Dalilin da lauyoyin Aminu Ado Bayero suka fice daga shari’ar Masarautar Kano

Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta ɗage zaman kotun zuwa ranar 18 wannan wata.

Dalilin da lauyoyin Aminu Ado Bayero suka fice daga shari’ar Masarautar Kano

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero

Lauyoyin da ke wakiltar Sarki Aminu Ado Bayero, sun fice daga shari’ar rikicin Masarautar Kano da ke gudana a babbar kotun Jihar Kano.

Lauyoyin sun ɗauki matakin ne a zaman da kotun ta yi ranar Alhamis, bayan kai ruwa rana tsakanin ɓangarorin da ke shari’a da juna.

A lokacin zama kotun, lauyan Aminu Ado Bayero, Abdul Muhammed SAN, ya fara da shaida wa kotun cewa akwai takardar shaidar da ke tabbatar da cewa sun ɗaukaka ƙara kuma an shigar da bayanan a gaban kotun, inda ya nemi kotun kada ta ci gaba da sauraron shari’ar har sai an saurari ɗaukaka ƙarar da suka yi.

Lauyan ya kuma buƙaci kotun ta ƙara musu lokaci don mayar da martani kan wasu takardu da ya ce an ba su ranar Laraba.

To sai dai ɓangaren masu ƙara sun soki waɗannan buƙatu, inda babban lauyan gwamnatin Kano da majalisar dokokin jihar, Eyitayo Fatogun ya ce babu waɗannan bayanan a kotun.

Fatogun ya shaida wa kotun cewa ba haka ake yi ba, yana mai cewa dokokin babbar kotu sun ce idan kana so ka shigar da wasu bayanai a gaban kotu nema ake yi ba kawai ka kawo wata takarda ba.

Bayan sauraron duka ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta ce buƙatun da lauyan Aminu Ado Bayero ya gabatar ba su da ƙarfin da za su hana ci gaba da sauraron shari’ar don haka ta yi watsi da su, sannan ta bayar da umarnin ci gaba da sauraron shari’ar da ke gaban kotun.

To sai dai wannan hukunci bai yi wa lauyoyin Aminu Ado Bayero daɗi ba, inda Barista Sanusi Musa SAN a madadin duk lauyoyin Aminu Bayero ya miƙe ya shaida wa kotun cewa sun fice daga wannan shari’a, sannan ya ce za su koma su sanar da wanda suke wakilta don ya nemi wanda zai wakilce shi, sannan suka fice daga kotun.

Bayan ficewarsu ne, kuma sai mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta ci gaba da sauraron karar, inda lauyan sarakunan da gwamnatin Kano ta ce ta sauke wato Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye, Hassan Tanko Kyaure ya buƙaci a ƙara masa lokaci don ya yi nazari akan takardun da aka ba su.

Sannan ya kuma buƙaci kotun ta rushe sabuwar Dokar Masarautar Kano ta 2024, amma mai shari’ar ta ce ba zai yiwu a ƙara musu lokaci ba, saboda ta bayar da odar cewa ba za ta ƙara lokaci ba.

Daga ƙarshe Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta ɗage zaman kotun zuwa ranar 18 wannan wata don yin hukunci a kan buƙatun da kowanne ɓangare ya gabatar.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun a ranar 27 ga watan Mayu ne masu ƙarar da suka haɗa da Babban Lauyan Kano, Kakakin Majalisar Dokokin Kano da Majalisar Dokokin Kano ta bakin lauyansu, Ibrahim Isah Wangida suka garzaya kotu.

Masu ƙarar dai na neman kotun ta haramta wa Sarakunan Kano, Bichi, Rano, Karaye, da Gaya waɗanda gwamnatin Kano ta rushe masarautunsu ayyana kansu a matsayin sarakai.

Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Aminu Ado Bayero na Masarautar Kano da Nasiru Ado Bayero na Bichi, da Ibrahim Abubakar II na Karaye da Kabiru Muhammad Inuwa na Rano, da Aliyu Ibrahim Gaya na Gaya.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa