‘Dalilin da muka shirya addu’o’i ga marigayi Jagaban’

A tarihi ba mu taɓa samun irinsa da yake nuna mana ƙauna da soyayya ba.

‘Dalilin da muka shirya addu’o’i ga marigayi Jagaban’

Kungiyar ’Yan Arewa Magoya Bayan Jami’yyar APC a Jihar Oyo, sun yi addu’ar fidda’u ta kwana 40 da rasuwar ɗan Majalisar Wakilai Hoarabul Musiliu Olaide Adewale Akinremi da ake yi wa laƙabi da Jagaban.

Ƙungiyar ta ce ta shirya yi masa addu’a ce a ranar Litinin da ta gabata saboda gudunmawar da ya bayar ga ci gaban al’ummar Hausawa a Unguwar Sabo da ke ƙarƙashin mazaɓarsa a Ibadan Babban Birnin Jihar Oyo.

Jagoran ’yan Arewa Magoya Bayan Jam’iyyar APC a Kudu maso Yamma, Marafan Ibadan Alhaji Audu Lawal da Shugaban Ƙungiyar a Jihar Oyo, Alhaji Bashir Luƙman Maiborno da Shugaban Ƙungiyar a Ƙaramar Hukumar Ibadan ta Arewa Alhaji Murtala, Ahmad Kofa ne suka jagoranci yin addu’o’in, inda malaman addinin Musulunci suka yi saukar Alƙur’ani sau biyu don roƙon Allah Ya yi masa rahama Ya gafarta masa.

Zuriyar marigayi Musiliu Akinremi da wasu ’ya’yan Jam’yyar APC a Jihar Oyo suna daga cikin mahalarta addu’ar da aka gudanar a babban ofishin ƙungiyar da ke Unguwar Sabo mazaunin Hausawa a Ibadan.

Da yake yi wa Aminiya bayanin dalilin shirya wannan addu’ar, Alhaji Bashir Luƙman Maiborno ya ce, “Al’ummar Arewa mazauna Unguwar Sabo sun yi babban rashin kan rasuwar ɗan Majalisar Wakilan wanda a tarihi ba mu taɓa samun irinsa da yake nuna mana ƙauna da soyayya ba.

“A lokacin da yake raye shi ne ya yi wa babban masallacin gareji kwaskwarima kuma ya samar da wutar lantarki ta sola ya gina rijiyoyin burtsatse a cikin wannan unguwa.”

Shi ma Alhaji Murtala Ahmad Kofa da Jagorar Mata ’Yan Arewa Magoya Bayan Jam’iyyar APC a Jihar Oyo, Hajiya Ladidi Usman cewa suka yi a tarihin ’yan Majalisar Tarayya da Sanatoci da suka wakilci wannan mazaɓa a baya ba su taɓa samun irin marigay Musiliu ba, kuma ba za su manta da irin gudunmawar da ya bayar kafin rasuwarsa ba.

“Ya yi mana alƙawarin sama wa ’ya’yanmu guraben karatu a manyan makarantu wanda ’yan majalisar baya ba su taɓa yi mana irin wannan alƙawari ba. Saboda haka muke juyayin rasuwarsa ba za mu taɓa mantawa da shi ba,” in ji su.

Aminiya ta gano cewa addu’ar fidda’un da aka yi, ta zo daidai da ranar da aka bayar da sanarwar rasuwar Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Oyo Cif Ajiboye Omodewu wanda ya kwanta dama a ƙasar Amurka bayan gajeruwar jinya.

Sun kashe yaron da suka sace bayan neman fansar N25m

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT