Dalilin da muka tsare ɗan jarida Fisayo Soyombo — Sojoji

Rundunar Sojin Najeriya ta yi ƙarin haske kan ɗan Jaridar nan mai binciken ƙwaƙwaf Fisayo Soyombo da ta tsare. Shelkwatar bataliya ta 6 ta rundunar sojin Najeriya ce ta yi ƙarin haske tana bayyana damuwa game da zarge-zargen da ake yadawa a kafafen sada zumunta na cewa ta tsare ɗan jaridar a birnin Fatakwal. Kwale-kwale […]

Dalilin da muka tsare ɗan jarida Fisayo Soyombo — Sojoji

Rundunar Sojin Najeriya ta yi ƙarin haske kan ɗan Jaridar nan mai binciken ƙwaƙwaf Fisayo Soyombo da ta tsare.

Shelkwatar bataliya ta 6 ta rundunar sojin Najeriya ce ta yi ƙarin haske tana bayyana damuwa game da zarge-zargen da ake yadawa a kafafen sada zumunta na cewa ta tsare ɗan jaridar a birnin Fatakwal.

Wata sanarwa ɗauke da sa hannun daraktan hulɗa jama’a na bataliyar, Laftanar Kanar Danjuma Jonah Danjuma ta ce kamen nasa na da nasaba da samamen da ake gudanarwa a yankin Neja Delta na yaƙi da satar ɗanyen mai.

Sanarwar ta ce “a wani samame da aka shirya, dakaru sun bi sawun ɓata-garin zuwa wani wurin satar ɗanyen mai.

“Yayin samamen, an kama mutane da dama, ciki har da Mista Soyombo wanda aka tarar a wurin.

“Ana gudanar da binciken farko a kan ɓata-garin da aka kama a wurin, ciki har da Mista Soyombo domin tantance irin rawar da suke takawa a satar ɗanyen man” a cewar bataliyar.

Bayanan sirri da aka samu a baya-bayan nan sun bankaɗo ayyukan wani gungun ɓata-garin da ya yi ƙaurin suna wajen lalata bututun mai a yankin.

Bataliyar ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai su tantance sahihancin rahotanni kafin su yada su ga jama’a.

Rundunar sojin dai ta saki Mista Fisayo Soyombo a cewar Cibiyar Binciken Ƙwaƙwaf ta Foundation for Investigative Journalism (FIJ).

Sakin Fisayo na zuwa ne bayan da ma’abota shafukan sada zumunta suka ƙirƙiri maudu’in #FreeFisayoNow na kiraye-kirayen neman a saki ɗan jaridar.

Soyombo fittacen ɗan jarida mai binciken ƙwaƙwaf musamman a kan rahotanni masu sarkakiya kama daga rashawa, wulaƙanta madafan iko zuwa cin zarafin bil Adama.

A watan Nuwamban nan ne dan jaridar ya saki wasu faifan bidiyo domin tabbatar da zargin safarar motoci da buhunan shinkafa ta ɓarauniyar hanya da ta shafi jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS).

Van Nistelrooy da Lampard sun samu aikin horaswa a Ingila

Dalilin da muka tsare ɗan jarida Fisayo Soyombo — Sojoji

Kwale-kwale ya kife da fasinjoji 200 a Kogi

An kuɓutar da ’yar shekara 4 daga hannun mai garkuwa da mutane a Kano