Dalilin da muke yin Maulidin Shehu Ibrahim Nyass a garuruwa biyu – Sheikh Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Usman Bauchi fitaccen malami ne kuma jagora a Darikar Tijjaniyya, a zantawarsa da Aminiya a gidansa da ke Bauchi ya yi bayani kan Maulidin Shehu Ibrahim  Nyass na Kasa da ake shiryawa a manyan garuruwa biyu da mutane ke gani kamar sabani ne tsakanin ’yan Tijjaniyya: Ga shi bana ma za a yi […]

Dalilin da muke yin Maulidin Shehu Ibrahim Nyass a garuruwa biyu – Sheikh Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Usman Bauchi fitaccen malami ne kuma jagora a Darikar Tijjaniyya, a zantawarsa da Aminiya a gidansa da ke Bauchi ya yi bayani kan Maulidin Shehu Ibrahim  Nyass na Kasa da ake shiryawa a manyan garuruwa biyu da mutane ke gani kamar sabani ne tsakanin ’yan Tijjaniyya:

Ga shi bana ma za a yi Maulidin Shehu Ibrahim a gari biyu rana guda a Kano da Abuja kamar yadda aka yi a bara a Kaduna da Abuja, me Shehi zai ce kan haka?

Alhamadulillahi! Mun gode wa Alah da Ya ba mu Annabi Muhammadu (SAW). Domin shi ne babban rahamar da Allah Ya bai wa halitta baki daya. Shi wannan babban alheri da Allah Ya bai wa duniya da Lahira wato Annabi Muhammadu (SAW), idan watan da ya zo duniya ya kewayo shi ne watan Rabi’ul Auwal muna sake gode wa Allah saboda alherin da Ya ba mu ya kewayo. Idan kuma watan Safar ya kama, ranar 13 sai mu taru mu sake gode wa Allah muna tuna watan da Allah Ya sa aka haifi Shehu Tijjani ke nan. Haka idan watan Rajab ya yi sai mu taru mu gode wa Allah na tuna alherin da Allah Ya ba mu da Ya kawo mana Shehu Ibrahim (RTA) a cikin wannan wata na Rajab, da yake a watan Rajab ne Shehu Ibrahim ya zo duniya shi ya sa idan watan ya zo sai mu taru mu sake maimaita wa Allah godiya kan wannan alheri da Ya ba mu. Watan Rajab yana da muhimmancin gaske domin a ciki aka samu juna biyu na Manzon Allah (SAW), a ciki aka samu tafiyar Isra’i da Mi’iraji, a ciki aka samu haihuwar Shehu Ibrahim (RTA) saboda haka muhimmi ne wannan wata. Don haka in ya kewayo sai mun sake gode wa Allah saboda alherin da Ya ba mu, kuma Allah Ya ce ku gode wa alherin da Na ba ku saboda haka muke gode wa Allah don kwadayin Ya kara mana alherinSa saboda ya ce idan ka gode maSa zai kara maka.

Saboda haka muke gayyatar dukan al’ummar Musulmi masoya Manzon Allah (SAW) su halarci wajen wannan Maulidi da za mu yi a Abuja wadansu ’yan uwanmu kuma za su yi irin wannan taro a Kano duk dai saboda kasaitar wannan waliyyi ya sa ko’ina ana sonsa, ana marmarin a yi taro a gode wa Allah saboda samunsa.

Amma wadansu na ganin rashin fahimta ce take jawo wannan rarrabuwa na yin Maulidin waje daban-daban?

To wane ne da wane ne suka bata, ballantana a ce an samu rashin fahimta? Masu maganar in suna yi su fadi sunan wadanda suka bata mana ? Rashin fahimta ai batawa ce ko? To su wane ne suka bata? To ba a bata ba ma, balle a samu rashin fahimta da juna. Raba taron ai kasaita da isar malamin ne ya sa ake taro har kashi biyu haka. Wani ma in ya yi musu ya kira taron malaminsa ko babansa a gari daya ya ga ko za a taru haka, a gari daya balle manyan birane kamar Kano da Abuja. Ai kasaitar wanda ake yin taron dominsa ne ta jawo abin ya yalwaita ya bunkasa ya wuce gari daya sai ya zama gari biyu; Kano a yi, a Abuja ma a yi.

Wace shawara za a bai wa mahalarta Maulidin don yin komai cikin tsanaki kuma a gama lafiya?

Muna shawartar dukan masu halartar taron Maulidin Shehu Ibrahim a Abuja da Kano da dukan ’yan Tijjaniyya da su halarci wajen don su samun albarka. Shehu Ibrahim yana cewa duk wanda yake  dazuzzuka daga garinsu ya zo wajen, Allah Ka sa shi daga cikin zababbun bayinKa, duk wanda ya je Kano din ko Abuja din ya shiga cikin wadanda Allah Ya zaba, shi ya sa ya kashe kudinsa ya bar ayyukansa don zuwa hidimar wannan bawan Allah Shehu Ibrahim (RTA). Yin wannan hidima girmama alfarmar Allah ce da mutumin da Allah Ya girmama.

Allah Ya ce duk wanda ya girmama alfarmar da Allah Ya kafa, to hakika yin haka shi ya fi masa a wajen Allah kuma yana nuni da cewa yin haka tsoron Allah ne. Shi ya sa ’yan uwanmu suka taimake mu suka shirya mana wannan taro na girmama waliyyin Allah Shehu Ibrahim (RTA). Muna rokon Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya, Allah Ya yaye bala’i a Najeriya. Dukan abin da ba ya da kyau Allah Ya yaye shi a Najeriya, dukan alheri kuma Allah Ya kawo mana shi a Najeriya.

Muna kuma shawartar ’yan Najeriya da cewa za su ga turuwar jama’ar Shehu Ibrahim da ga ko ina sun fito don halartar wadannan tarurruka ko a Abuja ko a Kano sun cika hanyoyi da su yi hakuri  bakin Allah ne. Allah Ya sa mu yi tarurruka lafiya kowa ya koma gida lafiya.