Dalilin da muka tafi Kotun Duniya kan kisan kare-dangin da aka yi wa Fulani a Taraba – Sale Bayeri

Aminiya: Mun samu labarin cewa kungiyarku ta kai kara zuwa kotu kan abubuwan da suka faru da Fulani kwanakin baya a karamar Hukumar Mambila da ke Jihar Taraba, mene ne gaskiyar wannan labari? Sale Bayeri: Kamar yadda kuka samu labari, kan ta’addancin da aka yi wa al’ummar Fulani a karamar Hukumar Mambila da ke Jihar […]

Dalilin da muka tafi Kotun Duniya kan kisan kare-dangin da aka yi wa Fulani a Taraba – Sale Bayeri

Aminiya: Mun samu labarin cewa kungiyarku ta kai kara zuwa kotu kan abubuwan da suka faru da Fulani kwanakin baya a karamar Hukumar Mambila da ke Jihar Taraba, mene ne gaskiyar wannan labari?

Sale Bayeri: Kamar yadda kuka samu labari, kan ta’addancin da aka yi wa al’ummar Fulani a karamar Hukumar Mambila da ke Jihar Taraba, kwanakin baya.  A karamar hukumar akwai wata kabila da ake kira Mambila, ’ya’yan wannan kabila ne suka auka wa Fulani a wuraren da suke zaune a yankin. A harin da aka kai wa mutanenmu an kone mana gidaje da rugage wadanda har zuwa yanzu ba mu gama tantance yawansu ba. A wadannan hare-hare an kashe mana mutum 937 kuma an kashe mana shanu sama da dubu 27.

Ganin an yi mana wannan abu ba tare da wani laifi ba, ba ce an yi wani ta’adi ko wani fada ba, haka kawai aka kawo mana wadannan hare-hare domin a fitar da al’ummar Fulani daga gonakin da suka saya ko suka gada kusan shekara 60 da suka gabata.

Kuma ganin cewa a cikin kudin tsarin mulkin Najeriya, babu inda aka ce a yi irin wannan abu, don haka muka ga cewa ba za mu ci gaba da barin mutanenmu suna daukar doka a hannunsu ba. Saboda mun gano cewa wannan zamani ba zamanin da za a rika daukar doka a hannu ba ne, don haka wannan kungiya wata biyu da suka gabata ta tafi kotuna uku ta kai kara kan wannan lamari. Na daya mun shigar da kara a Kotun Afirka ta Yamma, muna neman hakkin wadannan mutane namu daga gwamnatin Jihar Taraba da Gwamnatin Tarayya, wadda take da hakkin kare rayukan al’ummar Najeriya. Domin mun sani hakkin Gwamnatin Tarayya ce da gwamnatin Jihar Taraba su tabbatar Fulani suna walwala da samun kariya a jihar da kasa baki daya.

Bayan haka mun shigar da wata karar na neman a dakatar da gwamnatin Jihar Taraba daga kafa dokar hana kiwo a jihar a Babbar Kotun Jihar Taraba, domin wannan doka ta tauye ’yancina Fulani na gudanar da sana’arsu a jihar. Haka kuma mun kai kara a gaban Kotun Duniya don neman hakkinmu kan wannan kisan gilla da kone-konen gidaje da dabbobi da aka yi wa al’ummar Fulani a karamar Hukumar Mambila. Tuni lauyoyinmu sun je gaban wannan kotu sun gabatar da takardun kararmu.

Mun tattara adadin rayukan da muka rasa da hotuna da muryoyin mutanen da wannan ta’adanci ya rutsa da su da shaidun da wannan lamari ya faru a kan idonsu duk lauyoyinmu sun gabatar wa kotun.

Aminiya: Daga lokacin da wannan lamari ya faru zuwa yanzu ko akwai wani tallafi da aka yi wadanda lamarin ya shafa?

Sale Bayeri: A lokacin da muka fara maganar shigar da kararrakin an fara yin wasu abubuwa amma mu ba mu gamsu ba, musamman gwamnatin Jihar Taraba. Domin sai da muka fara koke-koke a gidajen rediyo da jaridu cewa gwamnatin Jihar Taraba da Gwamnatin Tarayya ba su yi komai ba, da aka ji cewa muna ta tarurruka domin daukar matakan shari’a, daga nan ne Gwamnatin Tarayya ta fara tura mutane domin su je su ga abin da ya faru. A lokacin aka dan yi kokari aka tura wa wadanda lamarin ya shafa tallafi.

Amma abin da muke nema yanzu shi ne hakkin mutanen da aka zalunta, saboda haka duk abubuwan da ya kamata mu yi na bin doka mun yi, kuma mun kira al’ummarmu cewa a yi hakuri mu bi dokar kasa a karkashin wannan kungiya, don mu ga abin da za a iya yi.  Saboda mun san cewa tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane dan Najeriya ’yancin gudanar da rayuwarsa a ko’ina a kasar nan. Saboda haka duk wanda ya ce zai hana Bafulatani kiwo a Najeriya, ya taka kundin tsarin mulkin Najeriya.

Aminiya: Mene ne ra’ayinka game da kiraye-kirayen da ake yi na sake fasalin Najeriya?

Sale Bayeri: Mu ra’ayinmu kusan mu dama tuntuni gwamnati baki daya kan yadda take tafiyar da harkokinta ba ma cikin lissafi, saboda Ma’aikatar Gona ta Tarayya wadda a karkashinta ne makiyaya suke, babu wani abin da muke samu a ma’aikatar. Wannan ma’aikata ita ce ya kamata mu samu komai a wajenta, amma an mayar da ma’aikatar

ta manoma kawai. Saboda haka dama Najeriya a wajenmu ba wata kasa ce da muke morar komai daga gar eta ba, sai dai ita ce take morarmu. Muna da shanu sun fi miliyan 27 a kasar nan, mu ne muke samar da nama da nono da man shanu da kiraga ga kasar nan, don haka ba a shigo da nama zuwa kasar nan daga ko’ina a duniya. A duk shekara Gwamnatin Tarayya tana asarar biliyoyin Naira wajen shigo da kifi da kaji daga kasashen waje, amma ba ta asarar komai wajen shigo da naman shanu saboda muna samar da naman shanun. A sanina a Najeriya babu wata karamar hukuma ko wata jiha ta taba kiran Fulani makiyaya ta ba su wani maganin shanu ko wani abu na ciyar da shanu tallafi.

Saboda haka tuntuni gwamnatin Najeriya ba ta yi damu, ba ta san damu ba. Don haka maganar a ce za a sake fasalin Najeriya, mu dama tuntuni fasalin Najeriya a bace yake a wajenmu. Saboda haka idan za a yi gyaran muna fatar za a sauraremu a ba mu hakkinmu, kamar yadda ake bai wa kowanne dan Najeriya. Muna fatar za a zo a ce mana ga kason makiyaya a Ma’aikatar Gona ta Tarayya da sauran ma’aikatun gona na jihohin kasar nan.