi shi ne ya sa farashin mai zai zama daidai da farashin kayayyaki a kasuwa, kuma duk kasashe irin su Saudiyya da sauran su suna sayan man fetur da tsada.

Ali ya ce Hukumar Fetur ta Duniya OPEC ta kawo wani yanayi na rage yawan man fetur da ake sayar wa a kasuwanin duniya, wanda ya sa farashin gangan danyen man fetur ya tashi daga dallar Amurka 70 zuwa dallar Amurka 90, saboda haka farashin ya tashi sosai.

Ali ya ce mu ne muka jawo wa kan mu wannan tsada na man fetur, domin ba a ma tace man a nan gida Najeriya, saidai mu bada danyen man, sannan mu tafi mu sayo wanda aka tace mu shigo da shi gida Najeriya, saboda haka yadda muka sayo shi da tsada dole ne mu sayar da shi da tsada.

Ali ya ce akwai matsalar canjin kudi na Naira da Dala (RFES) wato Regulated Foreign Exchange System a turance wanda wani tsari ne da gwamnati ke taimaka wa Naira domin kar darajar ta ta fadi.

“Amma kuma an yi wasa da wannan wajen, sai gwamnati ta ce ba za ta ci gaba da tallafa wa Naira ba kuma, kasuwa ta yi halin ta, idan an samu dala da sauki, ba a sayar da kayan da sauki, sai kuma a sayar da kayan da tsada saboda a samu karin riba.

Ali ya ce “wasu kalilan sun yi amfani da wannan wajen kan azurta kawunansu.”

Shi kuwa, mataimakin shugaban Kungiyar IPMAN ta kasa Abubakar Maigandi Dakingari ya ba da shawarar mafita.

Ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta gyara matatun man fetur na Najeriya domin su fara aiki a wannan shekara, baya ga haka kuma a kawo wani tsari na amafani da wasu abubuwa daban-daban ba tare da an yi dogaro da man fetur ba, “wannan shi ne kadai mafita a yanzu.”