Dalilin da muka kafa ƙungiyar siyasa ta BAMV — Mohammed Jibo
Mu a Jam’iyyar PDP za mu tabbatar da ganin an yi duk abin da ya kamata.
Aminiya ta tattauna da Daraktan Janar na Ƙungiyar Bala Abdulƙadir Mohammed Vanguard (BAMV) Kwamared Mohammed Abubakar Jibo.
Ya ce, sun samar da ƙungiyar ce domin haɗa kan ’ya’yan Jam’iyyar PDP a ƙasa da nufin kawar da Jam’iyyar APC daga mulki, wanda hakan zai kasance alheri da samar da ci gaban dimokuraɗiyya:
Kwamared me ya jawo hankalinku kuka kafa wannan ƙungiya ta BAMV ?
To abin da ya jawo hankalinmu, muka kafa ko muka ɗauko wannan tafiya ta BAMV shi ne, lura da yadda shugabanci yake a ƙasar nan inda za a zaɓi shugabanni daga baya a tarar suna yin ba-zata wato ba manufar da aka zaɓe su a kai suke aiwatarwa ba.
Don haka muka yanke shawarar kafa wannan ƙungiya ta BAMV don tsayar da shugaba nagari da zai jagoranci jama’a cikin adalci da sanin ya kamata. Kuma yanzu haka muna da rassa a dukkan jihohin ƙasar nan da ƙananan hukumomi 774.
Duk abin ya jiɓanci siyasa, akwai tunanin samar da kuɗi, ta yaya kuke gudanar da wannan tafiya taku?
Gaskiya mu mun ɗauko wannan tafiya ce domin kishi da son ci gaban ƙasa, ba don kuɗi ba. Kuma muna samun ce ta hanyar gudunmawa da mu mambobin muke bayarwa daga aljihunmu.
Wasu za su ce da mutum ya shiga ƙungiyar zai samu kuɗi tunda ƙungiya ce da ke da alaƙa da Gwamnan Jihar Bauchi. Amma ka ce, manufarku ita ce zaɓo mutum nagari, me za ka ce ga masu wannan ra’ayi?
A gaskiya masu tunanin cewa wannan ƙungiya, idan ka shiga za ka samu kuɗi to ba haka ba ne.
Mu mun kafa ƙungiyar ce saboda kishin ƙasa, kuma shi ya sa muka ɗauko Gwamna Bala A. Mohammed a matsayinsa na mai kishin ƙasa.
A zaɓen baya mun neme shi ya fito takara don ya ceci al’ummar Nijeriya ya amince, to shi ne a wannan karo ma muka fito don roƙonsa ya fito takarar shugabancin ƙasa da zarar lokaci ya yi don ceto al’ummar Nijeriya.
A 2023 an ce ku ne kuka saya masa fom ɗin yin takara, ba ka gani a wannan karo zai iya bijire wa kiran naku lura da cewa akwai manyan ’yan takara irin su tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da suka nuna alamun sake tsayawa takara a 2027?
Mu a Jam’iyyar PDP za mu tabbatar da ganin an yi duk abin da ya kamata wajen ganin mun kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya ta hanyar zaɓo jajirtattacen mutum da aka ga kamun ludayinsa tun daga matakin sanata, gwamna har ya kai ga zama Shugaban Ƙasa.
Muna da yaƙinin cewa muddin aka tsayar da wanda yake ba ya da wani tabo to Jam’iyyar PDP za ta sake dawowa mulki a 2027.
Hakan ya sa wannan Ƙungiyar BAMV take neman amincewar Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya tsaya takara a 2027 matuƙar ana son kaiwa ga nasara da son PDP ta dawo mulki.
Yanzu a halin da ake ciki jam’iyyarku ta PDP akwai rarrabuwar kai, kuna ga kafin lokacin za ku iya haɗa kanku don cin zaɓe?
To lallai ina tabbatar maka cewa haɗin kai zai yiwu kafin zuwan lokacin zaɓe.
Domin a jam’iyyarmu ta PDP duk wani ɗan ƙasa mai kishinta ya san halin da ake ciki, don haka haɗa kai a tsakanin ’ya’yan Jam’iyyar PDP ya zama dole don a gudu tare a tsira tare.
In aka duba Jihar Bauchi tana da sauƙin matsalar tsaro, shin a jihar Bauchi za a iya cewa akwai ayyukan raya ƙasa da Gwamnan ke yi wa al’ummarsa da kake ganin in PDP ta tsayar da shi takara zai iya gudanar da irin waɗannan ayyuka in ya zama Shugaban Ƙasa?
Lallai muna da tabbacin in Allah Ya so matuƙar al’ummar Nijeriya suka amince da Gwamna Bala Mohammed a matsayin Shugaban Ƙasa in lokacin ya zo, zai yi fiye da irin ayyukan da yake yi wa Jihar Bauchi, a fannin samar da tsaro, bunƙasa ilimi, aikin gona.
Babu shakka zai taka rawar gani domin in an duba yadda cikin ƙanƙanin lokaci ya shawo kan matsalar da taso kunno kai a Jihar Bauchi.
Wato matsalar yin garkuwa da mutane, abin sai godiya inda a yanzu Jihar Bauchi na cikin jihohin da ke da kwanciyar hankali a ƙasar nan.