Dalilin da ke haifar da jinkirin gyara wutar Arewa – TCN

Amma kamfanin ya ce yana yin duk mai yiwuwa don ganin an dawo da wutar lantarki a Arewacin Najeriya.

Dalilin da ke haifar da jinkirin gyara wutar Arewa – TCN

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), ya ce matsalar tsaro ce ke haifar da jinkirin gyara layin wutar Apir-Ugaji, wanda ya lalace.

Manajan TCN, Injiniya Abdulaziz Sule, ya bayyana cewa injiniyoyin da ke aikin gyaran suna aiki tare da jami’an tsaro don ganin wuta ta dawo yankin Arewa.

Amma ya ce injiniyoyin suna barin wajen aikin da zarar ƙarfe 6 na yamma ta yi, don tsira da rayukansu.

“Lokacin da layin Shororo-Mando ya samu matsala, hanya ta biyu da ake amfani da ita wajen samar wa yankin Arewa wutar lantarki ita ce layin Ugwaji-Apir.

“Amma abun takaici, wannan layin ma an lalata shi,” in ji Injiniya Sule.

“Yanzu haka, injiniyoyinmu na aiki domin tabbatar da cewa an gyara wannan layi. Amma sai sojoji sun mana rakiya kafin mutanenmu su iya gudanar da aikinsu.”

Injiniya Sule, ya kuma bayyana cewa, idan an kammala gyaran, TCN za ta iya samar wa Arewa wuta tsakanin megawatt 500 zuwa 600.

“Da zarar mun kammala gyaran waɗannan layukan biyu, za mu iya tura megawatt 500 zuwa 600 zuwa yankin Arewa. Wannan shi ne halin da muke ciki a yanzu,” in ji shi.

TCN ya ce yana aiki kafaɗa da kafaɗa da al’ummomin yankin da hukumomin tsaro.

“Mun daɗe muna haɗin gwiwa da manoma da mutanen yankin,” in ji Injiniya Sule.

“Haka kuma, muna bai wa mutane a yankin motocin hawa da wayoyi don idan sun ga wani abu da ya faru a layinmu, su sanar da mu cikin gaggawa.”