Dalilin da muke son Tinubu ya cire sunan El-Rufai daga jerin ministoci — Almajirai

Hakan ne zai tabbatar da adalci domin kuwa El-Rufai mutum ne mai tarihin rashin mutunta manyan mutane.

Dalilin da muke son Tinubu ya cire sunan El-Rufai daga jerin ministoci — Almajirai

Nasir El-Rufai

Almajiran Najeriya masu karatun Al-Qur’ani sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya janye sunan tsohon gwamnan jihar Kaduna daga cikin jerin sunayen ministocin da aka mika wa majalisar dokokin kasar domin tantancewa.

Almajiran sun ce hakan ne kadai zai tabbatar da adalci, zaman lafiya, da ci gaban al’umma a wannan kasa.

Almajiran sun kuma bukaci Majalisar Dokokin Tarayya da ta ki amincewa da nadin minista da ake shirin yi wa El-Rufai, domin a cewar yin hakan ba zai amfani kasar nan ba.

Daya daga cikin manyan Almajirai makaranta Al-Qur’ani a Najeriya, Gwani Sidi Aliyu Sise Sheikh Dahiru Bauchi ne ya yi wannan kiran a jawabin da ya yi wa manema labarai a Bauchi a karshen mako.

A cewarsa, “Mun ga sunan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir ElrufaI mutum ne da ya fito fili ya nuna kiyayyarsa ga Al-Qur’ani.

“A lokacin da ya je gidan Maulana Sheikh Dahiru Bauchi ya kwashe daruruwan dalibai da hayaki mai sa hawaye a cikin dare a kokarinsa na ganin an daina koyo da haddar Al-Qur’ani mai girma, saboda haka irin wannan mutumin bai kamata a sake ba shi kowane irin mukami ba.

“Ya nuna bai san dokokin kasa ba, bai san girman manya ba, bai san girman Mahaddata Al-Qur’ani, kuma bai san girman Al-Qur’ani ba.

“Ya tauye ’yancin dan adam, don ba mutunta ’yancinsu a kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada wajen ba su ’yancin zama a duk inda suke so.

“Ya tauye musu ’yancin addini a kokarinsa na hana su karatun Al-Qur’ani, saboda haka bai kamata a bashi kowane irin matsayi ba balle minista.”

Sheikh Sidi Ali wanda shi ne Daraktan Ilimi a Gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce nada tsohon gwamnan “wanda ya zalunce mu kamar yin fito na fito ne da Allah Madaukakin Sarki ne kuma fada da Allah ba zai taimaki gwamnati ko kasar nan ba.

“Yanzu haka ma muna ta fama da matsalolin tsaro da tattalin arzikin kasa saboda wasu suna tsokanar Allah, don haka muna kira ga Shugaba Tinubu da ya janye sunansa domin amfanin kasar nan.

“Idan kuma har shugaba Tinubu bai yi hakan ba to muna kira ga Majalisar Tarayya da su sanya maslahar kasa a zuci, su ki bashi dama, a kan kowane mukami, domin a yi wa al’ummar Al-Qur’ani adalci, da ‘yan Nijeriya.”

Gwani Sidi ya kuma bukaci Shugaba Tinubu da ya yi hattara da El-Rufai da sauran mutanen irinsa wadanda a cewarsa ba sa goyon bayan koyo da haddar Al-Qur’ani.

“Muna rokon Tinubu, a maimakon nadin da zai yi wa El-Rufai, ya maye gurbinsa da Mallam Isa Yuguda tsohon Gwamnan Jihar Bauchi ya kuma karrama Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ta hanyar ba shi damar sa mutanen kirki a mukamai, saboda irin girmamawar da suke yi wa Almajiran Al-Qur’ani.

“Duk dai haka muka yi tsammani amma ba mu ji komai ba, sai muka yi mamakin ganin sunan El-Rufai a cikin jerin sunayen ministocinsa.

“Idan har yana son ya ci nasara ya gaggauta janye sunansa ya maye gurbinsa da wani dan Najeriya nagari, kwararre kuma wanda ba zai kyamaci tsarin karatun Almajirai ba, wanda ba zai nuna wariya ga tsarin ilimi ba sai dai ya kyautatashi.”

Gwani Sidi ya yi addu’ar samun zaman lafiya da hadin kai da kwanciyar hankali a kasar nan, sannan ya yi gargadin cewa “nada wadanda suke makiyan Almajirai da makarantun Al-Qur’ani ba zai yi wa gwamnati dadi ba domin suna fada da Littafin Allah da aka saukar domin shiryar da mutane, wanda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba su damar koyo da haddace shi a duk inda suke a kasar nan.”

Sheikh Sidi Aki ya bukaci Majaisar Dattawa ta 10 a kan kada ta tabbatar da El-Rufai a matsayin Minista, ya kuma shawarci Sanatoci uku daga Jihar Kaduna da su tashi tsaye, su dauki turbar girma da mutunci, su bijire wa amincewa da tsohon Gwamnan domin ci gaban al’umma.

“Muna so dukkan Sanatoci su yi watsi da nadin El-Rufai ba tare da wata shakka ba, don amfanin Almajirai da suka sha wahala a karkashin mulkinsa na shekaru takwas na zalunci.

“Ya kamata Sanatocin Najeriya su kubutar da kasar nan daga cikin hatsarin da ke tattare da sake tsugunar da irin wannan mutum a kujerar mulki.

“Mutumin da ke da tarihin rashin mutunta manyan mutane, da tsatsauran ra’ayi da rashin mutunta doka bai cancanci amincewar majalisa ba.

“Bai cancanci zama minista ba, kuma duk Sanatan da ya tabbatar da El-Rufai ya ci amanar al’ummar kasar nan; duk Sanatan jam’iyya mai mulki da ya tabbatar da El-Rufa’i ya zama minista, ya amince ne da nadin wanda zai ruguza gwamnatin Tinubu da.”

Sheikh Sidi Ali ya ce “kada matsain lamba ta sa Shugaba Bola Tinubu ya mika wuya ga kowane dan siyasa, ya kamata ya jajirce wajen janye sunan Elrufai domin ceto kasar nan da kuma ceto gwamnatinsa daga bala’i.

“Ya kamata kar a bari El-Rufai ya kusanci madafun iko idan har gwamnati mai ci na son a samu masaniyar cewa da gaske take yi, domin a idon jama’a ne Malam Nasir El-Rufai ya nuna kiyayyar AlQur’ani.

Ana sa ran cewa a ranar Litinin ce Majalisar Dattawa za ta fara tantancewa tare da tabbatar da sunayen ministoci 28 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika mata.

Kokarin jin martanin tsohon gwamnan na Kaduna ya ci tura domin bai amsa kiran waya da sakon tes wakilinmu ya tura ba.

Haka kuma, tsohon mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, bai amsa kiran waya da sakonnin tes da aka aika masa ba.

Tinubu ya yaba wa NNPCL kan fara aikin Matatar Warri

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9

’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos