Dalilin da Gwamnatin Tinubu ta ci gaba da biyan tallafin man fetur — PENGASSAN
Farashin man a kasuwar duniya ya tashin gwauron zabi sannan farashin dala na ci gaba da hauhawa.
Kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas a Najeriya PENGASSAN ta ce har zuwa yanzu Gwamnatin Tarayya na ci gaba da biyan kudaden tallafin man fetur ga manyan dillalansa.
PENGASSAN ta ce gwamnatin na biyan tallafin ne duk kuwa da ikirarin da ta yi na janye wannan tallafi a hukumance tun cikin watan Mayun da ya gabata.
- Ƙaruwar juyin mulki ya jefa Nahiyar Afirka a tsaka-mai-wuya —Masana
- Hezbollah ta shiga yaki da Isra’ila don goyon bayan Falasdinawa
Binciken Aminiya ya gano cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe naira biliyan 169.4 a watan Agusta wajen biyan tallafin man.
Gwamnatin ta biyan kudaden ne domin tabbatar da ganin farashin litar man fetur din bai haura Naira 620.
Tun kafin yanzu, wasu na ganin cewa dawowar tallafin ya zama babu makawa, ganin yadda farashin litar man bai sauya ba, duk da cewa farashin gangar danyen mai a kasuwa duniya ya haura Dala 95.
Wata takarda da muka yi kicibus da ita ta Hukumar Rabon Kudaden Gwamnati (FAAC) ta nuna a watan Agusta, kamfanin gas na kasa (NLNG) ya biya Gwamnatin Tarayya ribar Dala Miliyan 275 ta hannun kamfanin NNPCL.
Daga cikin kudaden NNPCL ya kashse Dala miliyan 220, kimanin Naira biliyan 169.4 wajen biyan tallafin man fetur, ya rike ragowar Dala miliyan 55, ba bisa ka’ida ba.
Takardar FAAC din ta nuna cewa an dawo da biyan tallafin mai kuma kamfanin NNPC na amfani da ribar da aka samu daga NLNG wajen biyan tallafin.
Ana iya tuna cewa, da yake jawabi bayan shan rantsuwar karbar akalar jagorancin kasar a watan Mayu, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur, lamarin da ya sanya farashinsa ya tashi daga N197 zuwa N615 da har a wasu wuraren ya kai N620 duk lita.
Sai dai shugaban kungiyar PENGASSAN, Festus Osifo wanda kuma shi ne shugaban kungiyar kwadago ta TUC yayin hirarsa da gidan talabijin na Channels, ya ce akwai bukatar gwamnati ta yi bayani game da tallafin da ta ke sanyawa a bangaren man wanda ya hana shi kai wa kololuwa duk da yadda ya tashi a kasuwannin Duniya.
Shugaban na PENGASSAN ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na daukar matakin zuba tallafin man ne don dakile hauhawar farashinsa, dalilin da ya sanya ta zuba kudaden ga ’yan kasuwar da ke hada-hadar man.
A cewar Mista Osifo, a lokacin da Gwamnatin Tarayyar ta sanar da janye tallafin man fetur, farashin duk ganga guda a kasuwannin duniya na kan dala 80 ne, yayin da a yanzu farashin duk ganga guda ke kaiwa dala 93 zuwa 94 amma farashin man bai sauya a Najeriya ba.
Haka kuma, Mista Osifo ya alakanta hauhawar farashin dala a kasuwar canji na daga cikin dalilan da a dole sai an ci gaba da biyan tallafin matuƙar ana son farashin ya tsaya a inda yake a yanzu.
Kungiyoyin kwadago na TUC da takwararta NLC sun gudanar da wata kakkarfar zanga-zanga hade da yajin aikin kasa baki daya don matsa lamba ga Gwamnatin Tarayyar wajen ganin ta lalubo mafita ga matsin da ‘yan kasar ke ciki bayan matakin janye tallafin a watan Mayu.
Bayan matakin Shugaba Tinubu na janye tallafin man na fetur, kamfanin mai na kasa NNPCL ya bukaci gidajen man da ke karkashinsa su rika sayar da duk lita guda kan farashin 480 zuwa 570.
Alkalumma sun nuna cewa wannan kari ne na kashi 200 idan an kwatanta da farashin da sabuwar gwamnatin ta tarar da shi na kasa da naira 200, amma kuma kasa da wata guda aka sake sauya farashin zuwa naira 617 a sassan kasar.