Dalilin da na ayyana dokar ta-ɓaci kan ɓangaren ilimi a Kano — Abba

Za mu gina azuzuwa 28,264 nan da shekaru 3 masu zuwa a faɗin jihar.

Dalilin da na ayyana dokar ta-ɓaci kan ɓangaren ilimi a Kano — Abba

Gwamnatin Kano ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi a faɗin jihar a wani mataki na farfaɗo da ɓangaren ilimin jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya jagoranci manyan jami’an gwamnati da masana harkokin ilimi da ‘yan siyasa wajen ƙaddamar da dokar ta-ɓacin ranar Asabar a birnin Kano, ya ce babban burinsa shi ne samar da ilimi mai inganci ga kowa domin ci gaban jihar.

Ya ce matakin ya zama wajibi domin magance matsalolin da ɓangaren ilimin jihar ke fuskanta.

Gwamnan ya kuma yi kira da sauran masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimin jihar su fito su haɗa ƙarfi domin magance matsalolin da suka yi wa ɓangaren ilimin jihar katutu.

“Ina kira ga masu ruwa da tsaki da gwamnati da malamai da iyaye da kamfanoni masu zaman kansu da sauran al’umma, su haɗa kai, wajen farfaɗo da fannin ilimi, domin ci gaban al’ummarmu.

“Samun ilimi mai inganci shi ne babban makami mafi inganci na yaƙi da talauci da miyagun laifuka cikin al’ummarmu.”

Gwamna ya ce manufar ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi shi ne samar da gagarumin sauyi kan yadda fannin ilimin jihar ya taɓarɓare.

Abba Kabir ya ce matakin zai bai wa gwamnati damar tanadar duk wani shiri domin aiwatar da gyare-gyare cikin gaggawa da mai da hankali wajen lalubo dabarun da za su sake gina ɓangaren ilimin jihar.

“Matakin zai taimaka wajen ceto makarantunmu da suka durƙushe, mataki ne mai tsauri na tabbatar da cewa kowane yaro a Jihar Kano ya samu ilimi mai inganci, wanda shi ne babban hakkinsu,” in ji gwamnan.

Gwamnan ya kuma ce wannan mataki zai taimaka wajen kawar da duk yaran da ba su zuwa makaranta daga titunan jihar domin mayar da su makarantu.

“Domin cimma wannan, da farko, dole mu samar da azuzuwa domin yara kimanin 989,234, da ba sa zuwa makaranta a cikin jiharmu.

“Kwaskwarima ga ɗakunan gwaje-gwajen kimiyya 300 tare da gina sabbin ɗakuna 300 a makarantu 200 da ke jihar. Jimilla, za a gina azuzuwa 28,264 a makarantun jihar daga yanzu zuwa shekaru uku.

“Za a sake buɗe dukkan makarantun kwana da gwamnatin da ta gabata ta rufe. Sannan za a ba da abinci sau ɗaya kullum ga ɗaliban firamare, da inifam kyauta.

“Ma’aikatar ilimi da SUBEB za su sa ido kan yadda za a gudanar da ayyukan.

“Domin daƙile matsalar rashin malamai, musamman a makarantu 400 da ke shiyyar Kano ta Kudu, inda ake samun malamai ɗaya a kowace makaranta, mun bayar da umarnin bai wa malaman BESDA 5632 takardun ɗaukar aiki na dindindin da za su fara daga yau”, a cewar gwamnan.

“Ɗaukar aiki na jami’ai 1000 a ɓangaren koyarwa da wanda ba na koyarwa ba a makarantun gaba da sakandare da ke faɗin jihar. Tare da ɗaukar sabbin malamai 10,000,” a cewarsa

“Mun ware Naira miliyan 300 don bai wa malaman firamare bashi mai sauƙin biya. Sannan an samar da manyan motocin bas 70 don kai yara mata makarantu.

Gwamnan ya ce ya bai wa SUBEB damar tsara yadda za ta gudanar aikin horas da malaman makarantar a faɗin jihar.

Abba Kabir Yusuf ya ce malaman makaranta za su ci gaba da samun horo lokaci zuwa lokaci don cimma burin da gwamnatin ta sanya a gaba.

Daga cikin muhimman matakan da gwamna Abba ya dauka game da dokar ta-bacin kan ilimi ya ce gwamnati za ta biya dukkan ƙudin makaranta na tuition fee tare da bayar da satifiket ga ɗaliban da aka bai wa tallafin karatu (scholarship) a jami’o’in jihar. Sannan za a biya kuɗin NECO da NBAIS ga ɗaliban da suka cancanta.