Dalilin da jirgin Titan ya tarwatse da mutum 5 a karkashin teku

Mutanen biyar sun tafi yawon bude karkashin teku.

Dalilin da jirgin Titan ya tarwatse da mutum 5 a karkashin teku

Rundunar jami’an tsaron gabar ruwa ta Amurka, ta ce an gano ragowar tarkacen karamin jirgin ruwan nan na Titan da ya yi nutso zuwa karkashin teku.

A cewar rundunar, binciken kwararru ya tabbatar da cewar, karfin igiyar karkashin ruwan ce tarwatsa karamin jirgin da karfin tsiya, lamarin da ya yi sanadin kashe baki dayan mutane 5 da ke cikinsa.

Jagoran aikin neman jirgin na Titan da ya bace Rear Admiral John Mauger ne ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Juma’a.

Ya bayyana cewar, na’urar bincikensu ta fara gano ragowar tarkacen jirgin ne da safiyar ranar Alhamis, a can kasan tekun na Atlantic da nisan kilomita 4, kuma akwai tazarar akalla kafa dubu 1 da 600, tsakanin inda jirgin nutson ya tarwatse da kuma ragowar katafaren jirgin Titanic da suka yi nufin kai wa gareshi, wanda ya nutse fiye da shekaru 110 da suka gabata.

Musayar bayanai ta katse tsakanin jirgin Titan da jami’ai ne, bayan tafiyar da ya fara zuwa karkashin tekun Atlantic da kimanin sa’a 1 da mintuna 45 a ranar Lahadin da ta gabata da safe.

Bayan shafe fiye da kwanaki uku ana ta lalube ne kuma, aka gano muhimman sassa guda biyar na jirgin karkashin ruwan, ciki har da jelarsa da kuma bangarori biyu da ke daidaita karfin igiyar ruwa da nauyinsa da jirgin na Titan ke ratsawa.

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano

Ɗan Gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa

Mutum 38 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama a Kazakhstan