Dalilin da Kamfanin sadarwar EE ya caji jama’a fiye da kima

Kamfanin sadarwa na EE ya ce matsalar na’urace ta janyo aka caji masu hulda da shi kudin da ya wuce kima.  Kamfanin mai samar da hanyoyin sadarwa na wayar salula da kuma intanet zai mayar wa wasu masu mu’amala da shi kudin da aka zare daga lalitarsu a matsayin haraji ba bisa ka’ida ba.Kimanin rabin […]

Dalilin da Kamfanin sadarwar EE ya caji jama’a fiye da kima
Dalilin da Kamfanin sadarwar EE ya caji jama’a fiye da kima

Kamfanin sadarwa na EE ya ce matsalar na’urace ta janyo aka caji masu hulda da shi kudin da ya wuce kima. 

Kamfanin mai samar da hanyoyin sadarwa na wayar salula da kuma intanet zai mayar wa wasu masu mu’amala da shi kudin da aka zare daga lalitarsu a matsayin haraji ba bisa ka’ida ba.
Kimanin rabin kashi daya cikin 100 na masu mu’amala da kamfanin da suka yi tafiya zuwa wasu kasashen da bana Turai ba, kuma suka yi amfani da intanet a tsakanin watan Oktoban 2012 da kuma Oktaban 2014 ne abin ya shafa.
Kamfanin EE ya shaida wa BBC cewa kudin da aka zare daga lalitar mutanen bana kamfanin ba ne, sannan ya dora alhakin matsalar a kan kuskuren na’ura. Kuma ya ce zai biya kowannen daga cikin mutanen daga Fam biyu zuwa Fam 80.
Mai magana da yawun kamfanin, Mista Dabid Nieberg ya ce tuni suka karbo kudin daga inda aka adana su, kuma za a mayar da su ga jama’a nan ba da jimawa ba.
Sai dai kamfanin ya ce ba zai biya mutanen da takardun kudi ba, sai dai ya tura musu kudin ta asusan cinikayyarsu, ko layikan wayoyinsu.
An gano matsalar ce bayan wani daga cikin masu hulda da kamfanin ya gabatar da korafi.