‘Dalilin da Masarautar Nunku ta shekara 40 ba Sarki’
Mai matraba Sarkin Nunku Alhaji Adamu Muhammad Abubakar ya ce rikici da shari’a da aka rika tafkawa a tsakanin haulolin kabilar Mada ne ya sa Masarautar Nunku da ke Karamar Hukumar Akwanga ta kwashe shekara 40 ba tare da Sarki ba. Sarki Adamu Muhammad Abubakar wanda aka nada a matsayin sabon Sarkin Nunku, ya bayyana […]
Mai matraba Sarkin Nunku Alhaji Adamu Muhammad Abubakar ya ce rikici da shari’a da aka rika tafkawa a tsakanin haulolin kabilar Mada ne ya sa Masarautar Nunku da ke Karamar Hukumar Akwanga ta kwashe shekara 40 ba tare da Sarki ba.
Sarki Adamu Muhammad Abubakar wanda aka nada a matsayin sabon Sarkin Nunku, ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya, inda ya ce, “Nunku sunan daya ne daga cikin haulolin kabilar Mada, ba sunan gari ba ne kuma an kafa masarautar ce a 1777.”
Ya ce, Turawa ne suka taso fadar masarautar daga Nunku suka dawo da ita garin Andaha. Ya ce bayan da Sarkin Nunku Musa Kaya II ya rasu a 1976, lokacin mulkin soja na Janar Murtala hammed da Janar Olusegun Obasanjo, sai rikici ya barke a cikin haulolin Mada inda sauran suka ce bai dace haular Nunku kadai ta rika yin sarautar ba, sai dai a zuba ta a faifai, mai rabo ya dauka daga cikin haulolin.
Ya kara da cewa, ana cikin haka ne sai siyasa ta bullo, mutanen Nunku suka bi Jam’iyyar NPN ta Alhaji Shehu Shagari, sannan wadansu daga cikin haulolin suka bi Jam’iyyar UPN ta Cif Obafemi Awolowo sannan Cif Solomon Lar na NPP ya zama Gwamna. Sarkin ya kara da cewa, Cif Solomon Lar ya haddasa rigimar, don ya ce idan ya ci zabe, zai hana yarimomin Nunku gadon sarauta, sai dai a zuba a faifai, mai rabo ya dauka, wato an maida sarautar Mada dimokuradiyya ke nan.
Sarkin ya ce, “Cif Solomon Lar ya ci nasara ya zama Gwamna, dama ana ta rigimar gadon saaruta don lokacin Sarki Nunku ya rasu tun 1976 har zuwa 1979 ba a nada sabon Sarki ba. Sai ya dauki wannan dama ya ce ya yi alkawarin ya mayar da sarautar ta dimokuradiyya, sai ya nada wani dan siyasa mai suna Mista Iliyi Iimi a matsayin sabon Sarkin Nunku, duk da bai gada ba.
Bayan ya rasu, sai ’ya’yan sarautar Nunku suka dauka Gwamna Solomon Lar ya huce, amma da suka ga ba a nada daya daga cikinsu ba, sai suka kai karar Gwamnatin Jihar Filato da Chum Mada (Sarkin Mada) mahaifin Chum Mada na yanzu a kotu. An yi shekaru ana ta tafka shari’a daga kotu zuwa kotu kafin Kotun Klin Najeriya ta yanke hukuncin cewa an zalunci Masarautar Nunku kuma a mayar da sarautar ga masu gadonta ’yan kabilar Njozah.
Ya ce an samu dabaibayi domin gwmanatocin da suka biyo baya tun daga tsohuwar Jihar Filato har zuwa lokacin da aka kafa Jihar Nasarawa sun kasa aiwatar da wannan hukunci na kotu har sai da Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya yi ta maza ya mayar da sarautar Nunku ga ’ya’yan gidan sarautar. Sarkin ya ce, “Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya nada ni Alhaji Adamu Muhammad Abubakar a matsayin Sarki don gadon iyaye da kakanni a matsayin Sarki Mai daraja ta Biyu kuma Sarki na 12 a zuriyar Nzojah. Hakan ya faru ne bayan an kwashe shekara 40 ana takaddama.”
Ya ce da yake Turawa, sun taso Masarautar Nunku zuwa Andaha, lokacin ake shari’a, sai aka ce kada wani ya shiga gidan sarautar, kuma da aka kare shari’ar aka nada shi Sarki, sai mutanen Andaha suka ce ba su yarda Sarki daga haular Nunku ya shiga gidan ba. Don haka aka gina wa Chum Mada gida a Akwanga, shi kuma Chum Mada aka ce ya zauna a garin Nunku. Don haka, yanzu da masarutar Sarkin Nunku da Chum Mada, ba wanda yake zaune a gidan. Sarkin Nunku da na Chum Mada suna da fadoji ne a bangarori daban-daban a Karamar Hukumar Akwanga.
Abin mamaki shi ne, bayan da aka nada Sarkin Nunku Adamu Muhammad Abubakar, ya ziyarci Chum Mada sun gana kuma cikin lumana a tsakanin kabilar Mada.