Dalilin da Hukumar Tace Finafinai ta kama Tubeless
Su Tubeless sun tayar da hatsaniya har da barazanar dukan jami’an tsaron da suka je wurin.
Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ta ce karya ka’idojinta da fitaccen mai daukar hoton nan, Nasiru Rabiu Tubeless ya yi ne ya sanya ta kama shi, tare gurfanar da shi a gaban kotu.
A daren Alhamis ne dai kace-nace ya karade soshiyal midiya, bayan bullar rahoton kama Tubeless din ba tare da wani bayani daga hukumar ba.
- Kotun Ƙoli ta tabbatar wa Farouk Lawan ɗaurin shekaru biyar
- Dole Isra’ila ta dakatar da kisan kiyashi a Gaza — Kotun Duniya
Yayin tattaunawarsa da Aminiya ta wayar tarho, kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya ce Tubeless ya bijire wa umarnin hukumar, tare da yin biris da gargadin da ta buga a wurin sana’arsa da ya dakatar da ayyukansa har sai ya yi rajistar.
“A jiya ne bayan samun labarin shi da sauran abokan sana’arsa da ke wurin suka yage takardun dakatarwar da muka manna a shagunan nasu, sannan suka ci gaba da gudanar da sana’o’insu.
“Da jami’anmu suka je sai su [Tubeless] suka tayar da hatsaniya har da barazanar dukan jami’an tsaron da suka je wurin.
“Hakan ya sa su kuma suka yi awon gaba da shi, kuma har ma mun gurfanar da shi a gaban kotu,” in ji Kakakin.
Idan za a iya tunawa dai a shekarar 2023 da ta gabata ce Shugaban Hukumar Tace Finafinan Abba Almustapha, ya bai wa dukkanin masu daukar hoto da sauran ’ya’yan masana’antar Kannywood da masu tura finafinai da wakoki da ake kira ’yan downloading umarnin yin rajista da hukumar, domin tantance su, ko kuma a rufe musu wuraren sana’a.
Wannan umarni dai ya tayar da ƙura matuƙa, inda wasu daga ciki suka nuna turjiya, har ta kai hukumar ta dakatar da wasu daga cikinsu, musamman ma taurarin Kannywood.