Dalilin da FIFA ta dakatar da Al-Nassr daga sayen sabbin ’yan wasa

Al-Nassr ta yi wa Ahmed Musa alkawarin biyan shi karin wasu kudade a lokacin da yake kungiyar.

Dalilin da FIFA ta dakatar da Al-Nassr daga sayen sabbin ’yan wasa
Dalilin da FIFA ta dakatar da Al-Nassr daga sayen sabbin ’yan wasa

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta dakatar da kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr daga sayen sabbin ’yan wasa.

FIFA ta dauki matakin ne yayin da ta ce har sai Al-Nassr ta biya bashin da ke kanta game da cinikin dan wasan gaba na Najeriya, Ahmed Musa wanda kungiyar ta saya daga Leicester City mai doka Firimiya a wancan lokaci.

Al-Nassr mai doka gasar Pro Lig a Saudiyya, bayanai sun ce ta gaza biyan wasu sauran kudaden yarjejeniyar cinikin Kyaftin din na Najeriya da ta saya daga Leicester City a shekarar 2018, wadanda suka kai yuro dubu 390.

Bayanai na cewa, a kunshin yarjejeniyar sayen Kyaftin din na Super Eagles, Al-Nassr za ta biya shi karin wasu kudade doriya a kan albashinssa da alawus muddin ya yi bajintar da za ta daga darajar kungiyar.

Hakan kuwa ce ta faru domin a lokacin dai Al-Nassr ce ta lashe babbar gasar ta Saudi Pro Lig, wanda Ahmed Musa na daya daga cikin zaratan ’yan wasa da suka rika ruwan kwallaye a ragar abokan karawar kungiyar.

Wannan ne dai batun da FIFA ke cewa dole sai Al-Nassr ta biya Leicester City kudaden gabanin iya sayen wani dan wasa.

Al-Nassr wadda sunanta ya karade duniya bayan cinikin Cristiano Ronaldo a bara, wannan hukuncin na FIFA na nuna cewa dole ta dakata da shirinta na yunkurin sayen Hakim Ziyech daga Chelsea da bayanai ke cewa tana shirin saka makuden kudade don kawo shi Riyadh.

Sai dai FIFA ta ce haramcin sayen ‘yan wasan kan Al-Nassr zai gushe da zarar kungiyar ta mutunta umarnin biyan kudaden ga Leicester City.

Dan wasa na baya-bayan nan da Al-Nassr ta saya shi ne Marcelo Brozovic dan Croatia daga kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan mai doka gasar Seria A a Italiya.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume