Dalilin da muka maƙale a Kudu duk da matsin tattalin arziki — ’Yan Arewa
Mun kara kuɗin wankin takalmi daga naira 50 zuwa naira 100.
A daidai lokacin da ake ci gaba da kokawa da yadda ake fama da tsadar rauyuwa a Nijeriya, a Jihar Legas da Ogun da sauran wasu jihohi na Kudu ma haka lamarin yake.
Wannan ya sa Aminiya ta nemi jin halin da ’yan Arewa mazauna Kurmi suke ciki.
- Taurarin Zamani: Mustapha Ahmad (Alhaji Sheshe)
- Gwamnati ta yi ƙarin haske kan fargabar rasa ayyuka yayin aiwatar da Rahoton Oronsaye
Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu, mazaunin jihar Legas ne kuma mai fashin baki a al’amuran yau da kullum, ya shaida wa Aminiya cewa, mutanen da ke zaune a Kudancin Nijeriya sun fi kokawa da halin da ake ciki na tsadar rayuwa fiye da takwarorinsu na Arewa, duk da cewa a Arewa an fi shan wahalhalu duba da wasu dalilai, amma mazauna kudu sun fi kokawa domin su ba su saba da irin wannan yanayi na karancin kayayyakin masarufi ko kuma hada-hadarsu ba.
“Lokacin da muke ciki sai dai mu ce AlhamdulilLah, domin babu abun da kuɗinsa bai ninninka ba, hatta sabulun wanka, ba ma sabulu ba, hatta garin kwaki wanda talaka zai zuba ruwa ya jika ya sha ko babu sukari ya sanya wani abu a cikinsa, kwanon awonsa da a baya Naira 350 ne, yanzu ya koma Naira 2,000.
“Mu ’yan Arewa da muke zaune a Kurmi ba mu saba da wannan yanayi na kunci ba. Shi ya sa za ka ga an fi kokawa a nan fiye da Arewa.
“Kuma a gaskiya adadin mutane da suka shiga halin neman taimako sai karuwa yake, sannan kayan masarufin sai tsada suke dada yi, mabaratanmu na Arewa sai dada kwararowa suke yi nan Kudu.”
Muhammad Fayama Jarimi da ke zaune a Karar Basi a Jihar Ogun, wanda ke harkar sufurin motocin bas da ke jigila tsakanin Legas da Ogun ya shaida wa Aminiya cewa, a yanzu masu yin harkar sufuri suna cikin wani hali duba da yanayin tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.
“Yanzu haka tayar motar da muke saya a ’yan watannin baya Naira 40,000 yanzu sai mun saka Naira 85,000, haka in ka zo juyen bakin mai ana maganar Naira 18,000 zuwa a Naira 20,000 a lita biyar ko shida.
“Sannan ga tsadar man fetur, wannan ne ya sanya harkar sufurin a yanzu duk sai hakuri, domin kayan sun yi tsada idan kuma ka kara kudi sai a rasa masu shiga motar,” inji shi.
Haka shi ma Muhammad Warshu Matankari, wani dan kasuwa da ke hada-hadar kayan abinci a kasuwar Ilepo a Jihar Legas, ya shaida wa Aminiya cewa, zuwa yanzu mutane sun kai wuya, a yanayi na kuncin rayuwa sakamakon tsadar kayayyakin masarufi.
“Domin a yanzu duk wani majalisi ko wajen taron jama’a idan ka zauna za ka ji hirar da ake tattaunawa ba ta wuce ta tsadar kayayyakin masarufi ba.
“Domin yanzu muna wani yanayi ne da yau za ka sayi abu Naira 1,000 gobe ya koma Naira 2,000 ko N3,000.
“Yanzu a Legas mutane tattaki a kasa zuwa wajen aiki ko kasuwanci suke yi a maimakon su hau babur na adaidaita sahu ko motar haya, wanda hakan ke sa ma’aikata da yawa makara zuwa wajen aiki, yayin da wasu ke zuwa wajen aikin a gajiye.”
Shehu Usman, dan asalin garin Zariya ne da ke ci-rani a Legas, ya shaida wa Aminiya cewa, a baya idan ya zo Legas yana samun babur ne na a Acaba ya tuka yana biyan mai babur, yana samun abin da zai rufa wa kansa asiri, amma yanzu an hana tukin babur na acaba a wurare da dama a jihar, hakan ne ya sanya ya koma yin aikin kamfani.
Malam Umar Warawa magidanci ne da ke zuwa ci-rani garin Abeokuta daga Jihar Kano, ya shaida wa Aminiya cewa, ya kai kimanin mako hudu da ya dawo daga Arewa, amma bai samu babur na acaba da zai yi aiki ba. “…haka muke ta fama da rashin aiki, da na ga haka sai na koma sana’ar hakar rijiya, tunda yanzu rani yayi, babu wadatar ruwa.
“Sai dai abin da muke samu ba zai ishe mu sayen abincin sayarwa ba, saboda tsada.
“Sai dai mu hada wuta mu dafa da kanmu. Domin dan kudin aikin sai ya kare a abincin da za mu saya, mu ci.” in ji shi.
Sai dai duk da wadannn matsaloli babu wanda ya yi sha’awar komawa gida Arewa duk da matsanancin halin rayuwa da ake fama da shi kasa sakamakon matsin tattalin arzikin da kowa yake kokawa.
A Kalaba da ke Kuros Riba kuwa, a daya daga tashar motocin garin wakilinmu ya tarar da Alhaji Ya’u Isma’il Girei, shugaban daya daga cikin kamfanonin motocin da ke jigilar fasinja daga Kalaba zuwa Jos.
Ya ce, “Batun tsadar rayuwa akwai ta amma ba ta tsananta ba da har ’yan Arewa za su fara komawa gida, duk da cewa akalla shayin da mutum ma zai sha sai ya kashe mafi karanci Naira700 a nan.
“Duk da haka mun fi ’yan uwanmu na Arewa samun saukin rayuwa,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “yawanci yanzu mutane sako suke bayarwa a kai musu gida Arewa, idan tafiyar ba ta zama dole ba.”
Abdurrahman Bello Suleiman wani fasinja ne da wakilinmu na yi kicibis da shi a tashar yana shirin tafiya Jos, ya ce ziyara ce za ta kai shi Jos, amma zai dawo inda ya ce ya fi son zama a Kalaba.
A birnin Ibadan wasu daga cikin al’ummar Hausawa masu kananan sana’o’i a sun koka da irin yadda tsadar rayuwa ta shafi harkokin kasuwancinsu.
Aminiya ta samu zantawa da irin wadannan mutane da suke dora kayan da suke sayarwa a kawunansu suna yawon talla a unguwanni daban-daban na cikin gari.
Sarkin ’yan guga Ibrahim Muhammed cewa ya yi, “muna sayo tsofaffin tayoyin mota ne da muke yankawa da dinkewa da sarrafa su zuwa gugan janyo ruwan rijiya.
“Akwai (belt) wato igiyar daurawa a jikin guga da muke yawon talla ga mabukata a cikin gari.
“Farashin yadda muke sayo wadannan kayan aiki ya tashi sama a dalilin karanci da ya haifar da tsadar su. Muna sayar da guga daya a kan Naira 300 zuwa 500. Ita kuma igiyar muna sayar da ita a kan Naira 150 zuwa 200 ne.
“Mabukata suna yi mana tayi yadda suka ga dama domin babu takamaiman farashin.
“Yanzu da matsalar tsadar rayuwa ta shafi gidan kowa sai lamarin ya birkice mana saboda irin yadda muke yin doguwar tafiya a kasa na tsawon kilomita 20 zuwa da dawowa ba tare da mun samu masu saya ba.
“Mu ma muna rokon gwamnati ta taimaka wajen kawo karshen matsalar tsadar rayuwa.”
Shi kuwa Isa Salihu da yake yawon sayar da takalma cewa ya yi, “ka ga yawan takalman da nake yawon talla sun kai guda 20 da farashinsu ya fara daga naira 700 zuwa dubu daya da 300. Amma Wallahi sai in shafe yini daya ban samu mai saye ba.
“Ka ga zan cinye dan jarin da ke hannuma wajen neman abinci da sauran bukatu ke nan.
“Haka muke jajircewa muna yin wannan sana’am, inda wani lokacin kuma muke yin godiya ga Allah saboda budewar kasuwa.”
Wani mai sana’ar sayar da yadin sutura mai suna Tanko Yaro ya ce, “duk da yake akwai tsadar rayuwa amma a gaskiya ni dai sai godiya ga Allah domin ina yin cinikin samun abun da zan biya bukata.”
Wasu masu sana’ar gyaran takalmi (sobata) sun yi bayanin cewa, “mun kara kuɗin wankin takalmi daga naira 50 zuwa naira 100, amma da kyar mutane suke biyan sabon karin kudin.
“Mun fi samun alheri ga dinkin takalmi fiye da wanki.”
Ta fannin dafaffen kayan abinci, Aminiya ta jiyo bayanai daga masu tallan soyayyen kifi da doya da masu teburan sayar da shayi da burodi da kwai da suke cewa tun da muna sayo danyen kaya da tsada ne, to mu ma mun yi karin yadda muke sayarwa ga jama’a, amma muna yin la’akari da irin rayuwar mutanenmu wajen yin sauki.
Bincike ya nuna cewa, a halin da ake ciki kudin shan kofin shayi babu madara da bonbita ko Lipton ya tashi zuwa naira 100 ne idan aka haɗa da karamin burodi zai kama naira 200.
Idan kuwa aka hada da madara da bonbita ko Lipton da burodin Naira 200 da soyayyen kwai zai kama Naira dubu daya da 200 da mutum daya zai sha domin karya kumallo ba tare da ya koshi ba.